Skip to content
Part 27 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Sun ɗauki ya yi minti ashirin kafin ya wuce, Anisa kuma ta yi part ɗinsu.

Sai sannan ta samu ta ɗaga ƙafarta da ta riƙa ji kamar ba za ta ɗauke ta ba, ɗakin barcinta ta koma “Namiji munafiki” abin da take faɗi kenan a ranta yayin da ta rintse idonta hoton Abdurrashid da Anisa na gilma mata, ƙirjinta ta dafe da wani baƙin ciki ya tokare.

Tana cikin da hawaye ta ji shigowar sa, ƙara rintse idonta ta yi “Yau nan za mu kwana kenan Madam? Ta ji muryarsa sai kuma ta ji ya fita.

Ba a daɗe ba ya dawo gadon ya hau ya kwanta a bayanta ya rungume ta, jin ta ƙanƙame jikinta ya ƙyale ta ya shiga barci.

Da gaske dai Abdurrashid aure zai yi kuma kanuri zai auro mata da take ji ake cewa sun iya riƙe miji, gaskiya ne ko da wannan fitinannen ƙamshin sa janye namiji, ita kam tana sayen turaren feshi da Air freshener amma su humra turaren wuta ba su gabanta, ta ina za ta soma ne? Ta tambayi kanta.
Da ƙyar ta samu barci ya ɗauke ta.

Da gari ya waye da wuri ta tashi ta fara ayyukanta, sai zuci-zuci take Abdurrashid ya fita gidan.
Bai fita ba sai ƙarfe uku ta ce ita ma za ta je ma wata course mate ɗinta barka ta haihu. Ya ce ta zo su fita tare ya sauke ta ta ce A’a ya je kawai ita sai ta yi la’asar.

Yana fita dama a shirye take jakarta da ta sanya Atm ɗinta da wayarta ta rataya sai matafinta,da kanta ta ja motar ta bar gidan.

Wani Mall da suke zuwa ta yi wa tsinke, wani shago na saida turaruka da ke kusa da wanda take zuwa a saman shi an rubuta *HAJJA YANAH KANURI* ta shiga, a saman bene yake hawa na biyu.

Masu aikin wurin sun tare ta da maraba, mai wurin da ke zaune a wuri na musamman hango shigowar Hamida da ganin ta a jiƙe take jagab cikin Naira ya sa ta ce wa ɗaya cikin masu aikin ta ta kawo mata ita.

Ta isa Hajiyar ta yi mata maraba aka ba ta wurin zama har da lemo aka kawo mata ta ce “Me kike so ƙanwata?

Sai da Hamida ta ja wata gwauruwar ajiyar zuciya ta ce “Ina son humra masu kyau da turarukan ɗaki.”

Ta ce “Da waɗanne iri kike amfani?

Ta girgiza kai “Ban amfani da su yanzu dai zan fara.” Cikin mamaki ta buɗe baki kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa ta miƙe, Hamida sai kallon ta take yadda har ƙafafuwanta ke iya ɗaukar gangar jikinta saboda tsananin ƙibarta.

Kala-kala ta zaɓo ta dawo ta ajiye su gaban Hamida “Waɗannan suna matuƙar kyau,sai dai suna da tsada.”

Hamida ta ɗauka tana shinshinawa tana lumshe ido ƙamshin su ya gamsar da ita.
Ta kuma tashi ta ɗebo humrori “Waɗannan ma na musamman ne, su ɗin ma duk sun yi ma Hamida, a jikin kowanne akwai kuɗinsa, Atm ta miƙa masu su cire kuɗaɗensu Hajiyar ta ce “Daga kin ce ba ki amfani da su ƙanwata, ga abin da za ki dinga turara suturunki, ga kuma su bunner ya kamata ki s gaaya.”

Ba musu Hamida ta saisaya.

Har ta miƙe ai yafuto ta Hamida ta dawo sai da ta rage murya ta ce “Ba za ki sayi na gyaran aure ba?

Muna kuma yin gyaran jiki.”

Hamida ta ce “Ina so.”

Wani itatuwan turare ta ɗauko ta ce “Kin ga wannan sai mace ta isa, kina tsuguno da su mijinki zai ji ki daban, ba zan iya tsayawa yi miki bayani ba sai kin gwada, kar ma ki biya sai kin gwada.”

Hamida ta saki ajiyar zuciya “Na gode, ina so, ina ake gyaran jikin?

Ta ce “Ciki ne,yarana ke yi, amma zan miki da kaina.”

Suka shiga inda ake yi, kamar yadda ta cen da kanta ta yi mata.

Awanni suka ɗauka wanda ya ja lokaci.

Yamma sosai aka kammala ta ce “Kyan ki sati guda za ki samu kina zuwa ƙanwata, zan gyara ki sosai.”

