Skip to content
Part 24 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Hamida ta ji jiki hannun Abdurrashid sai da ya gamsar da kanshi ya koma gu daya yana mayar da numfashi, ita kuma barcin wahala ne ya dauke ta.

Sai da ta farka ta ga sai ita kadai ba Abdurrashid, lallabawa ta yi ta tashi zuwa bathroom ta yi wanka ta fito ta koma ɗakinta, sallar la’asar ta yi sai ta yi kwalliya wata doguwar riga ta ɗauko cikin kayanta da Aunty Karima ta ce ta fara kawowa daga kowane lokaci Abdurrashid zai iya dawowa.

Ta yi kyau sosai ta fito tana ƙamshi mai daɗi.

Abdurrashid ta gani da Usman zaune a falon ta ƙarasa ta zauna tana gaida Usman saƙo da ta ji ya shigo wayarta ya sa ta dubawa Abdurrashid ne ke gaya mata ta koma ɗaki cak ta miƙe ta kama hanya Usman ya bi bayanta da kallo, don tun rabuwar su ya kasa samun sukuni da ya tuna abin da Abdurrashid zai yi da Hamida da zarar sun isa gida sai ya hankalinsa ya ƙara ɗagawa, shi ya sa ya yi ta kiran Abdurrashid a waya wai ko idan ya ɗauka ya fahimci halin da yake ciki amma sam bai ɗaga wayar ba hakan ma ya ƙara tada mishi hankali tabbatar da zarginsa.

Key ɗinsa ya ɗauka don barin gidan matarsa Jamila da ke ta rawar jiki miji ya dawo ta ga zai fice da ta nemi sanin inda za shi daga dawowa ya ce ma ruwa ya yi wurin Abdurrashid yanzu zai dawo bai tsaya sauraren ta ba bare ɓacin ran da ta nuna.

Yana isa ya samu Abdurrashid ya fito zuwa masallaci tare suka yi sallar sai suka shiga ciki.

Hamida da ta shiga ɗaki wayarta ta janyo ta kunna ta ta shiga Whatsapp saƙon Hanan da Mimi ta yi ta gani suna mata tsiya ta bi miji ta bar su.

Murmushi kawai take yi Abdurrashid ya shigo ta ɗaga ido ta dube shi “Wai ke ba ki da wasu kaya sai irin waɗannan ta dubi jikinta doguwar riga ce da ta kamata daga sama sai aka buɗe ta daga ƙasa bai saurari amsar ta ba ya shiga ciro kayanta cikin wardrobe ganin duk irin su ne ya ja tsaki ke a tafiyar da na yi gaba ɗaya ma kin manta ke matar aure ce sai ya juya ya bar ɗakin.

Bayan tafiyar Usman ɗaukar ta ya yi suka fita wani babban Mall ya kai ta ya zaɓar mata kaya irin waɗanda suka yi daidai da ra’ayin sa na ɗinki ya bayar da ɗinki sai suka tafi gida yana gaya mata waɗancan shi kaɗai za ta riƙa sanya nawa.

Kwanakin da suka biyo baya amarci kawai suke kwasa ba shiga ba fita Hamida da Abdurrashid ban da ma Usman da ke yawan takura musu da zuwa shi kuma matarsa Jamila ta yi ma Abdurrashid waya ta kai mishi ƙarar Usman ɗin tunda ya dawo ya birkice mata, ga yawan fita baya son zama a gida. Haƙuri ya ba ta da ya yi ma Usman magana cewa ya yi share ta ƙorafi ne irin na mata.
Abdurrashid ya ce a’a dai mutumina ka dai gyara.

Ganin ba su da niyyar komawa Yola bikin Mimi, Hamida ta tambayi Abdurrashid ya ce ba inda za su amarci suke.

Kuka ta yi ta yi bai saurare ta ba ganin hakan ba zai fisshe ta ya sa ta canza dabara.
Ya fita sallar magrib ta sheƙa kwalliya ga ƙamshi na musamman tana yi wasu riga da wando ta sanya rigar kamar best take ta kama jikinta sai guntun wando da mazaunai kawai ya rufe mata ya shigo ya ga fitilun falo a kashe sai hasken TV da ke magana.

Cikin matuƙar mamaki ya nufi wurin kunnawa carab! Ya ji an rungume shi ta baya wani mamakin ya kuma kama shi don bai yi zaton Hamida za ta iya masa haka ba, ya birkito ta gaban shi sai ya kunna wutar yadda ya gan ta sai ya ɗauke wuta kan kujera ya ja ta duk wasu wasanni da yake mata yau ta zage tana yi masa, gaba ɗaya ta sukurkuta shi ta gigita shi don ta mayar mishi da martani ba kullum da take barin sa ya yi kiɗansa da rawarsa don kunya da rashin sabo.

