Ishola ta zaro hoto ɗaya ta juyo musu fuskar ta ce, “Wannan shi ne Dr. Hadi Daura, sunanshi ba ɓoyayye ba ne a faɗin jami’ar a dalilin kasancewar shi fitinannen mutum mai masifar son ‘yan mata. An kai jallin da duk yarinyar da aka gan su tare ana yi mata kallon ba mutuniyar arziƙi ba.
Cikin haka ne wata rana Habiba sun fito daga ɗakin karatu, gwaji (test) ce suka yi don haka a jigace ta fito ta nufi wani sashe da yake da yalwatattun bishiyu masu kaɗa sassanyar iska. Ba ta jima da zama kan. . .