Skip to content
Part 4 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Lokacin da suka isa Jihar Lagos dare ya fara shiga, don haka suna yin masauki a hotel ɗin da suka kama kowa ya ɗaura alwala suka rama sallolin da suka hau kansu a cikin ɗaki.

Isah ya daɗe a zaune yana addu’a a kan neman dacewa cikin uzurin da ya kawo su.
Jami’an ‘yansanda biyu da suka taho da su suka fice don neman division ɗin da za su ba su taimako.
Don haka ɗakin ya rage mutane uku kacal, Isah, Kamal da kuma Turaki.

Kamal a matuƙar gajiye yake don a rayuwarshi bai taɓa yin doguwar tafiya makamanciyar wannan ba, don haka lafiyar gado ya bi ya mimmiƙe.

Turaki waya ya zaro ya kunna Data ya shiga facebook, kai tsaye akwatun bincike (search box) ya tafi ya rubuta sunan mutumin da ya ɗora hotunan gayyatar shagalin bikin Maryam kasancewar Isah ya faɗa masa sunan mutumin tun a jiya, ya nemo shi kuma ya tura masa katin gayyatar zama abokai shi ma, don haka niyyarsa a yanzu ita ce ya duba ya gani ko ya karɓe shi.

Ya rubuta sunan kamar yadda ya yi a jiya ADETUNJI GOBBONI, sai dai me?
Masarrafar na’urar facebook ta sanar da shi sam babu mai irin wannan sunan a cikin kundin adana bayananta.

Da sauri ya ɗaga kai zuwa ga Isah da ya rufe fuskarsa da tafukansa, tabbacin addu’ar da yake yi tun daga ƙarƙashin zuciyarsa yake yi.

“Khalifa (sunan da ake kiran Isah da shi kenan a dangi) don Allah katse addu’ar nan ka sake maimaita min sunan gayen nan.”

Ba tare da Isah kai inda ya ke so ya kai ba ya shafa ya kuma ya miƙe da sauri, “Sunan wane gaye?”

“Adetunji.”

“Adetunji Gobboni.”

“Haka na rubuta amma sun ce babu mai irin wannan sunan a facebook.”

“Wataƙila ka kuskure wani abu cikin rubuta sunan, amma ni tun jiya ya yi accepting request ɗina, har saƙo na tura masa… Bari in duba.”

Ya zaro wayarsa daga jikin caji ya kunna Data a gurguje ya antaya shafin sada zumunta mai sunan fuskar littafi (facebook).

A yadda Turaki ya ga yanayin fuskar Isah na sauyawa da kaɗan da kaɗan take sai gabanshi ya faɗi, idan ya lura da kyau ma kamar tsattsafin gumi ne ke tashi a fuskar.

Kusan kamar mintuna biyu Isah na tsaye da waya yana lalube cikin iska, Turaki ya baza masa idanu cikin kullewar tunani don haka sai ɗakin ya yi tsit, don shi Kamal tuni ya kai kai uku a duniyarsa ta baccin gajiya.

Jaɓar! Isah ya faɗi ƙasa yana ambaton “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Me ya ke shirin faruwa ne?”

Sai aka yi saɓatta-juyatta, shi Turakin sai ga shi zumubur ya miƙe yana kai hannu zai karɓe wayar hannun Isah.

“Ya aka yi ne Khalifa? Kai ma haka suka ce maka ko?”

“Turaki lamarin nan ya fara shallake yadda nake lissafa shi… Ka duba ka ga yadda kwata-kwata babu bayanan Adetunji, har saƙwannin da na tura masa a jiya duk sun ce ba a yi haka ba, ko dai mafarki nake yi dama?”

“Ba mafarki ba ne Khalifa, wannan kuma kar ya zama abin da zai takure mana lissafinmu, tashi ma ya kamata mu yi mu fara gudanar da abin da ya kawo mu tunda kwanaki biyu kawai muke da su rakkin… Kai Kamal.!”

Ya juya ga Kamal, “Kalli shashasha sakarai bacci ma yake!” Ya kai masa dukan da sai da ya farka a gigice yana salati.