Maganganun da yake mata cikin fitar hayyaci ya sa ta fara kukan kissa wanda ya kiɗima shi yana tambayar ta meye ta ce bikin Hanan ya ce yaushe kike so mu tafi? Ta ce “Gobe.” Sumarta ya shafa sai ya gyaɗa kai.

Bayan lafawar komai ɗaki ta wuce ta gyara jikinta sai ta fito Usman ta gani zaune da matarsa a falon cikin fara’a ta ƙarasa ta zauna tana masu maraba kafin ta miƙe ta kawo musu ruwa da lemo ta wutsiyar ido ta dubi Abdurrashid da ke zaune kamar bai gama wattsakewa ba.

A cikin hirar su ta ji yana gaya wa Usman gobe za su koma Yola biki don jibi ne bikin.
Sun shiga ciki da Jamila ta samu ta gujewa mayataccen kallon da Usman ke mata wanda ya fara damun ta.

Da ta yi wa Abdurrashid complain ɗin abokinsa ya cika yawan kallo cewa ya yi haka yake tun ba mata ba shi ya sa nake so in za ki fito ki riƙa rufe jikinki.

Sun ɗan taɓa hira da Jamila kafin suka tashi tafiya ta haɗa mata kayan kwalliya ta bi ta da su zuwa mota sai da suka tafi suka juyo.

Hakan aka yi washegari suka kama hanyar Yola. Sun sha shagalin biki inda aka kai Amarya Bauchi.
Duk yadda Abdurrashid ya kasa ya tsare sai da ya tafi ya bar Hamida don Monday zai koma office kuma Aunty Karima ta ce sai Monday za su koma ita da Hamida.

Hamida na can suka yi waya da su Innawuro inda ta ba ta labarin zuwan Abdurrashid da alherin da ya baibaye su da shi,sai ta gane daga Adamawa Daura ya wuce.

Ranar da suka dawo da hantsi suka dawo Hamida ta gyara wurinta ta yi girki da kanta saboda Abdurrashid, ta yi wanka da kwalliya na jiran mijinta sai ta tafi wurin Aunty Karima don gaida Engineer Shehu Bello wanda shi ma jiya ya dawo ƙasar.

Da ta dawo daga gaishe shi ta je ta gaida Mami sai ta yi ƙarshe da wurin Aunty Karima ba ta so Abdurrashid ya dawo tana nan ga Aunty Karima na mata hira hakanan dai ta daure ta ce za ta koma gida Auntyn ta ce muna hira ta yi murmushi ta ɗan ƙara zama sai kuma ta miƙe ta yi mata sallama ta fita ta zo ƙofar da ta raba gidajen nasu tana turawa suka yi kaciɓis da Abdurrashid murmushi suka yi wa juna don sun yi missing ɗin juna na kwana biyu hannunta ya kamo ya sa ta jikinsa suka nufi gidansu falon su suka yi masauki sai da ya gama yamutsa ta ya sake ta da ƙyar suka ci abinci sai suka shiga ɗaki.

Ganin ya je Daura ya gaishe su washegarin dawowar ta da yamma ta same shi da zancen su je gidan Gwoggonta da ganin fuskarsa bai so ba sai dai bai yi musu ba.

A ƙafa suka taka suna shan gaisuwa daga mutanen Estate ɗin idan sun hadu da su. Gwoggo tana ta ina aka saka ina aka aje da su, zaman awa ɗaya suka yi ya ce su koma gida ba ta ji daɗi ba sam da ko kwabo bai ba Gwoggonta ba tana mamakin yadda yake wa ‘yan Daura alheri amma bai son ba Gwoggonta. Har sun fita ta ce mishi tana zuwa ta koma ciki ta miƙa wa Gwoggonta kuɗin da ta sanyo a jakarta “Ga shi in ji shi.” Gwoggon ta amsa tana ƙoƙarin ƙirgawa tana taɓe baki “Shi duk kuɗinsa iya alherinsa kenan?

Hamida ta juya tana faɗin “Sai mun yi waya Gwoggo.”

Abdurrashid da ya koma bakin aikinsa Hamida ma ta koma makaranta.

