Lokacin da suka isa Jihar Lagos dare ya fara shiga, don haka suna yin masauki a hotel ɗin da suka kama kowa ya ɗaura alwala suka rama sallolin da suka hau kansu a cikin ɗaki.
Isah ya daɗe a zaune yana addu'a a kan neman dacewa cikin uzurin da ya kawo su.Jami'an 'yansanda biyu da suka taho da su suka fice don neman division ɗin da za su ba su taimako.Don haka ɗakin ya rage mutane uku kacal, Isah, Kamal da kuma Turaki.
Kamal a matuƙar gajiye yake don a rayuwarshi bai taɓa. . .
Yabana 4