Skip to content
Part 5 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Sakon Godiya

Ina mai miƙa saƙon godiya tare da jinjina ta musamman gare ku masu ƙauna da bibiyar labarin nan, ina jin daɗi matuƙa da yadda ake nuna ƙauna ga wannan littafi.

Ina roƙon ku taya ni da addu’a yadda na fara yin rubutun Allah ya sai mun ga ayar ƙarshe da rai da lafiya

Kimanin ƙarfe biyu da kusan mintuna ashirin na dare Isah na tsaye a bakin tagar ɗakin yana hangen sararin harabar hotel ɗin da yadda tsilli-tsillin mutane ke shigowa wasu kuma na fita.

Duk yadda bacci ya kai ga gwanintar satar idanun mutum sai ga shi idanun Isah sun zama sa-gudu maganin ƙi-gudu gare shi.

Tun bayan kiran sa da Maryam ta yi da ɓoyayyiyar lamba ta faɗa musu wasu maganganu masu rikita lissafi sai ƙwaƙwalwar tashi ta ƙara dagulewa, komai ya ƙwace masa, dabara ko ta ƙulla ruwa a leda ta kasa zuwar masa.

Su Turaki kuwa tuni bacci ya wafce su ya tafi da su duniyarsa, duk da cewa shi ma Turakin yana cikin lissafin raba ɗaya-biyu baccin ya wawure shi, Kamal ko ba a ta tashi, ya ƙulla aminta sosai da bacci don haka zangon da ya yi a baccin ba wanda za a cim masa a kusa ba ne.

‘YanSandan ma tuni sun dawo sun kwanta, Isah dai shi kaɗai ke ta kokowa da zuciyarsa kan yadda zai warware wa kanshi wannan cakwakiya ta Maryam!

Wayarshi ta yi ƙarar shigowar saƙo, bai yi nawa ba wajen buɗe saƙon ya tarar da ɗan matsakaicin rubutu.

_Kar ka cutar da idanunka don son ganin abin da babu shi, kar ka wahalar da zuciyarka kan saƙa tunanin abin ba zai taɓa wanzuwa ba… Ka daure ka hutar da ƙwaƙwalwarka ka biya wa gangar jikinka haƙƙinta…

_Ka saka wa zuciyarka salama ka kwanta ka yi bacci… idan kana son jin labarin Maryam ka tabbatar ƙarfe bakwai na safiya ta yi maka a wannan wajen… (aka rubuta adireshin wajen)_

_Idan ka wuce haka kuwa kai da Maryam har abada.._

Ya karanta ya sake tisawa, ya karanta ya fi sau shurin masaƙi, abu biyu dai zuciyarshi ke ba shi, su ne bin umarnin abin da ke cikin saƙon, da kuma kiran lambar don ya ji wadda ta turo saƙon, sai dai ko da ya kira ɗin ma lambar ba ta tafiya, da ya matsanta yin kiran ma sai aka fara ce masa wannan lambar da ya ke ƙoƙarin kira ma sam babu ita (does not exist) don haka ba tare da ya sake ayyana komai ba ya juya zuwa ga gado ya kwanta ya runtse ido cike da fatan nannauyan bacci ya zo ya yi awon gaba da shi.

Ƙarfe shida da rabi na safe ya fice daga ɗakin, ya shige motarsa ya fice daga hotel ɗin. Sai bayan fitar sa ne Kamal ya farga da ba ya nan, da sauri ya tashi Turaki yana faɗin “Ya Turaki Yaya fa ya fice ba tare da ya yi wa kowa magana ba.”

Turaki ya miƙe da sauri yana murje idanu, “Kira shi a waya ka ji inda ya tafi.”

“To.” Kamal ya amsa tare da ɗauko wayarsa ya lalubi lambar Isah ya kira, sai dai har ta ƙaraci ringing ɗin ta bai ɗaga.

“Bai ɗaga ba.” Kamal ya ce yana sauke wayar.

“Ƙara kiran shi, may be yana tuƙi ne.”

Ya sake kira, duk sammakal, sai suka yi cirko-cirko. Daidai lokacin kuma ‘yanSandan biyu suka fito daga cikin ɗaya ɗakin da suka kwana, kasancewar dama Family room ne suka kama, ɗakuna biyu ne cikin ɗan madaidaicin falo, don haka su ‘yansandan a ɗaki ɗaya suka kwana su ma su Isah suka kwana su uku a ɗaki ɗaya.

“Me yake faruwa ne?” Sergent ya tambaya.

“Isah ne ya fita, kuma bai sanar da kowa inda za shi ba, sannan na kira wayarsa ma bai ɗaga ba.”

Kamal ya koro bayani.

“Me ya sa ba ku yi saurin sanar da mu ba kafin ya fice?”

“Wallahi kawai fitowa na yi daga toilet na ga ban ganshi ba, shi kuma Ya Turaki bacci ya ke bai ma san ya fita ba, da na leƙa gurin ajiye motoci sai na ga ban ga motarshi ba.”

“Kamar misalin ƙarfe nawa kake zaton ya fita?”

“Gaskiya bai jima ba, don tare fa muka yi sallar asuba, kuma duk tare muka koma bacci.”
Suka yi shiru kowa na nazari.

