Skip to content
Part 6 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Ya tsaya yana tunanin wanda zai samu ya kira masa ita, wurin shiru yake sai zirga -zirgan ababen hawa jefi-jefi. Bakin Gate din ya zura wa ido ya dauki kimanin minti biyar kafin aka buɗe kofar da ke jikin Gate din Malam Buhari ne ya fito sai ya yi saurin ƙarasa gabansa, gaisuwa ya fara mika wa Malam Buharin amma sai ya sunkuyar da kansa har da yar rusunawa yana gaida Abdurrashid wanda ya yi wa farin sanin ɗan Mai gidan su ne, tare da kakkaɓin abin da ya kawo shi ƙofar gidansa. “Hamida nake nema.” Abdurrashid ya ce kamar ya shiga zuciyarsa, ɗan jim ya yi sai ya ce “Ina zuwa, ranka ya daɗe.” ya juya zuwa ciki.

Gwoggo Indo ya samu tana haɗa miyar taushe, ya dube ta “Zo mana.” ta tashi sai ta bi bayansa suna shiga falo ya ce “Wani abin mamaki ya faru yanzu ina fita. ” “Uhm me ya faru? Ya ce “Yaron Mai gida na samu a kofar gidan nan ya ce wai yana neman Hamida. Gwoggo ta gwalo ido Hamida ko dai Aina Malam? Ya ce “To ni dai Hamida ya ce mini. Ta tafa hannu cikin matukar murna “Koma Malam ka ce tana zuwa.” bata saurari cewar sa ba ta yi dakin su Aina tare ta same su da Hamida, Aina na danna wayarta Hamida na haɗa kayanta za ta wanke “Tashi ki ji Aina, abin alheri ne ya tunkaro mu, ɗan mai Estate din nan ne ya zo har kofar gidan nan neman ki.” Zumbur kuwa ta tashi zaune “Ni kuma ya ce Gwoggo anya? Ta ce “Ke dan Allah ba mu da lokaci, irin wadannan ba a ja musu aji, tashi ki gani ko rana aka sanya miki tuni za a warware ta, dan gidan Engineer Shehu Bello ne fa. Aina da tuni ta kai gaban wardrobe ta soga ciro kaya Gwoggo na taya ta har suka kai ga matsaya kan wasu riga da skirt na wani yadi mai taushi tana ma fuskarta kwalliya Gwoggo Indo na mata wankan turare. Hamida da ta gama haɗa kayan wankin ta ɗiba ta yi waje.

Sai da suka tabbatar Aina ta yi sannan ta fita Gwoggo na bayanta wadda ke jin kamar su tafi tare gudun kar Aina ta kwafsa musu duk da sanin gogewar Aina me wuya a samu matsala. Dakin masu mata girki ta shige windon dakin su ta waje yake sai dai ba ta hango inda ya tsaya sosai, ta dage sai ɗage take tana miƙa wuya a fatan da take ta hango su da kyau.

Aina kuwa tana fita sallama ta yi masa ya dago idanuwansa da ke ƙasa cike da mamaki yake duban cikakkiyar budurwar da ke gabansa ta gaishe shi ya amsa cikin ƙosawa ta ce “Mu shiga daga ciki. Wani sanyi ya ji don zaton ko an turo ta ne ta yi masa jagora ya bi bayanta inda take tafe tana kaɗa jiki don ƙara sace zuciyarsa sun shiga tsakar gidan ba kowa sai Hamida da ke wanki daga ita sai zane da ta yi daurin ƙirji masu girkin suna can karshen gidan suna hira kallo daya ya yi ma Hamida sai ya kauda kai yana jin wani abu na yi masa yawo game da ita, har falon Gwoggo Indo ta zaunar da shi ta wuce ta kawo mishi ruwa, ganin ta koma ta zauna ya sa ya ce “Ina Hamidar ne? Wata faɗuwar gaba ta ji sai kuma ta ji duk ta daburce “E tana nan.” ta ba shi amsa “Yi mini magana da ita pls. ” ta mike tana jin ƙafarta kamar ba za ta ɗauke ta ba dakin Gwoggo Indo ta faɗa, kaɗan ya rage su gwabza karo don a ƙofar dakin take tana leƙe, hangowar da ta yi sun bar inda suke tsaye tunaninta ya ba ta shigo da shi za ta yi, shi ne ta yi saurin baro dakin masu aikin ta shigo nata.

Ya aka yi Aina? Ta fadi tana yarfa hannu “Wai Gwoggo wurin Hamida ya zo.” ta fadi cike da sanyin jiki “Hamida kuma? Gwoggo ta yi tambayar mamaki kwance kan fuskarta. “Wallahi ita ya ce.” “To ko lafiya? Don ba na ce son ta yake ba, amma dai bari in je in ji.” ta fara ƙoƙarin janyo mayafi ta fita ta bar Aina wadda ta fada gadon Gwoggo kwajab kamar tsohuwar jaka rub da ciki ta yi ta rufe idanuwanta.

