Washegari da safe ko da ta yi sallah shirin makaranta ta soma. Wadda Aunty Karima ta ɗorawa alhakin gama abin karin Hamida kafin fitar ta Sch ta zo ta gaya mata ta kammala.
Ta fita zuwa dinning ɗin ta haɗa tea ta zuba agada da ƙwai a flate sai ta koma ɗakin, akan mirror ta ajiye plate ta tsaya tana karyawa tana duban agogo don lokacin tafiyar su ya yi ko me ya hana Abdurrashid fitowa? Turo ƙofar da aka yi da shigowa gabaɗaya ya sa ta kai idonta wurin, a shirye yake ya yi kyau kamar kullum. . .