Kwana uku da yin haihuwar da daddare Hamida na ɗakinta tana karatun makaranta don koyaushe suka yi waya da Abdurrashid ba abin da yake jaddada mata irin ta kula da karatunta. Don haka ta ƙara dagewa ta haƙura da karatun littattafan hausa da take sai kaɗan shi ma saboda abin ya shiga jikinta, ba abin da ke ranta irin ta yi abin da za ta burge Abdurrashid wanda sai da ya tafi ta gane ba ƙaramin so take mishi ba tana cikin kewar shi har lokacin.
Wayarta ta ɗauki ƙara ta ɗaga da sallama Gwoggo ce sai ta. . .