Skip to content
Part 26 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Washegari ta fita game da karatu ta da take son ta jona masters ta tsaya restaurant ɗin Gwoggo,sun daɗe suna hira kan mutanen Daura dan sun kwana biyu ba su je ba ita da Gwoggon.

Sun gama ta rako ta inda ta parker motar ta ta ga wucewar baƙin yammatan nan na part ɗin Mami wanda take jin sunan su Anisa da Amira,babbar ce Anisa, ta faɗa motarta ta bi bayan ta su motar.
Ba ta shiga gidanta ba yankewa ta yi ta fara shiga wurin Aunty Karima ta gaishe ta don tana fama da mura,sai dai dokar da Abdurrashid ya sanya mata ta lallai ne ta shiga gidan sai ta shiga part ɗin Mami ba ta son ganin waɗannan yammatan ‘yan rainin wayau da ta rasa uwar da ta yi musu indai za su gan ta sai sun ƙirƙiri abin da zai ɓata mata rai.

Sun parker motar su ita ma ta parker kusan ma a tare suka fito tana rufe mota ta ji suna dariya “Ai ba ki san ‘yar tuwo tuwo ba ce taɓ! Ai anan ya gan ta ana tallar abinci.”

Ƙaramar Amira ta fashe da dariya “Allah Aunty Anisa shi ne take wannan yauƙin kamar wata ɗiyar saraki?

Anisar za ta yi magana sai ganin Abdurrashid suka yi da ba su san ta yadda ya zo wurin ba.
Hamida wadda cin fuskar da suka yi mata ya yi matuƙar yi mata zafi ta fasa shiga wurin Aunty Karima ta gefen Abdurrashid da ita ma ba ta san ya aka yi ya zo wurin ba ta bi ta wuce gidanta, ɗakin barcin su ta wuce ta hau gado ranta na ci-gaba da suya,sai muryar Abdurrashid ta ji kanta “In kin samu lokaci ki je ki faɗa wa Gwoggoki na ce ta bar saida abincin nan.”

Saurin tashi zaune Hamida ta yi ta zuba mishi ido, “Yes ta bari ta yi min lissafin abin da take samu a wata ki karɓo acc no ɗinta, ta kuma ba ki list na abincin da suke ci za a dinga kawo mata duk wata.”
Hamida ta karyar da kai “Anya za ka iya da Gwoggo Hamma? Da ka bar ta da sana’arta kar ta zo…
Kina ganin ba zan iya riƙe ta ba ne, ko kina ganin duk abin da take samu ban da arziƙin ba ta?
Kwantar da kanta ta yi duk yadda ranta ke ɓace ganin yadda ya hasala kuma bai san nufin ta ba don ba za ta fito kai tsaye ta faɗa mishi Gwoggonta ba ta da godiyar Allah duk yadda zai kai ga kyautata mata sai ta yi ƙorafi.

“Ba ka gane ba Hamma ka bar ta da sana’arta saboda yau da…

“Yin sana’arta ba zai zama abin da za a riƙa goranta miki ba. Shiru Hamida ta yi gane cin fuskar da aka yi mata ya sa ya ce Gwoggonta ta bar sana’arta.

Washegari ta shirya ta tafi wurin Gwoggonta a wurin sayar da abincinta sai da suka keɓe ta faɗa mata saƙon Abdurrashid duk da hango ci da ta yi sai da ta ciza “A’a fa Hamida kin san mijinki ba son taɓuwa yake ba.”

Hamida ta gyara zama “Kin san dai halinsa Gwoggo idan ba zai yi abu ba ba zai ce zai yi ba.”
Ta ce “Shi kenan, idan aka rubuta zan kawo ne? Hamida ta ce A’a ni zan rubuta miki Gwoggo yau ina nan tare da ke har ki tashi har abinci zan taya ki sayarwa.”

Gwoggo ta riƙe baki suka yi dariya a tare ta ce “Rufa min asiri. Ta tashi ta fita tana ci gaba da da dariyar.

Nan Hamida ta zauna har sai da Abdurrashid ya koma gida ya kira ta a waya sai ta yi wa Gwoggon sallama ta koma gida.

Washegari tana kwance a falonta sai ganin shigowar su Anisa ta yi, ba ta ko motsa ba har suka zauna. Sai dai ta ƙudura yau suka yi mata rainin wayo ci musu za ta yi, da ma tana ƙyale su ne don ba ta son wata fitina ta hada ta da dangin miji Amira ta fara magana “Na ƙosa Aunty a yi a yi ki shigo ki santalo mana baby kalar uncle daga ke kin gaji haihuwa ba juya ba ce, ba su cogal ba ana tafe ana dingisawa a haka a ka mutu kan su.”

Gabaɗaya Hamida ta miƙe sai dai kafin ta fara ce musu komai Abdurrashid da ke ciki ya tako tsakiyar falon kaca kaca ya yi musu ya ce su fita harkar matarsa kar ƙafar wadda ya kara gani. Ya dubi Anisa a fusace “A haka kike tunanin za a aure ki ballagaza kawai.”

