Skip to content
Part 33 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Da zuwan su ta sallami me nafef ɗin, a hankali ta shiga asibitin sai da ta karɓi babban katin ta samu wuri ta zauna inda sauran mutane ke zaune suna ganin likita.

Abdurrashid ya ɗan jima bai fito cikin motar ba yana duban gidan, ya dai gyara farking sai ya fito kai tsaye ya shiga gidan wanda yanzu kowa ya ja doguwar katanga ba wanda zai san ka shigo sai wanda ka shiga wurin sa.

Sasan Innawuro ya shiga da sallama wadda ke taya me aikinta girkin tarar tsohon mijinta, ta amsa tana fitowa daga kitchen mamaki ne ya rufe ta ganin me sunan mijinta, duk da daman kullum addu’ar ta kenan Allah ya kawo mijin jikarta ta ta koma ɗakin ta.

Ta faɗaɗa fara’arta tana mishi sannu da zuwa ya zauna yana gaishe ta cikin girmamawa sun ɗan yi shiru ya ce Malam yau za su sauka Kano.”

Ta ce “Ma sha Allah, Allah ya kawo mana su lafiya.”

Ya ce “Amin zan je in gaishe da mutanen gidan.” Ta ce “Ai kam mazan duk sun fita.” Ya ce bari ya gaido Mama. Ta san maman Hamida yake nufi ta ce “To.”

Ko da ya je ya gaishe ta ya dawo suka ci gaba da zama ya ji Innawuro bata da niyyar kira masa Hamida sai ya tambaye ta ta ce “Da ciwon kai ta kwana, ta je Asibiti.” Da damuwa a fuskarsa ya ce “Ina ne asibitin? Ta ce “Bari dai in sa a raka ka.” Ta fita ta samo yaro ya miƙe suka fi ce.

Asibitin babu nisa da gidan, yana yin farking ya sallami yaran ya shiga ciki.
Wani mai saida kati ya tambaya ko ya ciro katin wata Hamida Ibrahim a yau? Ya ce “Bai ciro ba.” Ganin Abdurrashid babban mutum ne ya sa ya ce bari ya tambaya mishi, fita ya yi yana tambaya wata Nurse ya samu ta ce ya tambaya wurin masu ciki, ilai kuwa yana zuwa aka ce ta zo, ya duba ta wurin ganin likita, sai ya koma ya faɗa wa Abdurrashid hannu ya sa aljihu ya yi masa kyautar girma, ya shiga godiya ya bi Abdurrashid ɗin shi ya tambayi Hamida Ibrahim wasu mata biyu suka faɗi yanzu ta shiga wurin likita. Abdurrashid ya nemi ya nuna masa Office ɗin likitan.

Ya nuna mishi knocking ya yi daga ciki likitan ya amsa ya murɗa handle ɗin ya shiga, sun kalli juna da likitan ya ƙarasa ya bashi hannu suka yi musabaha Hamida wadda zaman ta kenan cikin dogon hijab ɗinta da safa jin ƙamshin turaren Abdurrashid ga kuma ƙarin mamakinta kamar muryarsa, ID Card ɗinsa Abdurrashid ya nuna masa wanda yasa likita ya ƙara shiga nutsuwarsa ya ce “Me ke damun Madam ɗi na? Likitan ya ce,

“Ciwon kai ne ranka ya daɗe ka san mata masu irin lalurarsu, can na ciwo nan na ciwo.”

Kan Abdurrashid ya ɗaure wace irin lalura ce da matata?”Kafin likita ya bada amsa ya kai wurin Hamida hannayenta ya lalubo cikin hijab ɗin ya ɗan rankwafo har suna jin nunfashin juna “Wa ce lalura ce da ke Hamida?” Ba ta yi magana ba hasali ma ko motsi ba ta yi ba “Wata biyu bana nan, ban san me yake faruwa da ita ba.” Abdurrashid ya fuskanci likita ba tare da ya ɗago ba likitan ganin kamar Abdurrashid ya manta yana wurin ya miƙe “Yallaɓai bari na dan tsahirta muku ina ganin tunda ka iso za kayi maganin ciwon kan.”.

Da haka ya bar kujerarsa ya fita ya ja musu ƙofa. Ajiyar zuciya Abdurrashid ya fidda gaba ɗaya ya cafko ta ya miƙar tsaye ya sa ta jikinsa sai ya ji cikinta da ya yi tauri ya cire hannun ya kama hannunta suka fito Office ɗin, sai da suka kai inda ya adana motarsa ya buɗe ya cusa ta ciki sai ya shiga glass ɗin tintek ne hakan ya ba shi damar ƙoƙarin cire mata hijab, duk da riƙewar da ta yi sai da ya yaye shi cikinta yake lalube taurin da ya kuma ji ya ce “Me ya same ki a ciki? Jikinsa har rawa yake don son jin amsar da za ta ba shi amma ta ƙi magana “To koma gaba mu tafi.” Nan ma banza ta mishi ya gaji ya koma gaban ya ja motar.