Sallama Gwoggo Indo ta yi masa ya ɗago yana amsawa, tana zama ba ta jira gaisuwarsa ba ita ta soma gaishe shi “An ce kana neman Hamida lafiya? Ya ce “E wurinta na zo? Ta ce “To bari in turo ta. ” ta fita ta bar shi cikin wani takaicin da mamaki da sauri ta samu Hamida “Zo diyata.” Hamida ta ajiye rigar da take wankewa ta same ta. “Baƙon nan ke yake nema, ki kula da kyau in kin je gaban shi, ɗan me Estate din nan ne.” ta ƙwalawa wata yar yarinya diyar daya daga cikin masu mata aiki ta ce ta je cikin kayan Hamida ta samo mata Abaya da gyalenta ta kwatanta mata inda kayan Hamidar suke. Ta amsa ta wuce cikin sauri, dakin masu aikin ta ja Hamida, sai da yaranyar ta kawo ta sanya “To yi maza ki je.” Ta ba ta umarni Hamida na fita Gwoggo Indo ta shiga zance Allah ya wadaran rashin sani in na sani ba gyara ta zan yi ba, ko da su Malam suka turo mutumin nan nake cewa auren Hamida ba yanzu ba idan yaron nan ya ce yanzun yake so a aura mishi ita ai da gudu za a yi hakan, ƙanƙanta? Mu da aka yi mana muna da sha biyu me ya same mu? Ji take kamar tana mafarki wai tilon ɗan Shehu Bello ne cikin gidanta ya biyo cikin yayanta, ita kam da wace irin sa’a ta zo duniya? Farin ciki ke ɗawainiya da ita.

Hamida dai a sanyaye ta isa falon ta yi sallama a hankali wadda da ƙyar ya jiyo ta kafin ta nemi daya daga cikin kujerun ta zauna.

Kanta na kasa ta ce mishi ina wuni.

Zaman minti goma suka yi shiru ya mike “Ni zan tafi.” ta ce Sai anjima. Ya ce “Ki bani nombarki.” kai ta girgiza “Ba ni da waya.” “To ki amso mini ta mamanku.”

Ta miƙe ta je ta samu Gwoggo Indo, jiki na ɓari a ka rubuto ta kai mishi, ya sa kai ya bar falon sai dai kafin ya idasa ficewa ya ji muryar Gwoggo na cewa “Har ka fito? Ya ce “E” ta ce “Sai kja a yi hakuri da ita karamar yarinya ce.” ya ce “Ba komai.

Ranar Monday daga wurin aiki wurin saida abincin su Hamida ya wuce. Ya kuma samu nasarar keɓewa da ita a cikin motarsa, bai fito ba wayar Gwoggo ya kira ta turo ta. Glass din motar tintek ne don ba ya son jama’a su fahimci shi ne. Tambayar ta ya yi me ya sa ba ta zuwa makaranta? Ta ce Gwoggonta ta ce za ta sanya ta ya ce da ma ba mamanta ba ce? Ta daga mishi kai tare da cewa yayar babanta ce ya ce ina mamanta, ba ta ko numfasa ba ta ce Tana garin su Daura. Ya ja ajiyar zuciya Babanki fa? Ta ce shi ma yana Daura nan Gwoggonta ce ta dauko ta. Ya jinjina kai “Me ya sa ba ki son karatu sai saida abinci? Saurin duban sa ta yi a karo na farko idanuwansu suka shiga na juna, ta janye nata da sauri. “Ina so.” “Kina son me? “Ina son karatun.” “Yanzu idan na samu Gwoggonki na ce zan sanya ki Makaranta ki bar saida abincin nan za ki yarda? Cikin sauri ta ce “E. “To zan zo gida za mu yi magana da ita.” Anan ya ga cikakkar fara’ar Hamida.

Ya sallame ta ta fita ya ja motar sai ya bar wurin cikin tunani.

A hankali ya ƙarasa a maimakon part dinsa na Auntynsa ya wuce, zaune take ta bi shi da kallo “Yau ma ina ka tsaya? Ta tambaye shi sai da ya zauna kusa da ita ya ce “Na ɗan biya wani wuri ne.” ta kada kai ba dan ta gamsu ba. Hira suka shiga yi har aka kawo masa abinci ya ci anan sai ya wuce wurinsa, sai da ya gabatar da duk abin da zai yi kafin ya haye gadonsa don ya yi barci amma tunanin rayuwar Hamida ya hana mishi sakat. Zumbur! Ya mike ya shiga sanya kaya kananan kaya ya sanya da suka yi matukar hawansa, ko da fuskarsa ba walwala bai hana shi yin kyau ba. Ya fito sai da ya biya wurin Aunty Karima kallon mamaki ta yi masa “Sai ina kuma daga shigowa? “Wani abokina zan gani anan gadon ƙaya.” ta gyada kai.

