Skip to content
Part 3 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Ba ta ko kai ga zama ba Gwoggo Indo ta mara mata baya. Gefen katifar suka zauna, Gwoggo ta shiga bude ledojin “Ya aka yi kika dawo daga fita?” Baki ta tabe “Ba fa shi ba ne, direbansa ya turo ya kawo mini tsarabar chaina, shi yana can karshen ta matarsa ta hana shi fitowa, kin san mijin ta ce ne. A haka kuma yake so ya aure ni mace na juya shi.

Gwoggo Indo tana mayar da kayan da ta ciro ta ce “Ai don dai kin ƙi ne, amma wallahi da sai kin aure shi, to mu ma zama za mu yi? Tashi za mu yi mu nema yadda ta nema. Kuma shi kin ga kullum ya zo maganar aure yake.”

Baki ta kuma tabewa “Kyale shi Gwoggo, gara mini Alh Uba.” ta ce “Na kyale shi, amma ya maganar sanya mini Easy? Na dawo na tarar da wuri yadda na bar shi.” ta ce “Ki yi hakuri Gwoggo, ya ce direba ne zai kawo mai sanyawar, kuma shi ne ya je dauko ku sai dai gobe.”

Ta ce “Yawwa don zafin garin nan ya zo sai ya kusa tafiya da mutum.”

Suna ta hirar su Hamida tun tana ji har barci ya yi awon gaba da ita.

Ta dai farka cikin dare ta gan ta lullube cikin lallausan bargo, Aina rike da wayarta tana charting, ta juya ta ci gaba da barcinta.

Asuba na yi lokacin da Innawuro ta saba tashinta ta farka. Ta mike ta yo alwala ta zo ta yi sallah har da karatun alkura’ni da ta saba. Ba ta tashi a wurin ba zama ta ci gaba da yi tana tuna Innawuro da mu’amalarsu, da kuma iyayenta da yan’uwanta.

Murda kofar da aka yi yasa ta daga kai Gwoggo Indo ce, soma gaishe ta ta yi ya yin da take kokarin zama, ta amsa cikin fara’a da tambayarta gajiyar tafiya.

Ganin yadda take amsawa yasa ta ce “Ki saki jikinki kin ji Hamida? Da ni da Ibrahim abu guda ne babu banbanci, ki dauke ni kamar shi, uwar mu daya uban mu daya, ciki guda muka kwanta.”

Hamida ta ce “To.” “Ko ba ki ga Aina harkokinta take ba ta da wata damuwa ba? Kai ta daga “To ke ma haka nake so ki rika yi.” kan ta kuma dagawa sai ta ce “Wane aiki zan miki Gwoggo? Kafin ta yi magana Aina ta yaye abin rufarta ta tashi zaune tana mika, kafin ta mike wata yar riga mai hannun best take sanye da ita, kanta ba dankwali ta shiga bathroom ba tare da ta yi magana ba.

Gwoggo Indo ta mike “Mu je ki gyara mini daki.”

Tare suka fita Hamida na biye da ita a baya. Dakin barcinta zuwa toilet ta gyara mata, ba ta ga mijinta ba Malam Buhari, da ta tambaya don ta gaishe shi Gwoggo ta ce yanzu ya fita wurin aiki. Daga inda take tana juyo hirar masu aikin Gwoggo, itan ma fita ta yi wurin su. Sai da ta gama gyara ko’ina tsaf! har falo, kitchen ne ba ta shiga ba don Aina tana aiki a ciki.

Tana gyara dakin Aina Ainar ta shigo dauke da trey ta ce “Zo ki zauna mu karya.” Da kanta ta hada mata tea me kauri ta turo mata chips da kwai, da ta kammala ci Aina ta fita, zuwa can ta dawo dauke da faranti da farfesun kaza ke ciki ta ajiye gaban Hamida nan ma cewa ta yi ta ci don idan suka fita ba samun zama ta ci abinci za ta yi ba.

Sanya naman kazar bakinta sai da kunnenta ya motsa don dadin da ta ji, sai ta gane gaskiyar Gwoggo Indo da ta kira waya lokacin suna hanya bayan sun kare wayar sai mita take Ita fa shi ya sa ko ganin gida za ta Daura take bari sai jama’a ta dawo lahadi ( don ba sa yin girki Asabar da lahadi) don ta fi so ta hada komai da kanta.

Kammalawarsu Aina ta zare cattle din da ta jona ta shiga wanka. Hamida ta kwashe kayan da suka bata ta yi kitchen, sai da ta wanke ta gyara kitchen din sai ta fito.

A falo ta tarad da Gwoggo da Aina zaune kowacce ta sha kwalliya, Gwoggo Indo atamfa ta daura dinkin riga da zane, sai ta dora after dress mai matukar kyau, tana rataye da jaka mahadin takalmin kafarta. Aina ma atamfar ce, sai dai ita riga ce da skirt ne matsattsu da Hamida ta lura ita yanayin shigar ta kenan. Sai takalmi da jaka, falon ya gauraye da kamshi. Gaba daya suka dube ta! Aina ta dubi dallelen agogon da ke daure a tsintsiyar hannunta sai ta ce “Ki je ki yi wanka Hamida, ke mu ke ta jira. Sai ta yi sauri ta shige ciki don ta shirya Gwoggo ta bi ta da kallo kafin ta maido idonta kan Aina “Sai kin samu zama sai ki samo mata kayanki a rarrage mata.