Ganin ya nufi GRA gidan Daddynsa inda yake sauka idan zai kwana garin ya sa ta ce “Ina za ka kai ni? Ya ce “GRA za mu in yi rarashin a can.” Ta ce “Wallahi ka kai ni gida ba zan je ba.” Ganin ba shi da niyyar canza hanya ya sa ta ce “Ko ka tsaya ko in buɗe ƙofa in fita, wallahi ba zan je ba.” Wawan burki ya ja ya mayar da motar gefen hanya.

“Ki yi haƙuri ranki ya daɗe.” Ya faɗi sai ya tashi motar zuwa gidan su Hamida yana tsaida motar ta riga shi fita ta shige ciki ba ta ga Innawuro ba ta shige ɗakinta kan kujerar mudubi ta zauna kawai ta rasa wane ma tunani za ta yi?

Ta samu ya yi minti talatin a zaune Innawuro ta turo ƙofa sai da ta tambaye kan wanda har ta manta da ciwon ta ce mata ana kiran ta a falo. Da ma ko hijab ɗin ba ta tuɓe ba ta miƙe cikin sanyin jiki sai ta isa falon bayan kujera ta ɗan raɓe ganin duk babanninta na wurin.

Sai da aka buɗe taro da addu’a sannan Baban Laila ya nemi Abdurrashid ya bayyana matsalar da ta haɗa shi da matarsa har ya turo ta gida ta zauna tsawon watanni biyu.”

Tiryan tiryan ya faɗi abin da ya sani da sakon da aka turo mishi da wanda Hamida ta ba shi labari.”
Baban Amina da duk cikin su shi ne mai zafi ya ce “To ka amince da abin da aka turo makan shi ya sa ka turo mana ita gida wata biyu?

Abdurrashid ya yi ɗan jugum kunya da nauyi suka kama shi ya yi ƙarfin halin amsawa da cewa “Ban turo Hamida gida don ina zargin ta ko na yarda da abin da aka turo min, na turo ta ne don in ja kunnenta na ji zafin abin da ta yi min ƙwarai na ɓoye min abin da yake faruwa, abokina Usman wanda yake aminina na tunkare shi a ranar da Hamida ta tafi ya kasa fuskanta ta ƙarshe sai gudawa ya yi yanzu haka iyalansa da iyayensa ba su san inda yake ba. Ya turo min text yana neman gafara ta tare da bayyana min komai, ya kuma ƙara wanke Hamida kan mace ce ta ƙwarai kuma Allah ya kare ta kan mummunan ƙudirunsu akan ta.

Falon suka ɗauka da faɗin Alhamdulillahi. Sai da suka tsahirta ya ce yana roƙon a ba shi Hamida su wuce yau.

Baban Amina ya ce Hamida za ta koma amma ba yau ba sai Malam ya dawo.

Dafe kai kawai Abdurrashid ya yi ya rasa yadda zai roƙe su su yi haƙuri su ba shi matarsa ita ya hukunta amma ya fita shiga damuwa na rashin ta kusa da shi bai ankara ba sai dai ya ji suna yi mishi sallama kowa ya fice Hamida ma da ke raɓe ta miƙe ta shige ciki Abdurrashid ya bi ta da kallo.

Sau biyu Hamida tana leƙowa sai ta gan shi zaune, kuma hakika yunwa take ji, ana ukun ne ta ga ya fita ta fito ba ta ga Innawuro ba a falon ta wuce kitchen ɗanwake take sha’awa da miya tana da garin ɗanwaken da Innawuro ta sa aka yi mata rogo ne da dawa da alkama da wake da gujjiya har kuka an sanya wurin niƙan. Akwai jiƙaƙƙen ruwan kanwa sai ta kwaɓa ta ajiye wuri ɗaya sai ta soma haɗa muryar akwai tantaƙwashi da ganyaye a fridge ta haɗa lafiyayyar miyar gyaɗa, sai da ta gama haɗin ta kunna ɗaya kan gas ɗin ta sanya ruwan ɗanwake da ta riga ta tafasa ruwan a kettle nan da nan ta fara saki tana gamawa ta koma kan miyarta tana cikin juyawa ta ji muryar Abdurrashid yana kiran sunan ta, ƙofar ta harara ta ci-gaba da abin da take.

An ɗan jima yana kiran ta kafin ta ji shigowar sa kitchen ɗin gyalen abayar jikinta ta yi saurin warwarewa ta rufe kanta zuwa kafaɗa sai kallon ta yake daga sama har ƙasa duk da ta ba shi baya “Hamida.” Ta kuma ji ya kira sunan ta, ko motsi ba ta yi ba har ya iso inda take sai ta ji ya rungume ta da sauri ta zabura “Meye haka kake yi ka manta nan ɗin ko’ina ne, za ka shigo har kitchen? Hancinsa yake gogawa a wuyanta “Ni ko na san ko’ina ne, Innawuro ta bar mana wurin ta san rabon miji da matarsa watanni biyu ta san akwai kewa.”