Ranar wata Laraba ta dawo makaranta Abdurrashid ya je aiki Kaduna jiya ya tafi kwana uku zai yi.
A gajiye take sam ta manta ta sa key ma ƙofar falonta ɗakinta ta wuce ta rage kayan jikinta don zafi da ake ba kama hannun yaro, doguwar riga ce a jikinta ta saman ta cire ta bar ta ƙasan mara hannu, kanta ba ɗankwali ta fito falo tana miƙa Usman da ta gani zaune cikin ɗaya daga cikin kujerun falon ya sa ta gintse hammar, ta juya ciki da sauri mayar da yar saman rigar ta yi ta ɗaura gyalen rigar sai ta kuma fitowa yana zaune inda ta bar shi yana aika mata kallon da ta tsana yake kuma takura ta ba sakin fuska ta yi mishi sannu da zuwa shi kam sai faman murmushi yake, ta wuce ta kawo mishi lemo da ruwa ba ta zauna ba kitchen ɗinta ta wuce ta zuba abincinta ta ci sai da ta gama ta zubo ta kawo mishi ta koma nesa da shi ta zauna labari yake ta mata tana amsa shi da ƙyar wata har yamma ta fara ya ƙi tafiya gaba ɗaya ta takura don yana yawan yi mata haka idan Abdurrashid ba ya nan ya zo ya yi mata zaune kuma ta lura baya son ta kawo mishi laifin abokin na shi wata leda da ya ajiye ya miƙo mata yana miƙewa “Ga wannan na sawo maku ke da Jamila “Ba ta tashi ba ta ce “An gode.
Sai ya yi ɗan sororo ya ajiye a wani ɗan stool da ke kusa da shi ya fita ta bi ƙeyarsa da harara.

Nan ta bar ledar ba ta taɓa ba har Abdurrashid ya dawo ganin ya dawo ya same ta har an kwana tana nan inda ya bar ta ba ta ɗauke ba ya magantu “Ledar meye wannan ke ajiye tun dawowa ta ba ki ɗauke ba? ta dubi ledar kamar ba ta son magana ta ce “Usman ne ya kawo min da ya zo.”

Ya ɓata rai “Wai meke damunki game da Usman Hamida abokina ne fa kuma aminina ba ni da wani amini sama da shi ba na jin daɗin yadda kike mishi.”

Shiru ta yi ta sunkuyar da kai “Zo ki buɗe meye ya kawo miki?

Shiru ta yi ta nufo ledar duk da ya fi ta kusanci da ita, ta ɗauka ta ciro ɗanɗasheshiyar sarƙa ce Dubai da ke ta sheƙin ɗauke ido bai ce komai ba ita ma haka sai juyawa ta yi zuwa ɗaki da nufin kai wa ta ajiye da gudun kar Abdurrashid ya kuma magana kan abin da ta yi.

Watan su tara cif da dawowa Jamila matar Usman ta haiho ɗanta namiji Hamida ta je barka ta je suna, duk da Jamila ta girme mata nesa ba kusa ba shiri sosai suke suna ziyartar juna daga lokaci zuwa lokaci, Hamida dai ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba.

Wasa wasa har ta kusa kammala digirinta wanda Exam biyu ya rage mata ta kammala haihuwa shiru.
Zuwa lokacin haihuwa take so kamar ta janyo, Abdurrashid ko da ba me yawan magana ba ne ta san yana so.

Addu’a dai take ta yi ko aikin hajji da umra da suka je addu’a ta farko da take fara yi Allah ya ba ta haihuwa ya ba ta ɗiya masu albarka.

Tana zaune wani weekend Abdurrashid da ya leƙa barrack ɗinsu, da yamma ya dawo ya ce ta shirya su je ganin Likita ta yi ta tunanin abin da zai kai su sai da suka je ta ji complain ɗinsa kan haihuwa ne, wani abokinsa Dr Nasir suka gani an yi gwaje-gwaje da bincike-bincike sun ta sintirin zuwa Asibitin amma ƙarshe sakamakon ya nuna ba komai ba su da wata matsala lokaci ne kawai bai yi ba.
Wannan ita ce rana ta farko da Hamida ta yi ta zubar da hawaye saboda rashin haihuwa,gane shi ma Abdurrashid ɗin yana so idan ya gaji daga jin lafiyarsa ƙalau zai iya yi mata kishiya.

Yin wannan tunanin ya sa ta ƙara rushewa da kuka, Abdurrashid da ke ta duban ta tun dawowar su tana koke-kokenta ya ga ba ta da niyyar dainawa kamo ta ya yi ya sa bisa gado sai ya ɗora mata nauyinsa, maganganu yake gaya mata na tawakkali da dangana,sai ya shiga share mata hawaye,sai da ta haƙura suka yi soyayyarsu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 23Shirin Allah 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.