Kamar daga sama sai ga su Alhaji Tukur (babansu Isah) sun bayyana a cikin maƙabartar, har da Alhaji Ahmad mahaifin marigayiya Maryam da kuma su Turaki da Munkaila duk yayyun Maryam.
Gaba ɗayansu suka yi cirko-cirko a tsaye a gaban ƙaburburan da ke gurin cikin matuƙar ɗimuwa da tu'ajjibi.
Da gaske ne fa babu ƙabarin Maryam babu alamarsa, kuma tabbas babu tantama ko shakkar lallai a nan ne aka haƙa rami aka binne ta, a yanzu kuma babu, don haka lamarin yanzu ya shallake hankalin kowa, dole kuma a yi wai-wai-da-baya a. . .
Muna godiya