Skip to content
Part 16 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Kyakkyawar mace zankaɗeɗiya mai cikar zati, wacce kwatancen kyawunta zai fi ga misalin kyawawan ‘ya’yan fararen aljanu. Fuskarta cike da annuri, takunta gwanin birgewa ta ƙaraso gabansu ta tsaya tana wadata idanuwansu da sassanyan murmushi.

Za a iya karantar mamaki, fargaba da kuma al’ajabi a fuskar kowannen su, yayin da suka shiga kallon-kallo a tsakanin su cike da shakku.
Muryarta tamkar busar sarewa, Hausarta da rauni sosai ta ce.

“Kar ku bari mamaki ya sarayar muku da kuzari, kar ku ji tsoro idan kuka san wace ce ni…”

Tsoron nasu kuwa ya yi tasiri, domin ja da baya suka fara yi cikin zazzare idanu, su kansu su Seargent kasancewar su jami’ai bai saka zuciyoyinsu sun yi dakewar da za su iya jure wannan tsoro ba.

“…Na sani tuni kun gama yanke wa ranku hukunci a kaina… tabbas ni ba Bil-Adam ba ce! Kamar yadda na yi hasashen abin da ke cikin ranku kenan… ku zauna mu ƙarƙare komai…”

Duk sun kasa cika umarninta, yadda suke a tsaye cirko-cirko Isah ya buɗe baki ya ce cikin rawar harshe.

“Me.. Mee… me kike so ki faɗa mana kuma yanzu?”

“Asalin sunana Isholatul Askar… ɗiyace ni ga sarkin fararen aljanu na yankin daularmu ta fafaren jinnu, ba mu kasance Muslmai ba amma akwai adalci sosai a tsakanin masauratarmu da kuma mabiyanmu.

Na faɗa tarkon Kabasa ne a dalilin ƙin bin umarnin mahaifina da na yi, inda na saci jiki da dare na bar nahiyarmu na taho nahiyar baƙaƙen fata, na sauka a kan wani kogon dutse, na dinga shawagina cike da farin ciki ina zagaye a duniyar bakaken fata jinsin Adamu ina ganin yadda suke gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da jin daɗi.

Idan na so na kan ɗauki siffar Adamu in shiga cikin mutane in ta yawatawa, in shiga kasuwa, in shiga makarantu, jami’o’i, bankuna… har gidan gwamnatoci na shisshiga, na yi cuɗanya da ‘ya’yan Adamu mabambanta.

Kwatsam! Wata rana na gama shawagina ina tafe kan hanyata ta komawa masaukina, kasancewar a cikin siffar farar tsuntsuwa nake, na ratso daji ina tafiya sai na hango kamar mutane a can ƙasa, don haka na yi ƙasa na sauka can gefe. Ashe wasu mata ne suke tafe a mota cikin wannan ƙasurgumin daji motar ta lalace, haka kawai sai na ji ina son sanin inda waɗannan mata za su je, don haka na matsa can gefensu ina sauraron hirarsu.

Ɗaya ta ce.

“Hajiya anya ba hakura za mu yi mu ƙarasa da ƙafa ba?”

Hajiyar ta yamutsa fuska, ga dukkan alamu cikin matuƙar damuwa take, akwai alamun gajiyawa a fuskarta ta ce.

“Yaya kike ganin nisan tafiyar kafin mu isa? Na fi tunanin kawai zafi motar nan ta ɗauka… ga dukkan alamu kuma babu ruwa a kusa a wannan baƙin dajin.”

“Gaskiya Hajiya akwai sauran tafiya, sai dai babu yadda zamu yi, gwara mu tafi ɗin kin ga dare na neman ya riske mu…”

Hajiyar ta ƙara ɓata fuska, ta soma waige-waige a sararin dajin.

“Shi ko wannan wane irin taƙadarin matsafi ne da ya rasa inda zai yi muhalli sai bangon duniya…!”
Cike da dariya waccan matar ta ce, “Bangon duniya fa Hajiya! Ai Hajiya ina faɗa miki in dai kina neman taƙadarin matsafi, majanuni, tantiri gawurtacce wanda hatta Aljanu suna shakkar taƙadirancinsa don yadda yake sarrafa su son ransa in kika samu Kabasa sai a shafa fatiha… shi ya sa aikinshi ba ya taɓa lalacewa, in dai an je masa da buƙata kowace iri ce to wallahi take-yanke zai gama miki komai… Kuma kin san me Hajiya?”

Ta gyaɗa kai.

