Skip to content
Part 22 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Kwana uku da yin haihuwar da daddare Hamida na ɗakinta tana karatun makaranta don koyaushe suka yi waya da Abdurrashid ba abin da yake jaddada mata irin ta kula da karatunta. Don haka ta ƙara dagewa ta haƙura da karatun littattafan hausa da take sai kaɗan shi ma saboda abin ya shiga jikinta, ba abin da ke ranta irin ta yi abin da za ta burge Abdurrashid wanda sai da ya tafi ta gane ba ƙaramin so take mishi ba tana cikin kewar shi har lokacin.

Wayarta ta ɗauki ƙara ta ɗaga da sallama Gwoggo ce sai ta soma gaishe ta da suka ƙare gaisuwar Gwoggon ta ce “Abin da ya sa na kira ki game da gudummuwar Laila ne, Aina ta turo da na ta ke me za ki bayar?

Hamida ta ɗan yi shiru kafin ta ce “Zan duba kuɗaɗen da Abba ke ba ni na makaranta abin da na samu zan faɗa miki Gwoggo.”
Waye Abba? Gwoggo ta tambaya
Ba ta ko numfasa ba ta ce “Babanshi.

Gwoggo ta ce “Shi kenan sai na ji ki.”

Hamida ta ce “Sai da safe.”

Ta katse kiran ta ɗauko jakar makarantar ta ciro kudaden ciki ta haɗe su wuri daya ta ƙirga, kamar ta kira Gwoggon ta shaida mata abin da ta samu sai ta yanke ta bari sai da safe.

Da safen kuma da ta tashi tana sauri ta wuce makaranta ba ta samu kiran Gwoggon ba har sai da ta dawo tana ɗaki Aunty Karima ta shigo wata ƙatuwar leda mai ɗauke da tambarin wani store ta miƙa mata sai bundle na dubu daya, ta ce “Waɗannan zannuwan ki kai wa yar’uwarki mai jego. Kudin kuma Daddy ne ya ce a ba ki ki yi hidimar sunan.”

Ta karɓa tare da godiya mai yawa Daddyn ma ta je ta yi mishi godiyar.

Sai da Aunty Karima ta fita ta buɗe ledar manyan Atamfofi ne guda biyu sai less asalin irin waɗanda Auntyn ke ɗaurawa.

*****

Ranar suna sai da suka tashi daga makaranta da ta dawo ta yi shirin zuwa gidan sunan.
Baba Adamu ya kai ta ba ƙaramin farin ciki ta yi ba da ganin yan Daura.

Ƙarin jin daɗinta ba har da Innawuro sai dai ba mamanta. Gwoggo Indo ta ba kayan mai jegon, da suka keɓe kuma ta ba Innawuro kuɗaɗen da Baban Abdurrashid ya ba ta ta ce su raba su hudu da babanta da Mamanta da Innawuron da Malam.

Innawuro ƙin karɓa ta yi sai da ta yi ta mata magiya sai ta karbi rabi ta ce ta riƙa adana duk abin da ta samu. Sun sha hotuna sosai Walida ma ta zo mata suna Aina ma ta zo sai dai ba ta kwana ba ranar ta juya.

Hamida kam sai da Innawuro ta matsa mata ta zo ta tafi gida ta ce direba zai zo ƙarfe biyar.
Aunty Karima ta kira Hamida ta waya ta ce in za ta taho ta zo tare da Innawuro don sun yi waya da Malam ya ce mishi har da ita aka zo.

Haka aka yi taren suka tafi murna kamar ta kashe Hamida suka kwana tare, ga shi washegarin sunan babu makaranta suka wuni da Innawuro wadda Daddy ya hana komawa gidan Gwoggo Indo, don sai washegari za su koma.

Sauran yan sunan sun zo da yamma sun tafi kenan kiran Abdurrashid ya shigo wayarta wanda tana gaishe shi ya soma tambayarta hoton ita da su wa ta ɗaura akan Dp ta?

Ta ce “Yan’uwana ne yan Daura.
Ya ce “Yaushe suka yi hoton ta ce “Jiya da suka zo suna.”

Cikin matuƙar mamaki ya ce “Sunan wa? Ta ce “Aunty Laila ce ta haihu.”

