"Da gaske kai kake wannan furucin Alhaji? Na yi mamaki matuƙa! Ko a labaran almara ban taɓa jin inda aka yi haka ba kuma a kalli hakan a matsayin abin da zai faru a gaske, sam!"Cewar Mama cikin bayyana takaicinta.
Umma Fatima abokiyar zaman Mama ce ta tsinka cikin maganar Maman.
"Gaskiya abin dai akwai ɗaure kai da kulle zuciya matuƙa, wannan ya wuce a kira shi da tsananin kama, domin duk wanda ya san Maryam idan ya kalli waɗannan hotunan ko a ransa ba zai kawo cewa mai kama da ita ba ce, kai. . .