Ta fashe da kuka ta ruga da gudu ta fice falon Amirar ta mara mata baya.

Hamida ta koma ta kwanta ya tako zuwa inda take ya zauna kanta ya ɗora saman cinyarsa, sai ya yaye zanenta yana shafa ƙafarta da aka gama yi wa gori don ɗan adam tara yake bai cika goma ba tun Hamida na ƙarama ƙafarta ta ɗan buɗe tana girma tana raguwa to yanzu da ta girma sai ka sa ido da kyau za ka gane kafar ta ɗan buɗen.

Kamar an tsikare ta ta tuna kalaman Amira ta tashi zaune ta tambayi Abdurrashid aka turo ƙofar Haj yar Gambo ce ta shigo a fusace tun kafin ta ƙaraso ta soma jidali “Ka kori yar’uwarka saboda matarka, to ko me za ka yi aure ba fashi,daga ko ubanka bai isa ya musa ba.

Za a ɗaura aurenka da Anisa ko za ka samu rabo, kana zaune da mata kusan shekara goma ba haihuwa kai an haife ka kai kaɗai ba ka fatan ka haifa, shi ma uban naka da yake cewa ita ma ɗiyarsa ce don yar amininsa ce wa ya fi kusa da shi ita da Anisa?Cikin watan nan, za a sanya rana matar taka ta faɗi ta mutu.” Ta juya a fusace.

Aka shiga kallon kallo Abdurrashid da Hamida kafin ta fashe da kuka “Aure za a yi maka saboda ban haihu ba?

Sai ta miƙe ta nufi ɗakinta ta rufe, ya yi bugun duniya da ban bakin ta buɗe amma ta ƙi.
Da safe ma ba ta fito ba har sai da ya kira Aunty Karima, kira ɗaya Auntyn ta yi mata ta zo ta buɗe ta fito kanta a ƙasa tana gaida Auntyn.

Aunty Karima ta dubi agogo “Hakanan ki azabtar da kanki, shiga kitchen ko Tea ki haɗo ki zo ki sha. Kitchen din ta wuce ba ta yarda ta dubi inda Abdurrashid ke zaune ba, ta haɗa ta fito a ƙasa ta zauna tana kurɓa a hankali.

Aunty ta fara magana “Me zai sa ki rufe ƙofa? Ki yi haƙuri da abin da kika ji,ko Alh ba a san ransa yaya ta ƙulla wannan magana ba, amma ba yadda zai yi da ita. A maimakon fushi da addu’a kika kama kika yi ta yi inda sharri za a nufo ki Allah ya mayar wa Mutum abin sa.

Haihuwa ta Allah ce, wanda ya so yake ba mu ba ga mu zaune ba, ita Haj Mariyar da ta ƙulla abin ta haihun ne?

Ba hakana Alh ya zauna da mu ba? Haihuwa lokaci ne ko ni ban fidda rai ba ballantana ke da duka duka yaushe aka yi daren. Ki kyale su su yi ta abin su ,in sun aura mishi ita akan ki za ta zauna ki yi ƙoƙari dai ki kyautatawa mijinki shi ne ba wata kishiya ba,ki yi haƙuri don Allah.

Hamida da ta kasa ci gaba da shan Tea jin da gaske dai kishiya za a yi mata, wata za a kawo su raba Abdurrashid da ita. Ta share hawaye ganin Auntyn ta mike ta fita Abdurrashid ya bi bayanta me mata aiki cikin masu aikin Aunty karima take ta kan taimaka mata saboda fita makaranta da take ta shigo sai da ta fara gaishe ta kafin ta soma ayyukan da take yi.

Hamida kuma kitchen ta shiga don yi musu girki tana yi kuma tana share hawaye.

Dole ta tilasta ma kanta haƙuri amma ƙasan zuciyarta kamar ta yi ta zunduma ihu.

Su Anisan ma ba ta ƙara ganin su ba tun daga ranar don ko gidan ta shiga ba ta shiga part ɗin Mami,tunda ta ji Aunty Karima ta ce ita ta ƙulla a yi mata kishiya take jin haushin matar.

Abdurrashid ya samu canjin wurin aiki shi da Usman zuwa barrack ɗin Abuja shi kaɗai ya tafi ya bar Hamida ranar da ya tafi sai ga yaran Mimi da Hanan.

Hanan yaranta biyu Mimi tana da guda daya sai cikin na biyun, Affan yaron Mimi sai Afrah yar wajen Hanan, wai sun kawo yaran su taya ta zama kwana ɗaya suka yi suka tafi suka bar mata yaran, ta kan rungume yaran ta yi hawaye mai isar ta kafin ta share.

Ta ji daɗin zuwan yaran sun ɗebe mata kewa sam ba ta gajiya da hidimar su, ana gobe za su tafi ya yi daidai da satin su biyu Abdurrashid ya ce mata ga shi nan zuwa.

Cikin dare ya iso don kafin ta kwanta sun yi waya da Gwoggo Indo take tambayarta Abdurrashid yaushe zai zo?