Hamida ta yi murmushi “Na gode sosai in sha Allah zan zo.”

Suka yi musayar lambar waya, ta sa yaranta suka ɗaukar wa Hamida amma ban da wanda ta ce na tsuguno ne ta ce Hamida ta sanya a jakarta ta kula da shi kamar yadda za ta adana da kudadenta.

Sun yi sallama ta yi mata godiya sai da ta shiga mota fargaba ta rufe ta yamma ta yi sosai kar Abdurrashid ya riga ta dawowa,sai addu’a take har ta isa, ilai kuwa motar da ya fita da ita ga ta nan a ajiye, ta ɗauki kayanta ta nufi ciki yana zaune falo idonsa na kan TV motsin buɗe ƙofar da ƙarar takalmanta bai sa ya ɗago ba, ta isa inda yake jin bai amsa sallamarta ba ta ce “Sannu da hutawa.”

Ko motsi bai yi ba gabanta ya ƙara faɗuwa ta wuce ciki alwala ta yi jin an soma kiran sallah.

Tana idar da sallah ta ciro kayanta bunner ta kunna ta ciro kayan da za ta sanya ta turara, sannan ta fita falo shi ma ta sa turaren sai ta wuce bed room ɗinsa don bunner uku ta sawo shi ma ta sanya mishi ta ƙara gyara shimfiɗar sai ta fito.

Knocking ta ji ana yi ta isa ta buɗe mai aikin Aunty Karima ce ta kawo abinci don har yanzu daga can ake kawo mata, ta kan faɗi abin da take so in kuma za ta shiga kitchen da kanta sai ta shaida musu.

Sai da ta shirya tebur ta wuce ɗaki, bayan ta gamsu da daddaɗan ƙamshin da ko’ina ya ɗauka wanka ta shiga bayan ta haɗa wani ruwan turaren da ta sawo wanda Haj Yanah ta ce kar ta yi wasa da shi matuƙar namiji ya shaƙa sai ya biyo, ta gama ta fito ta yi kwalliyarta ta shafa humrorinta kayan da ta turara ta ɗauko ta sanya riga ne da skirt na material da suka yi mata dam! Ko’ina ya fito ta ɗaura ɗankwalin, ta tsaya shawarar ta yi turaren tsugunon ko ta bari sai anjima ƙarshe dai ta yanke ta yi yanzu, key ta danna ma ɗakin duk da sanin Abdurrashid na fushi da ita ba zai zo ba sai da ta gama ta fito ta samu Abdurrashid zaune ya fara cin abinci ta ƙarasa ta zauna “Sannu da zuwa.” Wani kallo ya ɗago ya yi mata sai ya ci gaba da cin abincinsa, ta zuba ta fara ci “Ina kika tsaya har magrib? Ta tsinkayi muryarsa ba zato cikin kanta. “Shopping Mall na biya na sawo turare.”

Ta faɗi da sanyin murya “Amma kin san ban son ki fita ki kai magrib ko? Ta ce “Ka yi haƙuri don Allah.”

Bai ƙara magana ba har ya kammala sai ya koma kan kujerun falon ya zauna, ta tattara kayan abincin ta kai kitchen sai ita ma ta zauna, miƙewa ta ga ya yi ya nufi ɗakinsa ta bi bayansa da kallo a ranta tana faɗin “Fushin bai ƙare ba kenan ko da na bayar da haƙuri?

Tun tana jiran zai fito sai ta ji shiru don suna daɗewa suna hira kafin su kwanta.

Ranta ya ɓaci tana ta masifa a ranta ba don Aljanna da kake nema ba aljanna kuma ba ta samuwa ta sauƙi, yaushe za ka zauna a yi ta maka wannan latsin?

Ta miƙe ta fara kashe kayan kallon da nufin ta wuce ɗakinta ta kwanta ta ji wayarta ta soma ƙara, hannu ta kai ta ɗauko ta sai ta ga shi ne tana picking ya kashe ta san kiran ta yake.

Ta kama hanyar ɗakin nasa, tura ƙofar hango shi ta yi ya yi ɗaiɗai bisa gadonsa daga shi sai guntun wando ƙirjinasa ta kalla sai ta ji wani shauƙi ya kamata hannayensa ya miƙo mata ba ta yi saurin zuwa ba ta ce “Zan je in canza kaya.”
Ƙara miƙo mata hannun ya yi ta ƙarasa ya janyo ta ya sa ta cikin jikinsa, wasu tagwayen ajiyar zuciya ta ji ya fidda wanda ta san sai ya daɗe rabon shi da ita yake yin hakan.

A wannan daren Hamida ta ga tarairaya da soyayya na musamman har safiya ji yake da ita.