“Abin da yake burge ni da aikinshi, ba ya buƙatar ya ce ki kawo wani abu, duk abin da dodanniyar tsafinsa ta buƙata ko na jini ko na ruhin mutum, to aljanunsa masu yi masa hidima yake sakawa su je su kawo masa… Hajiya shahararshi fa ta sa ko kuɗin mutane ba sa gabanshi don a kan idonki zai iya haɗa miki maƙudan miliyoyin kuɗi… hmm mu je dai hajiya idonki ya gane miki.”

Duk da jin harshen Hausa bai wadata gare ni sosai ba, amma na ji tattaunawar tasu na kuma fahimta sosai. Sai na yi tsaii da raina ina rarrabe tsakanin abin da ya kamace ni, tabbas na ji ina son na bi waɗannan mata don in ga wannan hatsabibin Adamu da aka ce yana sarrafa aljannu yadda ransa ya so… na sani tabbas mu jinnu cikinmu akwai hatsabibai taƙadirai, musamman baƙaƙen fata, amma a haka a ce har akwai wani taƙadarin Adamu da hatsabibancinsa ya fi na jinnu! Zan so in gan shi kuwa da gaske!

Gama yanke wannan shawara ke da wuya na tashi firr na luluƙa cikin dajin, tafiya na yi mai ɗan nisa na isa ga wata ƙorama na ɗebo ruwa cikin wani fasasshen ɓawon ɗan itaciya da ban san sunanta ba na koma na iske matan nan suna nan suna cigaba da shawarwari.

Na busa iska wacce ta zama guguwa ta turniƙe wajen da duhu, cikin haka na je na zuba wa motar ruwa ba tare da sun fahimta ba. Bayan iskar ta lafa suka koma cikin motar da sauri Hajiya na faɗin “Bari in sake jarrabawa in gani ko motar nan za ta tashi.”

Tana kunna motar ta tashi, ta figa a guje ina maƙale a bayan motar.

An yi tafiya mai nisa sosai har aka zo ainahin masaukina, na yi mamaki ƙwarai da yakasance ashe ma a kusa da inda na sauka shi wannan mutum yake. Kodayake ba abin mamaki ba ne kasancewar gurin cike yake da ɓaraguzan manyan duwatsu masu ɗauke da kogo baƙaƙe masu matuƙar baƙin duhu.

Babban ma abin da ya fi zama na mamaki shi ne yadda aka yi har mutane suka san da wanzuwar wannan taliki a cikin wannan ɓoyayyen daji har suke zuwa gurinsa ba sa ko jin tsoron ratso wannan baƙin daji.

Za ku sha matuƙar mamaki idan kuka ga yadda wannan fada ta Ujosa take cike da kayan tsatsuba na tashin hankali, abin da zai ƙara muku mamaki shi ne yadda waɗannan Hajiyoyi suka zo da buƙatar a hallaka mijin Hajiyar don ta samu kuɗin gado, nan take aka biya mata buƙatar, a kan idanunta aka kira kurwar mijin aka kashe ta…
Wannan hatsabibanci shi ya saka ni fidda ɗan karamin sauti wanda ya ja hankalin Kabasa ya ƙura min ido, tantirin ashe ya fahimci ni ɗin ba tsuntsuwar gaske ba ce, ban san me ya yi ba kawai sai ji na yi ya watso min wani abu kamar ruwa, ashe ruwan tsafi ne ya watso min wanda ya zame min baƙar azaba kuma ya tilasta min rikiɗewa zuwa siffar Adamu, wato wannan siffa da kuke ganina da ita a yanzu.

Ina daga kwance ina numfarfashin wahala na lura da yadda matan nan suka tsorata da wannan lamari, suka dinga ja da baya suna zazzare idanu.
Kabasa ya bushe da dariya ya ce. “Wannan da kuke gani aljana ce, tun ɗazu take biye da ku ba ku sani ba… leƙen asiri ta zo, sai dai ta tafka babban kuskure mafi girma a rayuwarta don ta riga ta faɗo Duniyar Ujosa… za ta zama ɗaya daga cikin hadimai masu yi wa Uwargijiya hidima…”

Daga nan ya yi tsafinsa ya mayar da ni tsuntsuwa, ni ce tsuntsuwar nan da na faɗa muku Maryam ta gani, kuma daga lokacin na fara hidima ga duniyar tsafi.

Ina daga cikin waɗanda ke shiga jikin Adamu suna sarrafa tunaninsu wajen sauya musu dukkan abin da aka so a juya su. Ban taɓa yin tasrifi a jikin Adamu ba sai a sanadin wannan matsafi.