Ta ce bai faɗa mata ba, Ai kuwa sai ga Gwoggo ta yo sammako, a falo suka zauna Gwoggo na cewa “Bikin Yusuf dai na ta matsowa.” (Ƙanen Hamida da ke bi mata) Hamida ta ce “E.”

Ta ce “To me za ki yi musu don mijinki ya kamata ace ya yi komai, amma ba zai iya ba.”

Shiru Hamida ta yi takaici ya hana ta ce mata yana ciki Gwoggo ta cigaba “To ni dai kuɗin da na faɗi ba su isa ta ki faɗi mishi.”

A ran Hamida ta ce ɗaya kenan.

Kwantar da murya ta yi ta ce “Ke fa kika faɗi Gwoggo.”

“To daɗi miji, idan ba za ki faɗi mishi ba ke sai ki dinga ba ni, kina da miji mai kuɗi ba za ki dinga tambaya ya ba ki ba, yanzu ki duba gidanmu kowa ya gyara sasansu na ku fa mijinki ya gaza gyarawa, ke kuma ba za ki faɗi mishi ba ” “Zai gyara Gwoggo,ba ya ba su gida ba sun ce ba za su koma ba wanda yanzu Yusuf zai zauna.”

Ta faɗi cikin takaici Gwoggon ma ina ta tsaya jin ta miƙewa ta yi Hamida ta bi ta a baya.

Kwana biyu Abdurrashid ya yi har kuma ya koma bai nuna ma Hamida ya ji zancen su da Gwoggonta ba ita kuma ba ta ce masa komai ba, illa dai da suka tafi bikin ƙanen nata ita ma kam sai ta ji ba daɗi, kusan gabaɗaya gidan an tsara shi an mayar da shi ginin zamani kowa ya gyara wa iyayensa su Innawuro Engineer ya gina ma Malam tafkeken gida amma Malam ya ce ba zai tashi daga nan ba shi ne ya gyara musu sasan su.

Laila ta gyara ma nata iyayen da daɗewa. Aina ta gyara nasu.

Su Amina ne sasan su ba wani mai ƙarfi da Hamida ta tashi gyara nasu sai ta haɗa ta yi musu iri ɗaya ta mayar da shi na siminti a maimakon na ƙasa da, ba dai ta yi kamar na sauran ba.

Abdurrashid da ya sai musu gida ƙi suka yi su koma.

Abin da dai ya sanyaya mata rai da Abdurrashid ya haɗa wa Yusuf akwati har sadaki da abin da za a ci duka shi ya yi, nata da ta ruƙo za ta yi hidimar sai ta ba mahaifinta.

Ana gobe ɗaurin auren Abdurrashid ya iso ya sauka gidan Engineer da ya saya don sauka idan ya zo garin.

Da zai tafi masauki da daddare ya tilasta Hamida sai sun tafi tare,sulalewa ta yi suka tafi sanin ba mai ma gane ba ta nan don jama’a da ta yi yawa.

Da ta tashi tun da safe yana barci ta zame ta gudu.
Engineer ma ranar ɗaurin auren ya iso tare da Aunty Karima. Ana gama ɗaurin ya wuce Abuja,dama daga can ya zo.

Ko da aka ƙare biki Hamida ta kwana biyu a Daura don ta daɗe rabon ta da garin nan Gwoggo da Laila suka tafi suka bar ta, Aina ma ta zo da yaranta biyu duka maza.

San da ta koma Kano ta samu Abdurrashid ya zo kwanan shi biyu sati guda zai yi.
Usman ma ya tafi da Jamila ta ma kira ta a waya ta yi mata sallama lokacin tana Daura.

Washegarin da ta dawo ta idar da sallar sallar Isha’i tana shirin kwanciya, Abdurrashid ya shigo ya same ta, cikin jallabiya yake da Hamida ta ga ya matuƙar ƙara yi mata kyau a cikin ta, ta yi murmushi tana jin wata ƙaunarsa mai tsanani tana ƙara shigar ta

“Zan je wurin Daddy in dawo.” Ta ce “To ka gaishe da Daddy.”

Ta juya ta ci gaba da taje gashinta sai ta sanya hula ta sa rigar barci ta fito falo sai ta ji gabaɗaya zuciyarta ba ta kwanta da fitar Abdurrashid a daren nan ba. Ƙofar falon ta buɗe ta fita, ƙofar da ta haɗa gidajen nasu a buɗe take bai rufe ba turawa kawai ta yi ta ji ta buɗe sai ta shiga ta fara tafiya ta hango mutane biyu tsaye, kallon tsaf ta yi musu ta gane Abdurrashid ne, don inda suke ba wadataccen haske. Gabanta ya shiga lugude tabbatar da Anisa ce,ta ƙara takawa ɗaya biyu sai ta ja ta tsaya don ƙafarta da ta ji ta riƙe, Abdurrashid ya ba ta baya Anisa sai karairaya take daga inda take ba za ta zolayi kanta ba daddaɗan ƙamshin turaren yan Maiduguri har daga inda take tana shaƙarsa. Ta yi ta yi ta ja ƙafar amma ta kasa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 25Shirin Allah 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.