“To ka sake ni in sauke miyar.” Ta faɗi tana ɓata fuska ya sake ta ya matsa jikin bango ya harɗe hannayensa, ta harhaɗa komai ta ɗauki tren za ta fita suka haɗa ido ta yi saurin sunkuyar da kai a falon ta ajiye ta zauna ta soma zubawa shi ma ya fito gabanta ya zauna yana kallon ta ba zai ce bai taɓa ci ba don idan ya je Yola Daada na yi, amma shi kam ba cimarsa ba ce. “Ba tayi? Ya faɗi yana tsare ta da idanuwansa mamaki yake yadda ta koma mishi ta yi ƙiba komai na ta ya ƙara cika ga kyau da ta ƙara wadda kullum ya tuna ya tura matarsa ƙauye ya yi banza da ita fargaba ke rufe shi yadda za ta koma, Allah kuma bai ba shi ikon ya fahimci ciki ne a jikinta kuma wata dakakkiyar doguwar riga ce ta sanya kalarta ash sai aka yi mata kwalliya da baƙi ba ta kama ta ba don haka cikin da ya soma fitowa ya ɓace cikin rigar. “Ka zo ka ci mana.”

Muryarta ta dawo da shi daga tunanin da ya lula, ajiyar zuciya ya fidda ya ƙara gyara zama kusa da ita ta tsaya da ci ta zuba mishi duk da miyar ta yi mishi daɗi ka sa cin na kirki ya yi, ganin ta gama cin wanda ta zuba ta sha ruwa ya kamo ta suka hau kujera kan cinyarsa ya ɗora ta “Lallai ma yarinyar nan. Ya lakaci kumatunta “Har ma wasu kumatuna kika ajiye ba ki ma damu da ba mu tare ba.” Ya daki mazaunanta “Komai naki ya ƙaru kin ƙara kyau ya riƙe ta da kyau “Ki shirya anjima mu je GRA.”

Saurin zabura ta yi za ta ƙwace jikinta ya ƙara riƙe ta “Allah ba inda zan bi ka yau … Jin kamar za a buɗe ƙofa ya sa ya yi saurin sakin ta ta tashi da gudu ta shige ɗaki.

Abdurrashid dai ya ƙi tafiya yana zaune falon Innawuro wadda ita ma duk ta takura ya yi ta kiran wayar Hamida ta ƙi ɗauka ya tura text yana roƙon ta fito su tafi ta yi banza da shi dole hakanan ya yi sallama da Innawuro ya nufi GRA.

Washegari tun hantsi Malam ya iso gaba ɗaya gida ya ruɗe da murna ana ta sannu da zuwa sai da Hamida ta fita ta ga tare suke da Daddyn Abdurrashid gaishe su ta yi ta koma ɗaki.

Sai da suka kintsa sannan aka haɗu kan matsalar Hamida da Abdurrashid bayan mayar da magana kamar jiya Abdurrashid ya ƙara da cewa “Ni da ma Daddyna nake jira ya dawo zan yi ƙarar Brigadier kan keta hurumin iyalina da ya yi.” Ɗakin ya yi shiru kowa da abin da yake tunani haɗe da zullumin yadda mijin Aina da Hamida za su zauna kotu.

Malam ne ya yi gyaran murya ya ba Abdurrashid Haƙuri iya iyawar sa kan kar ya yi ƙarar mijin Aina, ya bar musu su za su zauna da shi, sun kuma shirya hakan da Engineer tun kafin su dawo. Sauran mazauna wurin ma haƙurin suka ba shi Baban Aina dai ya dafe kai. Abdurrashid ya ƙara bada haƙuri ya ce yana so ya wuce da Hamida, Malam ya ce “Ba laifi.” Kowa ya fice sai Malam aka bari da Engineer.

Kwanciya Hamida ta yi bayan ta koma ɗaki. Tana nan kwance Innawuro ta shigo kusa da ƙafafunta ta zauna “Sai ki yi ƙoƙari ki shirya mijinki ya ce zuwa La’asar za ku wuce.”

Tagumi ta rafsa hannu biyu “Haba dai Innawuro, sai ka ce wata kaza ya wulaƙanta ni ya koro ni tsawon wata biyu sai kawai daga zuwan shi a ce in bi shi?

“Haƙuri za ki yi tunda su Malam ba su ce a’a ba, kuma da ma addu’armu kenan ya zo ki koma ɗakinki in kin zauna nan ɗin me za ki yi?

Hamida ta saka kuka, Innawuro ta yi lallashin amma ta ƙi yin shiru ta fita ta ja mata ƙofar.

Har uku saura Hamida ta ƙi tashi ta shirya ga Abdurrashid sai sintiri yake mata a haka Aliyu ya shigo gidan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 32Shirin Allah 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.