Ni aka saka na dinga tasrifi da jikin Maryam a duk lokacin aka so ta aikata wani abu, kodayaushe ina tare da ita, shi ya sa na iya ba ku labarin duk abin da ya faru da ita….

Lalacewar alaƙata da Kabasa ta samo asali ne lokacin da ya buƙaci ya aure ni, ni kuma na kafe kan ba zan aure shi ba, ba zan iya aurar Adamu ba kuma ma tsohon mutum ƙazami irin Kabasa, na fi so ya ‘yantar da ni in koma gurin iyayena. Nan ya dinga gana min azaba, ya ɗauke ni ya kai ni can wani tsibiri ya ɗaure ni, ya sa baƙaƙen aljanu suka dinga azabtar da ni, da na ji azaba ta yi yawa dole na haƙura na amince muka yi auren don ba yadda zan yi.

Bayan auren namu ne kuma wani sabon aiki ya taso, saboda a lokacin tuni an kashe Maryam.
Wata budurwa ce Kabasa ya samo, ya kuma tilasta sai na shiga jikinta na sauya mata tunani, sai dai shiga ta jikin budurwar shi ya zamo min silar waraka, don kuwa gawurtaccen Malami ne danginta suka kira ya zo da ƙarfin addu’a da ƙwarewar aiki ya cire ni daga jikinta ya kuma kama ni ya tafi da ni.

Ya so ya azabtar da ni amma sai na nuna masa nadamata, na kuma ba shi labarina tare da neman taimakonsa kan ya kuɓutar da ni.

Daga nan Malamin ya musuluntar da ni, ya kuma yi alkawarin taimakawa mu kawar da kabasa.
Sai dai me?

Kabasa ya yi amfani da lokacin da Malamin nan yake cikin janaba ya sa aka ɗauko masa shi ya kai shi duniyar tsafi ya daskarar da shi ya mayar da shi gunki… har yanzu kuwa yana nan a matsayin daskararren gunki.

Tsoron kar Kabasa ya cutar da ni ya sa na gudu nahiyarmu, sai dai sun ƙi karɓa ta duk da cewa na je na tarar sun karɓi addinin musulunci daga wata runduna ta tawagar musulman jinnu.

An kafa mini sharaɗin muddin ina so mahaifina ya yafe min sai na je na kawar da Kabasa daga doron duniya…

Abin ya zame min duka biyu, na rasa yadda zan yi, saboda hatsabibancin Kabasa ya fi ƙarfi na.
Da ƙyar na samu taimakon wani maridin aljani, mun fara aiki sai kuma muka gagara, maridin nan ya ba ni shawara sai na haɗa aiki tare da Bil-Adam sannan za mu iya kawo ƙarshen Kabasa, wannan dalilin ne ya sa na yi tunanin biyowa ta hanyar ku a matsayinku na dangin Maryam, na san za ku yi duk iyawarku don ku ɗauki fansar ran ‘yar uwarku tare da cewa kuskure iri ɗaya muka tafka ni da Maryam na bijirewa umarnin mahaifi, shi ya sa na yi tunanin bin wannan hanyar za ta zame mana silar gyara kura-kuranmu duk da ita Maryam ta rigada ta mutu, amma na tabbata duk wanda ya ji wannan labari zai tausaya mata, masu ƙullaci a kanta za su yafe mata…”

Babu wanda cikin su Isah jikinsa bai yi la’asar ba, dukkan su ganin lamarin suke kamar a mafarki kamar kuma labarin almara, wai dama hakan za ta iya faruwa? Ga su ga aljana har tana ba su labari…

Ishola ta zauna tana goge hawayen idanunta, ta cigaba da cewa.

“Dukkan wani abu da kuka ga ya faru na ruɗani to tabbas shirina ne, na shirya komai ne don in jawo hankalinku ku san cewa akwai wani ƙullalen abu cikin mutuwar Maryam… Ni ce na ƙirƙiri facebook account da sunan Adetunji Gobboni, na ɗora hotunan Maryam da na wani Bayerabe (Abdul-Latip Adebayo) da zummar za a yi bikinsu a Lagos, na saka lokacin ya zo daidai da na wani biki da za a yi duk don ku tashi hankalinku a kan lamarin, na yi amfani da ɓangarenka Isah saboda na san matsanancin son da kake yi wa Maryam tabbas za ka tashi hankalinka wajen nemo ta musamman yadda tun mutuwarta kake cikin shakkun mutuwar… Duk wani kira da ka gani an yi maka shi, da waɗannan mutane da ka haɗu da su a kan hanya duk ‘yan uwanane.

