Skip to content
Part 25 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Ranar wata juma’a ba ta shiga School kwance take a ɗakinta wayarta ta yi ƙara, Jamila ce matar Usman ke shaida mata ta haihu.

Ta tashi zaune fara’a kwance kan fuskarta take faɗin “Me muka samu?

Ga ni nan zuwa.”

Ta ce “Mace ce.”

Ba ta daɗe da yin wanka ba ta kwanta don haka kayan jikinta kawai ta canza sai ta tura wa Abdurrashid text message za ta tafi gidan Usman Asma’u ta haihu.

Don ba ya garin.

Tana shirin tana tuna abin Allah, Asma’u daga dawowar su Abdurrashid yanzu haihuwa ta uku kenan ta yi maza biyu yanzu ta yi mace.

Baba Adamu ya kai ta, ta iske mai jegon a bed room ɗinta ta ɗauki jaririyar suna ta hira take cewa Hamida daga wannan ta tsaya sai ta huta sai ka ce kaza duk bayan shekara biyu sai ta haihu?

Wani iri Hamida ta ji ta ce “A’a dai Maman Sultan,ki gode wa Allah wani ɗaya ma yake nema bai samu ba.”

Sai ta ji Hamidar ta ba ta tausayi ta ce “Haka ne fa kuma, Allah ya kawo muku kuma mu sha suna. Ko da ina naƙuda sai da na yi miki addu’a, daga an ce addu’ar mai naƙuda amsassa ce.”

Hamida ta ce “Na gode Maman Sultan.”

Murmushi ta yi “Meye wani abin godiya? Abban Sultan ɗin ma ya ce sunanki ya sanya wa babyn don wai son da muke wa juna da ke.”

Wani iri Hamida ta ji ga sunan uwar shi bai sanya ba,ga na uwar matarsa sai ta kanne ta ƙaƙaro murmushi har da yin godiya.

Suna nan zaune suna hira time ɗin da ta ce Baba Adamu ta ji shiru tana ƙoƙarin kiran shi a waya Usman ya shigo ɗakin ta gaishe shi tare da yi masa barka ya ce “In kin tashi tafiya sai in sauke ki, don na ce wa Baba Adamu ya je abin shi.

Hamida ta ce”Ai yanzu ma zan tafi zan yi karatu mun kusa fara Exam.”

Jamila ta riƙe baki “Kar dai kin kusa kammala karatunki ? Hamida ta ɗaga mata kai “Daga wannan Exam na gama.”

Ta riƙe baki”Kin ga ina zaune har kin tashi wasa, kullum ina waƙar komawa karatu ɗawainiyar ciki da goyo ya hana, ai yanzu dai zan tsayar da ita Allah karatu zan koma.”

Hamida ta yi murmushi “Ka ji Maman Sultan.”

Usman da ke tsaye yana jin su ya juya ya fita ita ma sallamar ta yi mata ta bi bayansa duk da ba ta son tafiyar tasu tare ya buɗe mata gaba ta shiga.
Sun fara tafiya suke zancen ranar da Abdurrashid zai dawo kafin ya ɗan dube ta sai ya maida idonsa kan hanya “Ai abokina ba ƙaramar sa’a ya taka ba, ga lafiyayyar mace ya samu yana ta more rayuwarsa shi ya sa kullum za ka gan shi yana wani ƙara annuri abin sa, to ya samu duniya ga ba ruwan shi da kataniyar yara da za su hana shi morewarsa.

Ɗif! Hamida ta ɗauke wuta jin zancen Usman me zai sa ya gaya mata haka duk da a take takensa ta san zai iya hakan. Zai cigaba ta ɗaga mishi hannu “Haba mana Usman.” Ta ambaci sunansa saɓanin Abban Sultan da take ce mishi “Ina matsayin matar amininka da ya ba ka yarda kana faɗa min irin waɗannan maganganun hakan sam bai dace ba.”

Wata ‘yar dariyar da ta ba ta mamaki ya saki ya turo hula gaban goshi da gani cikin nishaɗi mai yawa yake.

Ya ce “Allah gaskiya na faɗa,abokina ya caɓa ya samu luntsumemiyar mace sai dai ya yi ta buga duniyarsa ya…

Cikin tsawa ta katse shi “Ka tsaya in sauka Usman! Ba tare da nuna damuwa da tsawar da ta yi mishi ba ya ƙara faɗaɗa fara’arsa “Wallahi yau cikin nishaɗi nake mai yawa,jerawa da macen da ta amsa sunanta ma ai ba ƙaramin cinyewa ba ne.”

