Sun ɗauki ya yi minti ashirin kafin ya wuce, Anisa kuma ta yi part ɗinsu.
Sai sannan ta samu ta ɗaga ƙafarta da ta riƙa ji kamar ba za ta ɗauke ta ba, ɗakin barcinta ta koma "Namiji munafiki" abin da take faɗi kenan a ranta yayin da ta rintse idonta hoton Abdurrashid da Anisa na gilma mata, ƙirjinta ta dafe da wani baƙin ciki ya tokare.
Tana cikin da hawaye ta ji shigowar sa, ƙara rintse idonta ta yi "Yau nan za mu kwana kenan Madam? Ta ji muryarsa sai kuma ta ji ya fita.
Ba. . .