Tana nan kwance har sai da ta ji an tayar da sallah a masallacin da ke cikin estate din ta yi yunƙurin tashi, a daddafe ta kai kanta bathroom ruwa mai zafi ta tara da dabara da dauriyar da ta sanya ta shiga ruwan tana runtse ido, ga hawaye na gudu kan kuncinta sai da ta ji ya soma sanyi ta zubar ta sake wani, wankan tsarki ta yi sai ta yi wanka da ruwa mai zafi, sosai ta ji dama lokacin da ta fito doguwar riga har ƙasa ta samo ta sanya ta yi sallah ta lallaɓa. . .