Tana tafe tana share hawaye har ta isa gidan Gwoggonta.
Ita kaɗai ta samu tana kallo, ta zauna sai ta rushe da kuka. Gwoggon da ke duban ta tun shigowar ta hankalinta ya yi matuƙar tashi ta fara tambayar ta abin da ya faru, cikin kuka ta zayyana mataauren da za a yi wa Abdurrashid don ba ta haihu ba, har rana an sa.
Hankalin Gwoggo ya ƙara ɗagawa sai haƙuri take ba Hamida ta ce "Na soma amso miki taimako na haihuwa sai ki kama min dariya ki ce ke ƙalau kike."
Haka Abdurrashid ya shigo. . .