Ya saki uwar hamma tare da miƙa, “A ina aka tsaye ne Yaya?”

“A gidan ƙaniyarka.” Turaki ya ce a ƙufule.

Isah na nan zaune ya kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi balle a saka masa ran tashi su fara shiri, cikin damuwa Turaki ya sake duban shi, “Khalifa ka tashi mana, ya kamata mu yi komai a kan lokaci, na tabbata yanzu an fara gudanar da taron nan don haka gwara mu je mu san inda mu ka sa gaba.”

Daidai lokacin aka ƙwaƙwasa ƙofar, Turaki ya isa bakin ƙofar ya buɗe, ‘yansandan ne suke dawo, wannan karon su huɗu ne, wato sun sami ƙarin mutum biyu, ɗaya Bayerabe ɗaya Bahaushe.
Suka gaisa, Bayerben ɗansandan ya buƙaci su ƙara yi masa bayanin abin da ke wakana, a gurguje kuma a taƙaice Turaki ya faɗi iyakar abin da zai iya faɗa, a ƙarshe ya buƙaci Isah da ya ƙara haske kan yadda lamarin ya fara a shekaranjiya na yadda ya ci karo da hotunan a facebook, ganin zai ɓata lokaci da rashin kuzarin yin magana ɗansandan ya ce kawai su tafi gurin da aka ce za a yi bikin a can kasancewar wajen sananne kuma fitacce, wato Queen Lina Events.

Cikin ƙwarewa suka fara gudanar da aikin kasancewar ba su da tikitin shiga gurin, sai ‘yansandan suka fara isa ga jami’an tsaron gurin suka gabatar musu da ƙudirinsu da kuma neman haɗin kansu da cewar za su farauci wasu masu laifi ne da aka tabbatar za su baƙunci shagalin, da farko sun so fuskantar tasgaro, don kuwa securities ɗin ƙin amincewa suka yi da kafa hujjar hakan zai iya rusa ƙima da darajar wajen a idanun duniya, amma dayake akwai ƙabilarsu cikin ‘yansandan, wato Bayerbe sai suka hakura bayan an tabbatar musu da cikin ƙwarewa za su gudanar da aiki ba tare da hankulan mutanen sun kawo kansu ba, duk da haka sai da aka yi magana da shugaban gurin ya ce babu damuwa ai dolen su ne su ba wa hukuma dama ta gudanar da bincikenta a ko’ina ne ma.

Securities su suka yi musu jagorancin shiga katafaren gurin wanda tun daga harabar wajen aka liƙa tafekekiyar taswira mai ɗauke da hoton amarya da ango. Maryam dai ga ta nan sak a jikin hoton.

Isah, Turaki da Kamal, a yadda zuciyoyinsu suka buga da karfi kai ka ce fashewa za su yi, jikin Isah ya ɗauki kyarma, ya dinga jin kanshi na bugawa dum! dum! jijiyoyin jikinshi tamkar za su tsittsinke. Alla-alla ya ke su isa ciki ya yi arba da Maryam!

A yadda kiɗan ke tashi har ginin gurin ansawa yake, kunnuwansu kuwa tamkar za su ɓurme, waƙa ce irin wacce Yarbawa ke cashewa da ita a yayin shagulgulansu, wannan ke tabbatar da cewa tuni shagali ya yi nisa, yayinda jama’a ga su nan birjik suna kai kawo, sai gwarancin yarurrukansu ke ta shi, Yarbanci da pidgin English, idan ma akwai Hausa to gaskiya kunnuwansu ba su jiyo musu ba.

Tamkar dai wasu manyan baƙi haka aka kai su waje na musamman aka ajiye su, babu wanda zai kawo zargi a kansu don ko su ‘yansandan shigar kayan gida ne a jikkunansu na ƙananun kaya.

Rarraba idanu kawai Isah ke yi yana son gano ta ina zai ga Maryam ɗin?
Gurin da aka tanadarwa ango da amarya wayam yake sai tarin kayayyin ci da sha da sauran kayan ƙawa a wajen.