Gaba ɗaya Hamida ta taso ta daddanƙara mishi magana ta ce kuma sai ta faɗi ma Abdurrashid ko a jikinsa sai shafa haɓarsa yake yana murmushi ya ce “In zan ba ki shawara ki yard kar ma ki soma gaya mishi don reshe zai iya juyewa da mujiya, ko in ce ke za ki kwana ciki don yardar da mijinki ya yi min.

Ta kuma cewa “Ka tsaya in sauka.” Ya ƙi tsayawa ta saukan kuma bai fasa murmushn ba.
Yana tsaida motar yana horn kafin mai gadi ya zo ya buɗe ta ɓalle murfin ta fice, lokacin da mai gadin ya wangale gate ɗin bai shiga da motar ba tsayawa ya yi yana duban Hamida da ke tafiya a fusace wata irin sha’awar ta na ƙara fizgar sa yana jin sai dai ya ɓata da Abdurrashid amma sai ya ba zuciyarsa abin da take so. Sai da ta sha kwana ya daina ganin ta sai ya juya kan motarsa bayan ya yi wa mai gadin da ke ta gaishe shi alheri.

Ita kam tana shiga ɗakinta rub da ciki ta yi bisa gado tana tunanin wannan al’amari mai ban takaici da ɗaure kai sai lissafin yadda za ta tunkari Abdurrashid da wannan zancen ta ce amininsa ya yi mata haka da ita zai yarda ko da shi gane rashin alfanun bayyana zancen ya sa ta bar shi a ranta.

Ba ta ƙara komawa gidan Usman ba waya ta yi wa Jamila ta yi mata ƙaryar ba ta da lafiya, ita kuma sai cewa take Allah ya sa ƙaruwa muka samu.

Ranar suna kan ba yadda za ta yi ta je.
Sai yamma liƙis da Abdurrashid ya zo wurin Usman da suka gama hirar su ya yi mata waya ta fito su tafi da ta fito yi ta yi kamar ba ta da lafiya don kar ta gaida Usman sai ta ji almurin yana cewa Abdurrashid “Madam kuwa lafiya take?” Kallon inda take tsaye za ta shiga mota Abdurrashid ya yi “To ni dai ban san wani abu na damun ta ba.” Ya faɗa motar suka bar wurin sai da ya hau titi ya dube ta “Me ya same ki ake cewa ko ba ki da lafiya? Fari ta yi masa ta kaɗa ido “Ni na cewa wani ba ni da lafiya?

Bai ce komai ba sai idonsa da ya mayar titi.

Hamida ta kammala Exam ɗinta ta ƙarshe ta dawo gida tana murna a gidan ta iske Abdurrashid gaban Computer shi yana aiki, ta ɗora hannuwanta kan kafaɗarsa ta rungume shi ta baya tana raɗa masa yau ta kammala karatunta.

Ya waiwayo sai ya janyo ta ya zaunar da ita kan cinyarsa, “Kin kammala sai a zauna gida kuma hakanan a huta Madam.”

Ta kaɗa hannu “Zan cigaba da karatuna sai na ga ƙarshen biro da takarda, ni ba yara ba gara in ta karatun zai ɗauke min hankali daga damuwar hakan a…. Hawayen da suka taho mata ya sa ta yi shiru sai ji ya yi hawayenta ya ɗigo masa a wuya ya sa hannuwansa ya tallafo fuskarta ya haɗa fuskokin su “Me ya sa kike son jayayya da hukuncin ubangiji? Duk waɗanda suke cikin duniyar nan ba a ba su haihuwar ba haka kika ga suna zama su yi ta koke-koke? Ki yi haƙuri daga an ce lafiyar mu ƙalau lokaci ne in sha Allah za mu haihu.”

Ya kamo ta suka miƙe tsaye sai ɗakin barcinsa a can aka idasa lallashin.

Washegari ta samu baƙuncin Walida don sun yi waya take shaida mata ta kammala Exam ɗinta sai duban ta Hamida ke yi don sun daɗe ba su haɗu ba, ta yi wata uwar ƙiba ta zama babbar mace, ba ta cika zama ba kullum ba ta nan ba ta can da ganin ta ka san ta bauɗe ta saki layi. Tunda ta kammala NCE ba ta ci-gaba da karatu ba a can ta haɗu da ƙawayen da idonta suka ƙara buɗewa ta fara hulɗa sosai da maza masu naira.
Sai karakaina Hamida ke yi tana cika ƙawarta ta da kayan maraba da baƙo.