Ya ce “Kuma har kika fita kika je suna ban sani ba?

Ɗan shiru ta yi kafin ta ce “Aunty ta ce “In je.”
Cikin yar hasala ya ce “Aunty ke aurenki ko da ba za ki gaya min ba ya yi kyau.”

Ƙit ya katse kiran. Rasa yadda za ta yi ta yi sai ta ajiye wayar cikin sanyin jiki ta fita falo wurin Innawuro.

Washegari su Innawuro suka koma Daura da ɗinbin alhetin da Engineer ya yi musu.

Hamida ba ta ƙara samun wayar Abdurrashid ba hakan ya dame ta amma ba ta da dabarar da za ta kira shi.

Ranar da suka cika kwana uku rabon su da juna kwance yake a ɗakinsu shi da Usman juye juye yake ta fama don ba abin da yake so a lokacin irin ya kasance da matarsa.

Usman da ke gefen shi yana waya da matarsa Jamila, kalaman da yake furtawa duk su suka ƙara tsokano shi ya miƙe yana ce mata su yi Vedio call.

Abdurrashid ya bi shi da kallo ganin ya shige bathroom sai ya janyo wayarsa data ya kunna ya shiga whatsapp cikin sa’a ya ga Hamida online Video call ya kira ta yana raya wa a ransa ina ma Hamida ta yi girma da wayewar da za ta biya mishi buƙatar shi a haka.

Ganin hotonta ya bayyana ya sa shi sakin wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.

Sai da ya ɗaure fuskarsa ya ce “Ke in ba an kira ki ba ba ki kiran mutum ko? Sai da ta ɗan kauda idonta don kar su haɗa ido ta soma gaishe shi bai amsa ba ya ce “Ke ba ki san yadda za ki ba mijinki hakuri ba idan ya yi fushi?

Ta furta ka yi haƙuri sai kallon ta yake sanye take cikin atamfa riga da zane da ɗankwalinsu. Sai wani iri yake ji don sha’awarta da ke ƙaruwar masa.

Karatunta ya riƙa tambayar ta tana ba shi amsa, sun dade a haka har Usman ya fito daga bathroom ɗin yana goge kan shi da tawul sai satar kallon sa yake sanin wanka ya yi yana tuna tsiyar da yake mishi morewar auren babbar mace wayayya, yanzu ba ya kusa da ita amma ba shi da wata damuwa da sun yi Vedio call za ta biya masa bukatar shi.

Ya fidda ajiyar zuciya ya dubi Hamida da ido ma ba ta yarda su haɗa ballantana ya yi tunanin ta san hanyar da za ta biya masa buƙatar ta sa.
Wayar ya kashe ya miƙe don samo maganin da yake sha yake kwantar mishi da sha’awa.

Fahimtar abin da yake yi ganin yana shan maganin ya sa Usman ya fara mishi dariya da shegantaka shiru ya mishi har ya gaji ya kyale shi.

Hamida sun zana jarabawar First team har sun yi hutu wannan karon ta yi abin gani don na bakwai ta yi wanda tun soma karatun na ta ba ta taba kokari kamar wannan ba.

Momi Binta ta ce ta ta zo gidanta ta yi mata hutu can ɗin ta tafi bayan an tambayi Engineer, sai dai ita Hamidar ba ta bari ta tafi ba sai da ta gaya wa Abdurrashid.

Kwanan ta ɗaya Mimi ta dira Abujar suka haɗu su uku ga Hanan sosai Hamida ta ji daɗin zuwan ta Abuja, kasantuwarta da su Mimi ta ƙara wayewa ta naƙalci abubuwa da dama na rayuwa.

Sai da hutun ta ya kusa ƙarewa ta koma Kano.

Haka rayuwa ta cigaba da garawa Hamida na cigaba da karatunta idan suka samu hutu tana yinsa ne a Abuja ko Katsina gidan Aunty Safiya ko Yola wurin Daada da Aunty Zainab.

Tana kuma roƙon zuwa Daura idan suka samu hutun kwata kwata kwana uku ake ba ta ta je ta dawo.

