Skip to content
Part 5 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Akwai yar tafiya daga nan zuwa Gate din, sai da Gwoggo Indo ta faɗi sunanta aka kira uwargidan wadda wurinta suka zo ta bada izinin a bar su su shigo.

Hamida sai kashe kwarkwatar ido take ganin aljannar duniyar da take gani a zahiri ba a fina- finan masu jajayen kunnuwa da ta saba gani ba.

Wani falo a ka yi musu masauki a ka ce su jira Haj, zaman aƙalla minti Ashirin suka yi kafin aka zo a ka tafi da su inda Hajiyar take kishingide take tana waya, sai da ta gama suka kwashi gaisuwa.

Gwaoggo Indo ta fiddo abin da ta zo mata da shi ta ɗora saman wani ɗan teburin glass da ke gaban Hajiyar, ta bi abin da aka ajiye mata da kallo “Ina fata sun yi kyan na wancan karon? Gwoggo ta karkace kai,

“Wane mutum in ji mutuwa, ai ba haɗi wannan na musamman ne, takanas daga nan har Chad aka kawo shi, turaren can kar ki yi wasa da shi sau daya kika yi amfani da shi kin gama da namiji.” Ɗan murmushin su na masu da shi ta yi “Ai na yarda da al’amarin ki Haj Indo, nawa ne kudin? Gwoggo Indo ta karkace kai ta soma lissafi “Shi wancan maƙale mata na matsi ne, kuɗinsa dubu d…. Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga mata hannu “Ki faɗi kudinki gaba ɗaya kawai.” Gwoggo ta kafto ta faɗi ta ce “Zan miki transfer za ki ji alert ƙila ma kafin ki isa gida.” Gwoggo Indo ta ɗan ranƙwafa “Ina godiya sosai Haj, Allah ya ƙara girma.” Sannan ta yi mata bayanin yadda za ta yi amfani da su.

Sun tashi tafiya ta buɗe jaka ta ciro kudi ta dubi Hamida “Karɓi yammata ki sha sweet.” Dan shiru Hamida ta yi tana so ta ce ta bar shi ko Gwoggon ta fahimci abin da take son yi ne ta dan zungure ta sai ta isa inda take ta karba tare da godiya.

Sun fito sun dauko hanya Gwoggo Indo ta ji shigowar sako wayarta hannunta har rawa yake ta ciro wayar ta mika wa Hamida ta duba gaya mata adadin kudaden da suka antayo cikin Acc dinta ya sa Gwoggo zaro ido “Kin gani ko Hamida? Ta ninka kudin da na fada mata, ai masu kudin nan in dubu biyar kake sayar da magani ce musu hamsin in ba haka ba sai su ce ba shi da kyau.

Ita dai Hamida ba ta ce komai ba sai kakkabi take a ranta yadda aka saida wa Laila da kuma zunzurutun kudin da aka sayar ma Hajiyar.

Da suka zo ƙofar gidan Laila, Gwoggo Indo wucewa ta yi ta ce Yamma ta yi, bayan Hamida ta ba ta kudin da a ka bata.

Da sauri Hamida ta shiga gidan don ta kusa taushe hannu wurin ɗaura girkin. Sannu ta yi wa masu gidan da ta samu zaune a falo, Laila ta nutse a kujera tana danna wayarta Mai gidan kuma na riƙe da laptop dinsa, Amir ya bar kayan wasansa ya zo ya ƙanƙame ta. Ta sure shi suka yi daki hijab ta cire ta kama mishi hannu su fito ya ce sai dai ta goya shi, goyon ta mishi suka fito za ta wuce kitchen ta ji muryar Mai gidan na cewa “Bar girkin nan, yau ki huta anjima ma fita mu sawo.” za ta koma daki ya ce “Zauna nan ki daina takura kanki da zaman ɗaki.” kasa ta zauna tana yi wa Amir wasa.

Washegari da zai fita ya ce wa Laila ta fada wa Hamida idan ta ƙare girki ta kawo masa Office za su shiga meeting ba zai dawo da wuri ba.