Ni tare da taimakon ‘yan uwan nawa muka yi tasrifi a jikinku muka hana ku ganin ƙabarin Maryam tare da cewa ƙabarin na nan a inda yake, ko a yanzu idan kuka koma Kano ku je ku duba za ku ga ƙabarin nata yana nan. Maryam ta mutu mutuwa irin wacce dukkan mai rai zai ɗanɗane ta, a halin yanzu babu abin da take buƙata daga gare ku face addu’ar neman yafiyar Ubangiji… sa’annan ku taimaki ruhinta mu je mu yaƙi Kabasa mu kawar da shi daga doron duniya ko don mu ceci tarin mutanen da ke halaka dalilinsa… Kabasa ya kashe rayuka babu adadi, ya haukatar, ya makantar, ya gurguntar da mutane masu ɗimbin yawa, ya jaza talauci mummuna ga wasu, ya kawo arziƙi na banza na tsafi ga wasu, saboda haka ku taho mu yi jihadi mu ga bayanshi…”

Koda Ishola ta zo nan sai ta yi shiru tana cigaba da goge hawaye.

Dukkansu jikinsu tsuma yake, ba ma kamar Isah wanda shi ji yake kamar a lokacin komai ke faruwa, mikin son Maryam ya sake zama ɗanye a ransa.

*****

Sun koma Kano ɗauke da wannan gagarumin labari wanda musamman aka yi zama da duk wani dangi na kusa da kuma ‘yan Sanda tare da wasu shahararrun Malaman addini aka saurari recording wanda Seargent ya naɗa.

Malaman suka tabbatar da cewa lallai hakan zai iya faruwa duk da cewa an sani aljanu suna da masifar ƙarya musamman a kan wata manufa da suke son cimma, don haka sai da suka kira aljana Ishola ta bayyana cikin hayaƙi, kowa ya ganta da idanunsa, ta ƙara yi musu bayanin komai da bakinta, hakan ya sa Malaman suka gamsu suka kuma amince za ta jagorance su su je har can duniyar Ujosa su yi amfani da ƙarfin addu’a da Alqur’ani don kawar da Kabasa.

A ranar su Isah suka sake zuwa makabarta, abin al’ajabi suka tarar da ƙabarin Maryam na nan a yadda yake.

Malam Hashimu mai gadin maƙabartar hankalinsa ya kwanta da ya kuɓuta daga zargi, sai dai ya ayyana hakan a matsayin ishara ce gare shi ta aikin ha’inci da yake yi wajen kula da maƙabarta, don haka ya tuba ga Allah da ƙudirin zai kyautata aikinsa a gaba.

Duk wani bincike da ake yi da zarge-zarge aka rufe tun da an gano inda lamari ya samo asali, Likita da nurses ɗin suma da ake zarginsu yanzu an wanke su, komai ya wuce.

Bayan kwana biyu aka yi gagarumin shirin tafiya duniyar Ujosa, manyan motoci biyar aka cika da dangi da kuma Malamai tare da almajiransu, sa’annan da tarin jami’an tsaro. Ishola ta yi jagorancin tafiya ta hanyar ɗaukar siffar Ɗan Adam.

Sun yi tafiya mai mugun nisa ta kwana biyu da wuni sannan suka isa dajin.

Wani abu na al’ajabi da ya faru shi ne ganin tarin ‘yanmata kyawawa farere tas da su, su n1a zazzaune a bakin kogon dutsen, kowacce babu riga a jikinta sai ɗaurin ƙirji na wani jan yadin saƙi. Idanunsu a runtse yake yayinda hannunsu kuma ke riƙe da ƙoƙon duma suna bugawa suna karanta waƙoƙin tsafi.

Wannan lamari shi ya sa suka kasa ganin hanyar shiga kogon dutsen har ita kanta aljana Ishola.
Malamai suka fara karatu da addu’o’i, suna yi su ma matan nan suna ƙara ƙarfin sautin waƙar tsafinsu, abin sai ya zam tamkar faɗa a tsakaninsu. Malamai na addu’a su kuma suna waƙoƙin tsafi.

Malaman suka tsanata karatun nasu har suka fara cin galaba a kan ‘yan matan nan, jikinsu ya fara rawa tare da rinewa yana yin baƙi, sai dai duk da haka ba su daina kiɗa da waƙar ba.

