Ba ta ko kai ga zama ba Gwoggo Indo ta mara mata baya. Gefen katifar suka zauna, Gwoggo ta shiga bude ledojin "Ya aka yi kika dawo daga fita?" Baki ta tabe "Ba fa shi ba ne, direbansa ya turo ya kawo mini tsarabar chaina, shi yana can karshen ta matarsa ta hana shi fitowa, kin san mijin ta ce ne. A haka kuma yake so ya aure ni mace na juya shi.
Gwoggo Indo tana mayar da kayan da ta ciro ta ce "Ai don dai kin ƙi ne, amma wallahi da sai kin aure shi, to mu ma. . .