A tsakiyar filin gurin kuwa mata da maza ne ke cashewa cikin salon rawarsu ta Yarbawa.

Turaki ya yi tsai da ransa cikin yin nazarin gurin da dukkan nutsuwarsa, abin da yake son ganowa shi ne ina Hausawa suke wakilan Maryam a taron? Ko kuwa dai bayan guduwa da ta yi daga duniyarsu kuma ta canza yare daga Hausa zuwa Yarbanci? To amma me ya sa ba ta canza sunanta na Hausa ba ta mayar da na Yarbawa…?

Muryar mai gabatar da taron (M.C) ya jiyo cikin turancin kudu yana faɗin a shirya ga ango da amrya nan fitowa, wakar da take tashi ma aka sauya ta zuwa wata daddaɗar waƙa ta harshen Turanci mai tsuma zuciya.

Tabbas zuciyoyinsu sun kusa tsinkewa da gaske, kamar haɗin baki kuma suka miƙe dukkan su a tare.

Cikin sauri ɗansanda ɗaya ya dakatar da su tare da shawartar su kan su nutsu su bi komai a sannu.

Idan dai har abin da idanuwansu suke gane musu da gaske ne to tabbas rayuwarsu na cikin garari.

Wadataccen haske da yake gurin ya isa tabbatar musu da lallai ba gizo idanunsu ke yi ba wata ce daban wannan ba Maryam ba!

Kokaɗan ma wannan ba ta yi kalar Hausawa ba, sa’annan ita ɗin jika-jika ce, hakan ya yi matuƙar jefa musu shakku a zuciya, sai dai bayyanannen abin da zai kore shakkun shi ne kasantuwar angon lallai shi ne a jikin hoton, abin da ya ƙara tabbatar da haka shi ne yadda M.C ɗin ya ambaci sunansa kamar yadda yake a rubuce a katin gayyata wato Abdul-Lateep Adebayo…

Abu ɗaya ne yanzu ya rage su ji shi ne yadda za a ambaci sunan amarya, shin sunan Maryam ne za su ji an faɗa ko ko za su ji an ce Ada, Amaka, ko Oluwa ko ko dai can wani suna nasu?

‘Maryam Ahmad Isah!’

Haka M.C ya faɗi sunan amarya da bagwariyar Hausarsa, cikakken sunan Maryam ɗinsu amma kuma ba ita ba ce wannan.

“Turaki! Kuna ji da ganin abin da nake gani ko kuwa zautuwa na fara yi?” A ruɗe Isah ya jefawa Turaki tambayar.

“Akwa wani ɓoyayyen al’amari da har yanzu lissafinmu bai kai kanshi ba, kai tsaye ma ba hanyar tunkarar lamarin nan muka dosa ba Khalifa mun bar Jaki ne muna dukan Taiki… Tabbas wannan ba Maryam ɗinmu ba ce, amma kuma da gaske Maryam ba ta cikin ƙabarinta, faruwar wannan lamari tamkar wani madubi ne aka haska mana na nuni da cewa mutuwar Maryam akwai laujen da ya kamata mu cire shi daga cikin naɗi… Ku tashi mu tafi kawai…” Ya ƙare tare da miƙewa.

Da sauri ɗansandan ya dakatar da shi, “Hold on my man, lamarin nan bai buƙatar gaggawa ciki, mu ba haka aikinmu yake ba, don zuciyarka ta saƙa maka wani tunani ba shi ke nufin za mu karɓe shi da hannu bibiyu ba, don kun ga wannan ba a Maryam ɗinku ba ba shi ke nufin mu haƙura mu tafi ba, aiki yanzu muka fara gudanar da bincike ma.”

Ya zura hannu a aljihu ya lalubo wayarsu ta ‘yansanda ya kira Sufeta Usman ya sanar da shi abin da suka tarar.

Shi ma ba ƙaramin kaɗuwa ya yi ba da jin wannan batu, kuma da yake an samu nasarar gano inda sister Asabe ke aiki har an far mata da bincike, ita ma rashin samun gamsassun bayanai daga gare ta ya ƙara dagula lamarin.