An yi bikin babbar ɗiyar Aunty Binta da me bi mata haka ma yayan Aunty Safiya su biyu
Lokacin da Hamida ta kammala karatun sakandirenta lokacin kuma saura shekara guda Abdurrashid ya dawo ta yi wani irin girma ta zama cikakkiyar mace ga ɗinbin wayewa da ta yi don tana tare da wayayyun, sai dai in za su yi vedio call da Abdurrashid hijab take zabgawa wai kar ya gane ta yi girma.

Kamnala sakandirenta yayin da Engineer ke son ta cigaba da karatu a Open University ita Aunty Binta shawarar a nema mata Nile University Abuja.

Engineer ya ba ta haƙuri ya ce a bari ta yi Open University ɗin.

Da Hamida suke labarin makarantar da za ta cigaba da Walida wadda FCE za ta cigaba, wani abu ta ji ya tsaya mata ganin kodayaushe Hamida na saman ta kafin ta ƙaƙaro murmushi ta ce “Kin caɓa.”

Sun fara karatu Hamida na mayar da hankali sosai har suka ƙare shekarar su ta farko Computer Science don haka dole take dagewa.

Yanzu zuba idon dawowar Abdurrashid ake don za su iya dawowa a koyaushe.

Wata ranar laraba Hamida ta dawo makaranta, a gajiye take don haka sauri take ta yi sallah ta kwanta, ko abinci sai ta tashi ta yi niyyar cin shi.
Aunty Karima ta shigo ɗakin daidai ta idar da sallah, gaishe ta ta yi ta ce “In kin kammala ki same ni falo za mu duba gidan ku Daddy ya ce ki zaɓi kayan da za a zuba miki.”

Kanta ta sunkuyar jin abin da Auntyn ta ce kafin ta ce “To Aunty.”

Auntyn ta juya sai ta ja mata ƙofar.
Ta miƙe zuwa wurin kayanta don daga ita sai zane doguwar riga mara nauyi ta ciro da gyalenta ta zura sai ta ninke zanen da hijabin.

Ta fito ba ta ga Auntyn ba sai ta duba ta a ɗaki suka fito tare, Auntyn na gaba tana bayan ta ta cikin gidan akwai ƙofa da za ka shiga zuwa gidan Abdurrashid ta nan suka bi.

Gini aka yi mai matuƙar tsari da kyau, shuke shuken da aka yi sun ƙara ƙayata wurin.

Aunty Karima ta buɗe wurin suka shiga, ɓangaren ta daban haka na Abdurrashid. An gama komai sai dai Furnitures ne da ba a zuba ba.

Sun duba ko’ina yayin da me musu wanki ya yo ma wasu mata jagora sun iso suka gaisa sai suka ci gaba da duba wurin tare ƙarshe Aunty Karima ta dubi Hamida ga wadda za ta shirya muku wuri nan, aikinta kenan sai ki faɗa mata irin abin da kike so.”

Hamida ta sa hannayenta ta kama kumatunta “A’a Aunty na bata zaɓi.”

Murmushi Auntyn ta yi ta ciro wayarta ta soma kira daga yadda take wayar Hamida ta gane da Abdurrashid take shi ma tambayar shi ta yi zaɓinsa za a shirya masa wuri ya ce ta tambayi Hamida wanda ta zaɓa mishi shi kenan.

Murmushi kawai Auntyn ta yi ta sauke wayar tana faɗi ma Hamida yadda ya ce Saboda tsayuwar Aunty Karima wurin ta kasa faɗi ta ce za ta gaya mata.

Sati biyu kawai aka ƙara matar ta tafi china da ta dawo kuma aka shirya wurin da ya yi matuƙar ƙayatuwa da idan ka shiga ba za ka so fita ba.
Masu aiki suna shiga su gyara don kowane lokaci Abdurrashid zai iya dawowa.

Wani yammaci Hamida na kwance a daki kwana uku kenan da suka samu hutu wani littafi take karantawa.

Daya daga cikin masu aikin Aunty Karima ta yi knocking ta tashi ta bude ta sanar mata tana da bakuwa, kai ta daga sai ta fito Gwoggo Indo ta samu a falon ta nemi wuri ta zauna tana mata sannu da zuwa.