Ya fice motarsa ya fada ya ja zuwa gidan Gwoggo Indo da wayarsa ya kuma amfani ya shaida mata ya zo. An yi sa’a dawowarsu kenan maimakon ta tura Hamida yarinyar mai girkinta ta aika ta ce ya shigo.

Ita kuma ta fada dakin su Aina, dukkan su kwance suke bisa katifa Aina charting take, Hamida na kallon silif tana tunanin Innawuro da iyayenta da kannenta har ma da yan gidan su.

“Hamida ga Yallabai nan ya zo.” A tare suka ɗago suka dube ta Hamida ta ce “Waye Yallabai? Aina da ta ri ga ta gane inda zancen ya dosa ba ta tsinka ba “Yallabai mana da ya zo wurin ki shekaranjiya. Ganin Hamida ba ta da niyyar tashi ya sa ta zauna bakin katifar ta dora kanta a cinyarta “Na ga kamar ba ki murna da wannan babban kamu da kika yi? Jin Hamidar ba ta tanka ba ta ƙara da cewa “Kin ga duk girman wurin nan na mahaifinsa ne, duk kuma tarin al’ummar da kika gani cikin Estate din nan karkashin mahaifinsa suke, shi din kuma shi ne da daya tilo da mahaifinsa ya haifa.

Ina gidan da muka je da ke kina gidan Laila? Hamida ta ce “Na tuna shi.” “To shi ne gidan mahaifinsa, ga shi kyakkyawan saurayi ga arziki Hamida, ina gani ban taba rike wadda ta yi sa’a irin wadda kika yi ba.” Hamida ta ce “Ya ce zai tambaye ki ya sanya ni makaranta.” Gwoggo Indo ta yi cikakkar fara’a Yawwa to kin gani? Maza ki shirya ga Aina nan ta taya ki, ni zan je in tare shi, na sanya yar gidan magajiya.

ta shigo da shi.” Ta miƙe sai ta ja musu ƙofar.

Ganin Hamida ba ta motsa ba ya sa Aina ta kamo hannunta “Hamida.” ta kira sunanta, ɗago fararan idanuwanta ta yi ta dube ta, “Maganganun duk da Gwoggo ta faɗa miki gaskiya ne, kin yi dace da samun miji na nunawa sa’a, kin zo Kano da hannun dama. Ki ba shi fuska kar ki dinga zuwa ki yi masa dunkum kin ji Hamidata.” yarinyar ta ɗaga mata kai.

Aina ta mike ta ɗauko hoda ta ba ta ta murza ta fesa mata turare, don sanye take da riga doguwa ta atamfa hijab dinta iya gwiwa ta sanya, da Aina ta nemi hana ta narke mata ta yi kamar za ta yi kuka ta ce ta je haka, sai ta fita ta bi ta da kallo tana jin wani yanayi na ina ma ita ta dace wannan ɗanɗasheshen saurayin ya ce yana so, ko da kuɗi suke abin so wannan santalelen ma ko ba shi da tarin dukiya mace za ta so a ce shi ɗin mijinta ne. Ba da wanda take kwatanta shi sai da jarumin fina-finan India hitric roshan ko da ba su kama a fuska shi din ma dogo ne mai dogon hanci, tsawo da ƙirar jikinsu ce iri daya.

Gwoggo Indo tana fitowa sallama ta yi masa yau ma kuma ita ta fara gaishe shi bayan ta nemi matsuguni.

Sun ɗan yi jim ya ce “Me ya sa Hamida ba ta zuwa makaranta?

Ta ɗan karyar da kai “Ina son sanya ta, sai dai sha’anin rayuwar ne sai a hankali, akwai wasu kudade da nake sa rai su nake so idan suka zo sai in sanya ta.” ta ƙare jawabin cikin kwantar da murya. Kai ya girgiza “Haka ne, akwai makarantar da na yi zan kai ta can, amma ba na so ta ƙara zuwa wurin sai da abincin nan.”

“Shi kenan, ba za ta sake ba. Ganin ya mike ya sa ta ce “Za ka tafi ba ka ga Hamidar ba? “No ƙyale ta kawai, da ma maganar makarantar na zo yi miki. Ya sa kai sai ya bar falon daidai nan kuma Hamidar ta fito Gwoggo ta dube ta “Bi shi Hamida ki yi masa rakiya.” ta gyaɗa kai sai ta bi shi a baya
Yana ƙoƙarin buɗe mota ya ji a jikinsa akwai mutum a bayansa sai ya waiwaya Hamida ya gani tana kakkare fuskarta da hijab din jikinta.

Kallonta ya yi na wasu sakanni sai ya ce “Ki koma gida.” Ya faɗa motarsa sai ya bar wurin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 5Shirin Allah 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.