Kyakkyawar mace zankaɗeɗiya mai cikar zati, wacce kwatancen kyawunta zai fi ga misalin kyawawan ‘ya’yan fararen aljanu. Fuskarta cike da annuri, takunta gwanin birgewa ta ƙaraso gabansu ta tsaya tana wadata idanuwansu da sassanyan murmushi.
Za a iya karantar mamaki, fargaba da kuma al’ajabi a fuskar kowannen su, yayin da suka shiga kallon-kallo a tsakanin su cike da shakku.Muryarta tamkar busar sarewa, Hausarta da rauni sosai ta ce.
“Kar ku bari mamaki ya sarayar muku da kuzari, kar ku ji tsoro idan kuka san wace ce ni…”
Tsoron nasu kuwa ya yi tasiri, domin. . .
Allah ya ƙara basira