Sai da ta gaishe ta suka soma hira,cikin hirar Gwoggo ke kara gaya mata halin da take ciki,don wurin saida abincinta yanzu ba kamar da ba ya ja baya sosai saboda sababbin masu sayarwa da aka samu a Estate din.

Hamida ta yi shiru tana sauraren ta hannunta daya na cikin calabar ta tana yamutsawa sai da ta ji ta yi shiru ta ce “Zan ba ki abin da ke hannuna Gwoggo kafin in dawo.”

Gwoggo Indo ta yi saurin cewa “Ina za ki”
“Yola za mu tafi diyar Aunty Zainab za ta yi birthday,akwai kuma bikin Mimi wani satin,zan dan kwana biyu a can kafin in dawo.”

“To mijin naki fa da kika ce zai dawo cikin watan nan?

Hamida ta gyara zama “Ni dai abin da aka ce min kenan.”

Gwoggo Indo ta ce “Yaushe ne tafiyar ?
“Gobe idan Allah ya kaimu.”

“Shi kenan,amma ni dai na fi son ki gyara kanki kafin isowar shi.”

Hamida ta muskuta “Ni maganin sanyi na fi so Gwoggo.”

“Akwai su kala kala masu mugun kyau.”

“To ina so,wa za ki ba ya kawo min ?

“Zan ba Ladi Allah dai ya sa da gaske shan za ki yi.”

Murmushi Hamida ta yi “Allah zan sha Gwoggo.”

“Shi kenan zan ba ta idan na koma sai ta kawo miki.”

Ta mike ta koma daki kudi ta dauko ta kawo mata, sai dai daga ganin yadda Gwoggon ta karba ta san ta raina, sai dai ba ta yi magana ba mikewa ta yi Hamida ta bi bayanta don ta raka ta.
Da ta dawo daki ta shiga ta cigaba da shirin tafiyarta.

Washegari suka wuce Yola ita da Aunty Karima,
bikin Mimi ne don haka Hamida ita ce babbar kawa ita da Hanan.

Gidan Daada suka fara yada zango kafin suka isa gidan Aunty Zainab duka yayan Daada sun hallara saboda birthday din autar Aunty Zainab ana ta shagali a harabar gidan har Daadar suka sa aka dauko wadda aka samu ta zo da kyar wai me za ta zo yi a wannan shiriritar.

Hamida wadda tun da ta tashi take jin ta wata iri tana kwance tun dawowar su daga sallon Hanan ta shigo ta yaye abin rufar da ta rufe har kanta Hamida ta dube ta “Wai da ma ba barci kike ba?
Saboda Allah meye haka za ki wani shigo daki ki kwanta kowa na waje yana sha’aninsa,sai nemanki muke ni da Mimi, don Allah ki tashi ki yi wanka.

Ta mike ta shiga bathroom kafin ta fito ta ce shiga to ki yi wankan na hada miki ruwa.

Hamida da ke kallon ta ta mike a hankali ta shiga wankan ta yo ta fito ta samu Hanan din a inda ta bar ta tana danna wayarta.

Ta wuce ta zauna gaban dressing mirror ta sheka kwalliya sai kallon kanta take yadda ta zama,ta mike neman kayan da za ta sanya ta ga wani rantsatstsen less a kan gado ta san ita Hanan ta ajiye mawa kallon ta ta yi “Less din nan ya min nauyi my Hanan.”

Ita ma ta dago suka dubi juna “To me za ki sa?
Ta karasa inda kayanta suke wata atamfa ta ciro dinkinta karami ne da ta sanya ya zauna das a jikinta cikinta ya shafe kirjinta ya cika zanen ta yi daurin baya ta kafa dauri kamar kar ta sa mayafi da ta zura takalmi sai dai ta ciro wani karami ta ajiye shi a kafada dan kunne da sarka fashion ta yi amfani da su sai ta daura agogo.

Hanan ke ta fesa mata turare har sai da ta ce “Haba mana my Hanan.”

Suka fita rike da hannun juna nesa da inda ake ta cashe rawa suka tsaya nan Hanan ta zo ta same su suna ta hirar su silalowar da wata dalleliyar mota ta yi zuwa parking space ya sa suka yi mata kallo daya sai suka cigaba da hirar su.

<< Shirin Allah 21Shirin Allah 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.