Don haka da wuri ta soma aikin ta gama ta shirya sai ta dauki kwandon da ta shirya kayan abincin Laila ta yi mata kwatancen Office din.

Gabanta ya faɗi ganin Office din kusa da na Alh Ɗanlami. Ta daure ta yi knocking daga ciki ya bada izinin a shigo ta shiga da sallama rubuce rubuce yake bai dago ba sai nuna mata da ya yi ta zauna da hannu, ta ɗosana ta zauna ya dauki yan mintoci kafin ya ɗago ya fuskance ta “Zuba min abincin.” abin da ya fara ce mata kenan. Ta mike zuwa inda suke cin abincin ta ajiye kwandon sai ta shiga zubawa aka murɗa ƙofar sai a ka shigo “Likita bokan turai ba dai ba ka je Office ba? Ahmad ya fadi yana mikewa tsaye “Haba dai ko kuma na dawo ba? Wanda ya shigo ya bada amsa Hamida ta baro inda take don ta gama zubawa idan su ya shiga na juna da wanda ya shigo sai ta ji wani iri don wanda ya cece ta ne daga hannun Alh Danlami yau ma Allah ya kuma haɗa su, shi kuma a ransa cewa ya yi “Ita din ce dai kenan? yau ma na kuma ganinta a Office din wani, wai ina iyayenta suke take famar gantali a ma’aikatan nan? Don ya taho ya ga wata kamar ita sai ya biyo bayanta a hankali har ya ga ta shiga Office din.

“Na tafi Baban Amir.” ta faɗi a hankali tana barin Office din kamar ana tunkuɗa ta.

Zauna mana.” Ahmad ya ce yana nuna masa wurin zama ba sai na zauna ba a kan hanya nake. Ya mika masa hannu suka yi musabaha ya juya Ahmad ya bi bayansa don yi mishi rakiya. Sai da suka isa inda ya adana motarsa ya shiga ya bar wurin yana tafe kansa na chargy me ya sa duk san da zai ga yarinyar nan sai tare da namiji? Wadanne irin iyaye gare ta da basu gudun ta lalace? Ya daki sitiyari! Mahaukacin horn din da yake dannawa ya sa masu kula da gate din ɗebowa a guje suka wangale gate din, a wuce a guje abin da ya basu mamaki suka bi motar da kallo, fitowa ya yi bai ko rufe motar da kyau ba ya yi ciki.

Wani ƙasaitaccen falo ya fada ba kowa ciki ya fada kan sopa ya dafe kansa yarinyar kawai ke masa yawo a ido. A ranar farko da ya soma ganinta ya gan ta ne a Office ana ƙokarin keta mutuncinta. Rana ta biyu ya ga ta bi bayan wani matashi, rana ta uku yau kenan ya gan ta Office din Ahmad da alama kuma ta saba da shi.

Hannu ya sa ya daki kujerar da yake tuna yadda yarinyar ta hana mishi sakat yarinya ƙarama da iyayenta suka sake ta cikin company nan da sunan talla, alhali cike take da bunsurai maza da ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin amfani da ƙarfin aljihu sun ɓata ta.

Idan ya zo nan a tunanin sai ya ce to meye nawa a ciki? Meye haɗina da ita? Tunda ya gan ta a Restaurant yake zagaya wurin ko zai ƙara ganin ta, to ko mai kama da ita bai sake gani ba, tuna ko tafiya ta yi ya sa ya daina ganin ta ya sa ya mike zumbur! Ya suri key dinsa bari ya koma Restaurant din ko zai gan ta. Sai idonsa ya shiga cikin na Auntynsa tana tsaye ta rungume hannuwa “Kansa ya shafa “Aunty. Duk da bai fi shekaru biyu ta ba shi ba yana girmamata yana mata kallon uwar da ba shi da kamarta tunda ya mallaki hankalinsa. “Tunanin me kake? Ta jeho mishi tambaya Ba komai Aunty.” “To ina kuma za ka? Ko abinci ba ka ci ba? “Mantuwa na yi yanzu zan dawo.” Ta bi shi da kallo har ya fice.