Sun gama break past ta yi wanka nan ma bin gaɓoɓinta ta yi da humrorin, ta turara kayan da za ta sanya doguwar riga ce, ta shiga ɗakin ogan don gyarawa sai ga shi ya shigo “Ki fito ku gaisa da Usman.” Nan da nan ta sha mur ya gyara tsayuwa “Wai meye haka da na ce Usman sai ki ɓata rai?

Shiru ta yi ba ta tanka ba “Ki fito ku gaisa.” Ya faɗi sai ya juya ta raka shi da ido.
Sai da ta kammala gyaran ta fito ta same su falon ta zauna ta soma gaishe shi yana amsawa cikin fara’a, knocking ɗin da ake ya sa Abdurrashid miƙewa ya nufi ƙofar ganin mai gadi ne sai ya fita suna magana.

Usman na ganin ya fita ya juyo gaba ɗaya wurin Hamida “Madam kenan sai ƙara kyau kike abokina na hutawa, dubi safiyar nan amma ko’ina ƙamshi yake mai kwantar da hankali, ke kanki ƙamshi kike mai tayar da sha’awa.”

Zumbur ta miƙe “A’uzubillahi minashshaiɗanir rajim, ina neman tsarin Allah daga shaiɗancinka Allah ya.. Jin ƙarar buɗe ƙofa ya sa ta yin shiru sai ta dafe kanta, Abdurrashid ya shigo ganin ta dafe da kai ya sa ya ce “Lafiya? Ta ce “Kaina ke ciwo.” Ya ƙaraso inda take “Shiga ciki ki sha magani.” Sai kawai ta ɗora kanta jikinsa ya fara tafiya zuwa ɗakinsa, suna shiga ta mamutse shi zuwa gado ganin abin da take yi duk da hankalinsa ya fara tashi ya ce “Me kike yi haka? Ga Usman can na bari a falo.”
Hannunta ta cusa cikin jikinsa wata irin shafa take yi masa wadda ta sanya shi manta komai, sai ita kaɗai yake so.

Ta gamsar da shi matuƙa da gaske sai da ya dawo daga duniyar da ta kai shi ya ce “Kash yanzu me zan ce wa Usman?

A ranta ta ce “Ɗan iska ba? Ya gaji ya kama gabansa.

Jallabiya ya sa ya fita ta gyara kwanciya ta shiga barci don ba ta san yadda suka ƙare ba. Ta farka ta shiga bathroom ta tsarkake jikinta sai ta fito ta mayar da kayanta a falo ba ta ga Abdurrashid ba sai ta zauna tana taɓa wayarta. Cikin masu aikin Mami ta yi knocking sai ta buɗe goro da sweet da cingam take ɗauke da su niƙi-niƙi “Wai in ji Mami na sa ranar Anisa.” Cikin ɗaure fuska tana hararar ta Hamida ta ce “Na sa ranar ta da wa? Sunkuyar da kanta ta yi cikin daka tsawa ta maimaita na ce “Sa ranar ta da wa? Jikin yarinyar ya ɗauki ɓari cikin rawar baki ta ce “Da yallaɓai.”

Juyawa kawai Hamida ta yi ta rufe ƙofarta yayin da ta bar yarinya da tararrabi, don ta san ba ta isa ta koma ma Mami da waɗannan kaya ba, ga wadda aka kawo ma wa ba ta karɓa ba, duƙawa ta yi ta ajiye su a ƙofar ta koma inda ta fito cikin sanyin jiki.

Abdurrashid ya dawo daga fitar da suka yi da Usman yana buɗe ƙofa goro da sweet suka yi mishi maraba. Da mamaki ya wuce ya buɗe ƙofa ya shiga yana ƙwala kiran sunan Hamida, jin shiru ya sa ya nufi ɗakinta. Rub da ciki ya same ta tana zuba kuka, daga inda yake ya soma tambayar ta abin da ya same ta ba ta yi magana ba har sai da ya ce bari ya kira Aunty Karima ko ta san abin da ke faruwa.

Saurin tashi zaune ta yi “Don za ka yi aure Abdurrashid, wani duba ya yi mata jin ta ambaci sunan sa da ko da wasa bai taɓa ji ta faɗi ba, sai dai ta kira shi Hamma kamar yadda ƙannensa ke kiransa.

“Sai a riƙa ci min fuska, a aiko min kayan sa ranar ka.”

Ido ya zuba mata kafin ya ce “To ki yi haƙuri.” Maganganu ta ci-gaba da saki da suke nuna tsantsan kishin da take ciki yana sauraren ta.

Kiran wayarsa da daddynsa ya yi ya sa ya juya ya bar ɗakin, ita kuma ta yi amfani da hakan ta ja mayafinta ta fito ta bar gidan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 26Shirin Allah 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.