Ranar wata juma'a ba ta shiga School kwance take a ɗakinta wayarta ta yi ƙara, Jamila ce matar Usman ke shaida mata ta haihu.
Ta tashi zaune fara'a kwance kan fuskarta take faɗin "Me muka samu?
Ga ni nan zuwa."
Ta ce "Mace ce."
Ba ta daɗe da yin wanka ba ta kwanta don haka kayan jikinta kawai ta canza sai ta tura wa Abdurrashid text message za ta tafi gidan Usman Asma'u ta haihu.
Don ba ya garin.
Tana shirin tana tuna abin Allah, Asma'u daga dawowar su Abdurrashid yanzu haihuwa ta uku. . .
A gaskiya wannan labarin yayimin dadi sosai Allah ubangiji ya qara lfy da Nisan kwana Allah ya qara basira