Da shiga motarsa Restaurant din ya nufa, har masu saida abincin suka tashi ba ta ba labarinta. To ko tambayar su zai yi? Idan kuma ya tambaya ya ce me ye sunanta? Cikin wani zafi da yake ji a ransa ya ja motar ya koma gida.

Ahmad bai shigo gidan ba sai Yamma lis. Tana gama abincin ta shirya musu kamar yadda ta saba sai ta koma daki.

Sai dai bayan Isha’i har ta kwanta ta fara lumshe ido Laila ta shigo ta ce Baban Amir ya ce ta fito. Ta fitan sai da ta kuma gaishe shi yana cewa “Ke ba ki gajiya da zaman daki ne? Zauna a yi hira da ke.” ta zauna a ɗarare, Amir ya yi barci ballantana ta samu abokin hira, tana zaune tana wasa da yan yatsunta ya ce me ya sa take zaune kawai ba ta karatu? An sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi ta ce “Gwoggo ta ce in saurare ta, za ta sanya ni.” ya ce “Shekarunki nawa? Ta ce “Sha hudu ya kaɗa kai “Me zai hana ki yi zamanki nan in sanya ki boko da Islamiya? Ta dan narke fuska duk da ta gaji da zaman gidan shiru ta ce “Ka tambayi Gwoggo.” “Zan tambaye ta, amma gobe zan kai ki Islamiya ta cikin Estate din nan, zuwa Monday sai in kai ki boko.” Hamida ta ce “Na gode.” Laila da ke sauraren su ko tari ba ta yi ba.

Kamar yadda ya ce washegarin ya kai ta ya yi mata Register suka ba shi unifoam da littattafai, suka dawo gida Hamida na ta murna. Da safe kafin ya fita ya ce mata yana fita zai bayar a sawo mata jaka da za ta rika sanya littattafan makarantar. Ta ce ta gode.

Sai ƙarfe uku aka kawo mata jakar tana yin sallar La’asar ta sanya unifoam sun ɗan yi mata yawa amma da yake hijab din wadatacce ne tana sanya shi shi kenan, ta yi wa Laila sallama ta fita gidan Amir na kuka sai ya bi ta.

Aji hudu suka sanya ta a bisa gwajin da suka yi mata, amma yan ajin sun kusa shiga aji biyar.
Ana tashi sauri ta yi ta koma gida saboda girki sai dai tana tura ƙofar falon Gwoggo ta gani zaune, jin suna gaisawa da Laila ta gane zuwanta kenan. Ta kalli Hamida baki buɗe “Ashe har makaranta suka sanya ki? Ba ku da niyyar bani ɗiyata ko Laila, to yau ƙafata ƙafarta za mu koma gida.” Laila ta ba ta hakuri ta ce ta bar mata Hamida cikin satin nan za a kawo mata mai aiki.

Ta ce sam ki yi aikin gidanki, zuwa sati daya dai ba mutuwa za ki yi ba.

Laila ta ce “Baban Amir ba ya nan Gwoggo, idan ya dawo ba zai ji dadi ba ya samu ta tafi ba sanin sa.
Ta buntsura baki “Sai fa ki yi Laila ta karuwa da ta ji mai wa’azi, ta ce ka yi kanka a ke ji, ni sinima za ni.”

Maza Hamida shiga ki tattaro abin da kika san naki ne ki zo mu je gida.”

Hamidar ta mike ta shiga ta hado ya na ta ya na ta ta fito. Gwoggo Indo ta gyara zaman mayafinta “Mu je, ke kuma Laila abin da kuka yi niyyar ba ta idan mijinki ya dawo ku kawo mata.”

Da haka suka bar gidan Hamida na rike da kayanta.

Suna isa da Aina suka fara karo da ke tsaye da wani tana zance.

Ta baro shi ta zo ta rungume Hamida suka shiga ciki, Hamida ta ce “Ko ki zo ki duba ni Aunty Aina.” ta ce “Yi hakuri yar ƙanwata, zuwan ne dai ban yi ba amma kina raina kamar kudin haya.”