Sai da suka yi nisa cikin hirar su Hamida ta ce “Ya kamata Walida ki yi aure hakanan, dubi aurena yanzu fa shekarata tara.” Ido Walida ta buɗe “Gaskiya kin daɗe da shiga ciki don dai shekaru biyar ɗin farko Ogan ba ya nan, to amma ni Hamida sai in ga meye maraba ta da ke, ko don kina cikin daula shi ya sa ba ki ga illar zaman da kike yi ba har yanzu ba haihuwa ba?

Gaba ɗaya Hamida ta ɗauke wuta in har Walida za ta yi mata gorin haihuwa to wa ya saura mata da ba zai mata ba?

Muryar Walidar ta ji “Kodayake kin san ana gadon rashin haihuwa shi gidansu ba gidan haihuwa ba ne abin ya sa ki tsakiya.”

Cikin danne fushinta Hamida ta ce “Komai na Allah ne ni na dogara gare shi.” Walidar ta ce “Kin ko yi farar dabara. Yawwa Hamida wata abaya da na ga kin sa a status na cikar auren ku shekara tara ita za ki ara min, akwai wata fita da za mu yi ba ta wasa ba ce,ki haɗa min da jaka da takalman da kika sa.”

“Haba dai ai kin wuce in ba ki aro, ina zuwa.” Ta faɗi tana yunƙurawa yadda ta ce haka ta haɗo mata har da kuɗi dubu goma tunanin ta ko Walidar ba ta da kuɗi a ɗan datsin shi ya sa ta nemi aron kayan don tana ganin hotunanta da take ɗorawa a kafafen sada zumunta ba ƙaramar shiga ta alfarma take ba.

Ta zo ta miƙa mata, leƙawa cikin ledar ta yi tana kallon kayan ganin kuɗin masifa ta kama a ranta “Ita wannan tana ba ni yan wannan kuɗin,tana tunanin yanzu da ce,kayan ma na tambaye ta ne don raba mugu da makami.

Hamida kuma tana ta ƙara mamakin ta a ranta na yadda ba ta taɓa ba ta abu ta iya furta kalmar godiya ba.

Suka ci gaba da hirar su har Walida ta yi shirin tafiya wani ne ya zo ya ɗauke ta. Da ta dawo rakiyarta ba ta zauna ba wurin Aunty Karima ta wuce suna hira har magrib nan ta yi sallah sai da Abdurrashid ya shigo bai zauna ba ya ce ta zo su tafi, sun fito yake ce mata Mami ta kawo ƙarar ta cikin mamaki ta dube shi da tambayar me ta yi ɗauke kai ya yi “Ta ce in kin shigo ba ki shiga ki gaishe ta.”

Sanin ba shigar take ba ya sa ta yi shiru. Ya ce “Mu je yanzu mu gaishe ta.” Suka karkata zuwa part ɗin Mamin, ba ita kaɗai suka samu ba su uku ne da wasu ‘yammata su biyu.

Sai da suka gaishe ta take ma Abdurrashid bayanin bai gane yammatan ba ? Ya ce “E.” Ta ce “Yaran Haj Hanne ne babbar ɗiyar Haj yar Gambo yayar mahaifisa. Ya kaɗa kansa ta ce “Saboda sun tashi a Lagos ne shi ya sa ba kowa ya san su ba daga ba cika zuwa Arewan suke ba.” Ta faɗi tana wani murmushi Ya miƙe Hamida ta mara masa baya suka bar falon ɗaya daga cikin su na cewa “Sai mun shigo Uncle.”

Ya ce “Ok.

Washegari ya dawo aiki yana cin abinci sai ga su sun shigo sai mamakin shigar da babbar ta yi Hamida ke yi matsattsun riga da skirt ne na English wear sai karairaya take kamar tarwaɗa.
Abdurrashid da bai wani sakar musu fuska ba daga gaishe shi da suka yi yana gama cin abincisa ya tashi ya shige ciki, Hamida ta ga kar ta bar su su kaɗai sai ta cigaba da zama ba ta bi bayan mijinta ba, tsaki dukkan su suka ja sai suka miƙe suka bar falon, ta bi su da kallon mamaki kafin ita ma ta miƙe ta bi mijinta.

<< Shirin Allah 24Shirin Allah 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.