“Yanzu me kuka tsara ne Sergent?”

“E shi Turaki so ya yi su tafi kawai, amma na ankarar da shi hakan ba ita ce hanyar ɓullewa ba, yanzu haka muna son fara gudanar da sabon binciken yadda aka samu sauyin fuskar Maryam.”

“Welldone! Ka yi tunani mai kyau sergent, ku yi gaggawar bincika abin da kuka samo sai ka gaggauta sanar da ni.”

“An gama Sir.” Ya ƙame ya sara masa tamkar yana gabanshi.

Isah ya miƙe yana jin hajijiya na kwasar shi, da ƙyar ya iya dafa Kamal da shi ma ya miƙe, ɗaya hannun kuma ya dafe goshinshi da yake jin kamar zai faɗo.

“Yallaɓi kaina ciwo yake, ba zan iya cigaba da zama a nan ba, zan koma masauki in kwanta.”

“Babu damuwa kuna iya tafiya, mu za mu cigaba da bincikar lamarin yanzu.”

Kamal ya riƙe shi har gurin da suka faka motocinsu, suka shiga su ka fice daga gurin.

Isah ya baje a kan tafkeken gadon da yake cikin ɗakin, ya laluba da ƙyar ya ɗauko wayarsa wacce ya sanya ta a shiru (silent) ya tarar da kiran matarsa Jalila har sau bakwai, ya ji wani iri a ranshi na rashin daɗin yadda cikin kwanaki biyu jal ya juyawa matarshi baya kan wacce babu tabbacin kasantuwar ta a doron duniya.

Bai san lokacin da malalacin murmushi ya suɓuce masa ba, har zai tafi kiran ta sai ga kira ya shigo da ɓoyayyiyar lamba (privet number). Abin da ya zo ranshi take shi ne, Jalila ce ta ɓoye numberta ta kira shi da tunin in ta yi haka zai fi saurin ɗaga kiran, ya sake sakin guntun murmushi ya ɗaga kiran.

“Assalamu alaikum Ya Khalifa!”

Kamar a mafarki, kamar a farke, muryar Maryam a waya.
Ya yi ɗif kamar wanda ruwa ya cinye yayin da abubuwa da yawa ke zuwar masa cikin zuciya daga ƙwaƙwalwa.

“Hello ko ba Ya Khalifa ba ne? Ni ce Maryam!”

Da sauri ya zare wayar daga kunnesa ya saka ɗan yatsansa ɗaya a baki ya gatsa, tsananin zafin da ya ratsa ƙwaƙwalwarsa ya tabbatar masa da lallai a farke ya ke ba bacci ba.

Tuni ya nemi ciwon kanshi ya rasa, ya kuma tashi daga kwanciyar da ya yi, ya saka wayar a handsfree, muryarta raɗau ta sake magana.

“Yaya Khalifa a duniyar labarai na soyayya cikin jinsin mutane da aljanu, ban taɓa cin karo da labarin masoyi irin ka ba… Ina ma ina ma…” Ta tuntsire da dariya

“Kuna tantamar ina raye ko ina mace, a idanunka ni rayayyiya ce, amma a zahirin al’amari ni matacciya ce…. Na san za ka yi mamaki idan na ce yau na gan ku a wajen dinner ɗin bikin babbar ƙawata Stella wacce na sadaukar mata da sunana saboda tsantsar soyayyar da na ke mata…”
Ta sake rushewa da dariya, Turaki da sautin maganar ya farkar da shi daga baccin da ya fara yi ya girgije yana sauraron abin da ke fita a cikin wayar.

“… Na gan ku a gurin dinner kai da Ya Turaki, Ya Kamalu da kuma wasu da ban san su ba…. Na san kana son sanin abubuwa da yawa game da nu… Kunnuwanka na muradin jin batutuwa daga bakina… To ka sani ba za ka ji komai daga bakina ba… Saƙo ɗaya zan ba ka shi ne ka gaishe min da matakar Jalila da kyau.”

Ɗif kiran ya katse!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 3Siddabaru 5 >>

1 thought on “Siddabaru 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.