Da kai ta amsa sai ta ce “A ina za a ajiye ta? Dan shiru Gwoggon ta yi sai ta ce “Ina son ajiye ta a shago ta koyi saida kaya, ina son kuma ajiye ta wurin abinci ta rika bayarwa.” Aina ta ce “Ba da abincinta yana da matukar tasiri, a fara ajiye ta wurin sayar da abincin yanzu kafin nan gaba mu gani, ko Umar yana da amana zai kula miki da shagon provision din.” gyada kai ta yi cike da gamsuwa da shawarar.

Hamida ta fito cikin bakar jallabiya Gwoggo Indo ta bata ita tsaraba bara da ta je Umura. Ta dora bakin hijab, sosai ta yi kyau duk da ba wata kwalliya ta yi wa fuskarta ba.

Ganin fitowarta sai suka mike Aina ta rufe ko’ina.

A kasa suke takawa sun jera gwoggo da Aina kamar wasu kawaye, Hamida na biye da su a baya.

Aina ta ce “Amma ya kamata ki raba ta hijab din nan Gwoggo.”

Murmushi ta yi “Kar sanya hijab dinta ya dame ki Aina, ba abin da sanya hijabinta zai sa, ina ji a jikina dauko Hamida wani babban jari ne, don kyakkyawar mace kadara ce.

Sai suka yi dariya.

Har suka isa Hamida na kara kallon wuraren.

Kusa da get din fita wurin saida abincin yake shagon saida kayan masarufi na manne da shi. Masu aikin tuni suna wurin sun gyara komai, nar Hamida ta ga yarinyar jiya har suka yi hira take gayawa Hamida ita diyar daya daga cikin masu aikin Gwoggo ce sunanta Rabi.

Hamida ta soma bayar da abinci bisa jagorancin Rabi, sai kuma sannan ta ga nau’in abincin da ake sayarwa akwai farar shinkafa da miyar kaji, sai waina da miyar ganye wadda sai sun zo ake suyar ta.

Sai tuwon shinkafa miyar taushe ko kubewa danya.

Akwai farfesun kajj irin shi ne Aina ta debowa Hamida sai na kayan ciki.

Su Hamida sun ta zirga zirga daga wannan office zuwa wancan, ga shi akwai tazara mai yawa daga wurin nasu zuwa ainahin cikin company, ba nisan ya fi damun Hamida ba irin mayatar kallon mazan wurin ba ta saba ba. Da take ma Rabi korafi dariya ta yi mata ta ce su din wadansu irin mutane ne masu matukar son fararen mata.

Sai karfe biyu da rabi komai ya kare maaikatan ma suka tashi daga aiki. Hamida da Rabi suka fara wucewa dakin su Rabi suka fara yada zango sai da suka idar da sallah su Gwoggo suka dawo, sai ta bar Rabi ta nufi falon inda Gwoggo Indo da Aina suke zaune suna lissafin kudaden cinikin yau.

Sai mamakin tulin kudaden da ba ta taba ganin masu yawan su ba Hamida ke yi. Wayar Gwoggo Indo ta dau kara ta mika hannu ta dauko ta ta kanga a kunne “Alh Uba da kansa, ina gaisuwa ya kake ya harkokin? Ta dan tsaya ta saurara kafin ta ce “Kwarai ya ta ce, jiya na taho da ita, sai ta kuma saurarawa “Na ji to ya a ka yi? Ta kara saurarawa sai ta ce “Indai aure ne ka zo ka yi reno zan ba ka, amma ka bar wannan maganar.”

Sai ta kashe ta ta cilla ta saman kujera, suka hada ido da Aina sai suka saki murmushi “Aina ta ce “Da wuri haka Gwoggo? Wani kallo ta yi mata “Ba na fada miki ba, kin ga a hankali zan ja zarena zan dade ina tatsa don ko za a yi batun aurenta sai ta zama cikakkiyar budurwa, yadda duk wanda ya gan ta sai ya biyo.

Dariya suka yi Aina na cewa “Gaskiyarki Gwoggo.”

Cikin kwanaki bakwai Hamida ta sake da kowa a gidan. Tana shiga kuma a yi komai da ita, musamman girke girken saidawar da ake, hakan ba karamin dadi yake wa Gwoggo ba.

Ranar ta kama lahadi da safe misalin karfe goma zaune suke a falo. Gwoggo ta dubi Aina ” Wai ni kam Laila lafiya take? Aina ta ce “Me ya faru Gwoggo? Ta ce “Tun fa dawowata da ta kira ni ta yi min sannu da zuwa har yau ban kuma jin ta ba.”

