Cigaban labari
Isah ya zabura ya miƙe a gigice ganin shigowar Turaki, Kamal da kuma ‘yansanda su Sergent. Mamakin ganin su bai bar shi ya iya amsa sallamar da suke dokawa ba.
Suka tsaya a falon cirko-cirko suna wa juna kallon-kallo, dukkan su sararin fuskokinsu nuni suke da bayyanannen mamakin da zuciyoyinsu suke ciki.
Budurwar ta taka a hankali cikin fara’a ta isa ga su Turaki tana faɗin, “Marhabin da zuwan ku… bismillah ku ƙarasa ku zauna mu yi karin gaba ɗaya don na san ku ma ba ku samu sukunin karyawa ba. . .