Da zuwan su ta sallami me nafef ɗin, a hankali ta shiga asibitin sai da ta karɓi babban katin ta samu wuri ta zauna inda sauran mutane ke zaune suna ganin likita.
Abdurrashid ya ɗan jima bai fito cikin motar ba yana duban gidan, ya dai gyara farking sai ya fito kai tsaye ya shiga gidan wanda yanzu kowa ya ja doguwar katanga ba wanda zai san ka shigo sai wanda ka shiga wurin sa.
Sasan Innawuro ya shiga da sallama wadda ke taya me aikinta girkin tarar tsohon mijinta, ta amsa tana fitowa daga kitchen mamaki ne ya. . .