Suka yi dariya “Kin yi kumatu kin ƙara haske gidan Laila da daɗi kenan? Wata dariyar suka ƙara.

Washegari ta kama Alhamis da safe bayan sun gama ayyukan da za su yi har an wuce da abincin, sai suka yi wanka jallabiya ta sa mai yankakken hannu, ta yi rolling da gyalen rigar kamar yadda Aina ta koyar da ita. Takalmi flat ta sanya. Su ukun suka tafi kamar yadda suka saba, ƙawarta Rabi an mayar da ita garin su.

Karfe daya da rabi lokacin wurin cin abincin ya ɗinke da jama’a, ana ta sallamar su wani matashi ya shigo, kallo daya Hamida ta yi masa ta kawar da kanta wanda ya cece ta ne, sai ta ga ilahirin mutanen wurin suna kawo masa gaisuwa, daidai da teburin da ya nufa don ya zauna wanda ke zaune wurin tashi ya yi da sauri yana kakkaɓe masa wurin.

Ta juya kawai don ci gaba da aikinta, wadda ke ba mutanen kusa da shi abinci ta matso “Yallabai me za a kawo? “Kira min waccan yarinyar.” ya fadi yana nuna mata Hamida, ta je ta isar da sakon.

Ko da Hamida ta zo nesa kadan da shi ta tsaya, duk da daɗin da ya ji na sake ganinta, gefe guda yana jin wani irin ba dadi da ya gan ta tana sayar da abinci, yarinya kamar wannan da ya kamata yanzu a ce tana makaranta. “Me za a kawo maka? Ta tambaye shi ganin ya bar ta tsaye bai amsa ba don wani sabon tunani da ya shige shi game da ita. Tsayuwa ta cigaba da yi har dai ta gane wannan mutumin ba shi da niyyar kula ta, ga jama’a na jira sai ta juya ta yi tafiyarta.

Ya dawo daga duniyar da ya lula ya ɗago iso sai ya ga wayam waige waige ya shiga yi sai dai har ya gaji da ware ido ba ta ba alamarta, tashi ya yi ya bar wurin cikin tunani.

Ranar Asabar babu aiki don haka ba sa yin abinci sai ga baƙuncin Alh Mustafa sun samu ya zo wurin Hamida. Fada Gwoggo Indo ta yi ta surfawa me Hamida za ta ci da wannan mutumin? Ban da kuma Malam da ya yi mata waya ya sanar mata zai zo ba, da ko ganin Hamida ba ta bari ya yi ba, kora shi za ta yi. Ba ta ko ce ya shigo ciki ba albarkacin tafiyar nesan da ya shawo ta ce Hamida ta fita ta same shi bayan an shanya shi na kusan awa daya.

Ta sanya hijab ta fita tana tura baki, shi kuma fara’a ya ɓalle da ita yana ganin Hamida wadda bai iya hana kansa yin ta matukar zai dora idonsa kan yarinyar.

A darare ta gaishe shi yana ta jan ta da labari.

Abdurrashid wanda ya fito daga gidansu zai fice daga Estate din, idonsa ya gano masa Hamida yarinyar da ya tambayi daya daga cikin masu sayar da abincin ta ce mishi sunanta Hamida, wani mamaki ya kama shi ganin ta tare da wani Wai su waye iyayen yarinyar nan? Ya ƙara tambayar kansa a karo na barkatai.

Ajiyar zuciya ya fidda ya tsaida motar ya jinginajikinsa a bayan kujerar yana cigaba da kallonsu, ransa na daɗa ɓaci.

Mintuna sun yi arba’in suka dauka mutumin ya shiga motarsa ita kuma ta shiga gida. Wani lokacin ya dauka yana shawarar ya yi tafiyarsa ko ma mai zai faru da rayuwarta ba matsalarsa ba ce, ko kuma mai cewa ya yi sallama yau dai ya ga su waye iyayenta? Jikinsa a mace ya yi wa motar key ya karasa kofar gidan Gwoggo indo sai da ya gyara parking sai ya fito.

<< Shirin Allah 4Shirin Allah 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.