Ba ta jira cewar Aina ba ta dubi Hamida “Kira mini Rabi.” ta mike zuwa dakin nasu, su duka kwance suke sun tattake bisa shimfida mutum biyu ke barci, ukun hirar su suke. Ta gaishe su sai ta fada wa Rabi sakon Gwoggonta. Suka jera har gaban Gwoggon sai da ta gama gaishe ta ta ce “Ku je ke da Hamida gidan Laila. Sai ta mayar da duban nata ga Hamida “Idan kun je ki ce na ce tun da na dawo ban gan ta ba, kuma ta ba ki kayan sawa.” maganarta ta karshe ta sa Hamida ta ji wani gingirin! wai ta ce ta bata kayan sanyawa? Je ki canza kaya ki zo ku tafi Gwoggo ta ce mata ganin yadda ta tsaya sororo a sanyaye ta juya zuwa daki ta canza kayan ciki irin wadanda Aina ta ba ta kala goma sha biyu kuma duk masu kyau da tsada.

Ta kara murza hoda ta sanya farin hijab, sai ta fito suka yi musu sallama suka fice.

A hankali suke takawa cikin Estate din suna hirar su har take ji wurin Rabi kanfanin nan da suke ciki na sarrafa fata ne. Har suka kai wasu rukunin gidajen ma’aikata, gidajen duk iri daya ne kamar na su Gwoggo Indo sai dai wadannan sun fi kyau nesa ba kusa ba, don mijin Gwoggo Indo karamin maaikaci ne.

Rabi ce ta yi knocking shiru ba a bude ba ta kara nan ma shiru sun ci gaba da tsayuwa ba alamar za a zo a bude har sun fara tunanin ko ba kowa suka ji takun tafiya, ganin wadda ta bude yasa Hamida washe hakora domin dai bahaushe ya ce kowa ya ga na gida ya bata ahu, sai dai kallon ba yabo ba fallasa da yar’uwarta ta ta yi mata yasa ta,gintse fara’arta ta. “Ku shigo.” ta fadi kamar tana rowar a ji muryarta.

Ita ma din kyakkyawa ce kamar sauran yan gidan su, matsakaicin tsawo gare ta tana da jiki jawur take kamar ka taba jini ya fito. Mahaifinta Gwoggo Indo ke bi mawa.

Suka bi bayanta har cikin falonta. sun zauna wata mata ta shigo bayan ta kwankwasa Rabi ta mike ta bude mata, goye take da yaro a bayanta Hamida ta mike ta karbi yaron yar’uwarta ta mai suna Amir. Lailar ta umarci matar ta kawo musu lemo. Sun dan jima zaune ganin ba alamar za ta kara magana Hamida kuma tunda ta fadi Gwoggo ta ce ba ta gan ta ba tun da ta dawo yasa Rabi fadin sakon Gwoggo na ta bai wa Hamida kaya. Shiru ta yi kamar ba ta ji ba Hamida ta mike ta ce za su wuce. Ta ce tana zuwa, ta dan jima ta fito dauke da jaka ta mikawa hamida har da kudi, godiya ta yi mata suka fito.

Washegari suna wurin saida abinci Hamida zaune ita da Rabi, daya daga cikin masu aikin ta leko ta ce Gwoggo ta ce Hamida ta kai abinci office din Alh Danlami. Gabanta ya buga ta wuce cikin mutuwar jiki. Take away aka bata mai dauke da farfesu na kayan ciki sai aka saka cikin wata leda.

Tafiya take amma hankalinta ba ya jikinta don kullun aka aike ta mutumin sai ya yi mata maganar banza.

Masinjansa ya fada masa isowarta ya ce ya ce ta shigo shi kuma ya aike shi, don da masinjan yake aike amma tunda ya ƙyalla idonsa kan Hamida ya daina aikensa sai dai ya yi waya ya ce a kawo masa.

Hannunta na rawa ta murɗa handle din kofar ta shiga da sallama, ya amsa yana ƙure ta da kallon da ke kara sanya jikinta daukar rawa wurin da ake ajiye masa ta nufa ta ajiye sai ta juyo gani ta yi mutum yana sanya wa kofa key ta dora hannunta aka ta fashe da kuka ya tare kofar “Me kuke fitowa nema ba kudi ba? Ki bani hadin kai ba abin da ba zan yi miki ba, dubi can ya nuna mata wani tebur da tulin kudi ke ajiye. “Kwaɗayina kawai zan maida ki kwashe su duka.” Sai ya soma nufo ta tana ja da baya har ta kai bango, ganin zai cimmata yasa ta daka tsalle ta yi wani wurin ya biyo ta, haka suka yi ta zagaye Office din har Allah ya gajiyar da shi sai share zufa yake da habar babbar riga.

Allah ya bata sa’a ta kai ƙofa wata sa’ar bai zare keyn ba ta murza kafin ta fice ya cimmata finciko doguwar rigar jikinta ya yi dan gyalen rigar ya fadi da ma takalmanta tuni ta watsar da su fasa kukan Hamida da cafko ta da ya yi sun yi daidai da turo kofar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 2Shirin Allah 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.