Su Isah na can gefe suna kallon ikon Allah, abin kamar a shirin wasan kwaikwayo.

Tabbas tasirin addu’a ya fi ƙarfin duk wani tsini da kaifi balle tasirin tsafi. Tasirin ƙarfin addu’ar Malaman ta rinjayi tsafin ‘yan matan nan sai ga jikinsu ya soma narkewa yana zagwanyewa, kafin wani lokaci suka ƙone ƙurmus babu su babu ƙoƙunan dumansu.

Faruwar hakan ke da wuya sai ga ƙofa ta bayyana a jikin kogon dutsen, nan Malaman suka sa kai suna masu cigaba da karanto addu’o’i jami’ai na biye da su cikin shirin ko-ta-kwana.

Isah ya yunƙura da niyyar ya bi su ciki sai mahaifinsa ya yi zaraf ya riƙe shi.

“Ina za ka je Isah? Me za ka shiga ka yi?”
“Baba da ka bar ni na shiga in ga wannan hatsabibin mutumi!”

“To saurin me kake? Ko ka manta kama shi za a yi a tafi da shi tun da ga jami’an tsaro? Ka kwantar da hankalinka, kowa zai gan shi da idanunsa.”

A cikin kogon dutsen nan Malamai ba su fasa addu’a ba, yayin da dukkan wasu kayan tsafi suka dinga ƙonewa, shi kanshi Kabasa ya so yin gaddama don kuwa sai da ya dinga ɗirko tsaface-tsafacensa har ya yi nasarar daskarar da wani almajiri ya mayar da shi gunki.

Malaman nan suka cigaba da addu’a suna watsa wa Kabasa, Allah ya ba su nasara suka lalata duk wani surkullensa, ita kanta Uwargijiyar tasu sai da aka ƙona aljanin da ke tasrifi da gangar jikinta, sai ga gawar tata a yashe a ƙas duk ta ruɓe ta zama ruɓaɓɓen ƙwarangwal.

Gama lalata tsafin nashi ke da wuya ‘yan sanda suka kama shi suka yi waje da shi, almajirin nan kuwa da aka mayar gunki suka watsa masa ruwan addu’a sai ga shi ya yi ajiyar zuciya ya faɗi ƙasa rikicaa yana numfashin wahala.

Aljana Ishola ta tunasar da su batun malamin da Kabasa ya daskarar shi ma aka je aka tashe shi, sai dai shi inaaa babu rai sai dai gawarsa.

Faruwar hakan ke da wuya kogon ya fara rawa tare da rugujewa, manya-manyan duwatsu suka dinga rikitowa suna zubowa, da ƙyar suka kuɓuta daga cikin kogon nan.

Suna gama fitowa kuwa gaba ɗaya duwatsum suka nitse a ƙas gurin ya zama ta fili fetal, tamkar wani abu bai taɓa wanzuwa a wajen ba.

*****

Duniya ta ɗauka da labarin Kabasa da irin hatsabibanci da yake aikatawa, aka yi holonsa tare da miƙa shi kotu inda aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Dukkan mutanen da suke mu’amalar tsafi da shi hankulansu suka tashi da ganin wannan al’amari, nan wasu suka tuba suka yi nadama yayin da wasu kuma sai abin da ya cigaba.

A yanzu komai ya warware, mutane sun gane abin da ya samu Maryam har ya yi sanadin ranta, Abbansu ya yafe mata ya ƙara yafe mata, ya je kabarinta yana kuka yana nema mata gafarar Ubangiji.

Mamansu Isah kuwa jikinta ya yi sanyi ƙalau, ƙiyayyar da take yi wa Maryam sai ta rikiɗe ta koma kewar ruhinta.

A ɓangaren Ishola ma ta koma nahiyarsu, sun karɓe ta sun kuma yafe mata ita ma, labarinta sai ya zama izina ga waɗanda ke tunanin saɓa wa iyayensu a kan burikansu na duniya.

Isah ya riƙe matarshi Jalila da hannun biyu, tun da ta tabbata babu Maryam a yanzu ba shi da wacce tafi masa Jalilarshi don haka ya riƙe da kyau da kuƙawarsa da soyayya da komai!

Ma sha Allah!

ƙarshen wannan labari kenan na SIDDABARU, Allah ya sa an amfana, Allah ya ba mu ikon bin iyayenmu sau-da-ƙafa, waɗanda nasu suka rasu Allah ya jaddada rahamarSa gare su.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 15

1 thought on “Siddabaru 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.