Isah ya yi nisa cikin tuƙinsa, alla-alla yake ya isa gurin kafin cikar ƙarfe bakwai, duk gudun da ya ke tsugawa sai ya ke ganin kamar tafiyar kunkuru yake musamman yadda ya ga saura ‘yan ƙwayoyin sa’o’i bakwan ta cika.

Da na’urar nuna guri wato (location map) na jikin wayarsa ya ke amfani yana bin adireshin don bai san gurin ba tun da dudu bai wuce sau uku ya taɓa shiga Lagos ba, kuma ba wani shige-shige ya yi ba don haka ba ko’ina ya sani ba.

Lokacin da bakwai ta cika daidai lokacin ya samu isa gurin. Wajen ya yi kama da gidan cin abinci (restaurent), guri ya samu ya faka, ya fito da sauri yana rarraba idanu tamkar mayen da ya shiga kasuwa.

Dabarar kiran lambar da aka turo masa saƙon da ita jiya ta faɗo masa, bai ƙi bin shawarar ba duk da in bai manta ba a daren jiyan an ce masa number babu ita amma dai an ce da jarrabwa jirgin sama ya tashi.

Abin kamar siddabaru yana kira sai ga shi wayar ta shiga, idanunsa kyar a kan wata matashiyar budurwa da ke zaune gaban teburin abinci tare da wani saurayi kyakkyawa fari ƙar, da an gan shi an ga balarabe. Budurwar ya hango ta zuge jaka ta zaro waya, babu ɓata lokaco ta shafa wayar ta kara ta a kunne.

Dukkan abin da take faɗa shi yake jin na fita daga cikin mafitar sautin wayarsa (speaker) yana shiga kunnuwansa.

“Ka taki babbar sa’a! Mituna biyar da ka ƙara da ka rasa babbar dama a rayuwarka! Wannan ya nuna ka san muhimmancin lokaci saɓanin wasu daga cikin ‘ya’yan Adamu… abin da za ka yi yanzu shi ne ka koma cikin motarka, ka katse wannan kira da ka yi min, ni zan kiran ka da dukiyar cikin wayata, ba na buƙatar ka katse kiran nawa don ta haka ne zan maka kwatancen inda za ka je ka ga Maryam ɗinka!”

Kamar akwai rainin wayo cikin lamarin matar nan_ abin da ya ji a ranshi kenan, don haka cikin ƙwarin gwiwar da bai san a duniyar da ya samo ta ba ya watsa mata tambaya.

“Amma ba ke ce na ke ganin ki a zaune ba tare da wani Balarabe?” Da ya yi tambayar Sai kuma ya baza idanunsa gare su inda ya yi arba da fuskar budurwar a turɓune tana aiko masa da saƙon muguwar harara.

Ya yi saurin ɗauke kai, kafin ya ce wani abu ko ita ta ce, sai ya ji ɗif an katse kiran, ya sake kira shiru ta ƙi tafiya, ɗago kanshi da zai yi sai ya ga budurwar nan tare da saurayin balarabe sun miƙe suna harhaɗa kayansu, ya yi tsai yana kallon su har suka gama tattara komatsansu suka fito daga ɗakin cin abincin, ta inda ya ke tsaye suka zo suka wuce, sai da ta juyo ta auno masa doguwar harara, har da gajeren tsaki sannan ta yi gaba.

So yake ya tsayar da ita ya yi mata magana amma tamkar wanda aka ƙullewa harshe, yana ji yana gani suka shige mota suka bar wajen…

Shigowar kira a wayarsa ne ya dawo da shi duniyar hankali da lissafi, number Kamal ce, da kamar ba zai ɗaga ba don bai son su kawo masa tsaiko, ya fi so shi kaɗai ya warware wannan ƙulli ya gano inda Maryam take duk da a yanzu dai gayyar ta lalace, ko a ce ya lalata.

“Yaya ina ka shiga ne tun ɗazu ina kiran wayarka amma ba ka ɗauka ba?”

“Na fita wani uzuri ne, kar ku damu i’m safe, babu abin da zai faru.” Bai ba shi damar sake magana ba ya katse kiran ya saka wayar a jirgi (flight mode).

Cikin motarsa ya koma ya zauna jimmm cikin yin birkitaccen tunani, da a ce lafiya-lafiya ne, a yanzu daidai lokacin da yake buƙatar karin safe ne, amma abin mamaki yanzu tamkar wanda ya ci ya ƙoshi, ba ya jin yunwar komai ba kuma ya sha’awar cin komai.

Sanannen abu ne wayar da ke cikin (Aeroplane mode) tamkar wayar da aka kashe ce, don kuwa babu kira ko saƙo da zai shigo ko ya fita, amma bisa ta’ajibi da mamaki sai ga kira ya faɗo wayarshi da ɓoyayyiyar lamba, sai dai an yi kiran ne bisa tsarin kiran gaggawa (emergency call).

Ya yi zugudum yana kallon wayar, yayinda cikin ƙirjinshi ake ta fafatawa da zuciyarshi da ke hanƙoron yin ƙunar baƙin wake ta tarwatsa komai na ƙirjin. Hakan ya sabbaba masa tsoron da ya yi tasirin sakawa ya gagara ɗaga kiran har ya ƙatse, aka sake kira ya katse, aka sake yi karo na uku, sai ga shi shi ma ya yi ƙunar baƙin waken ya ɗaga yana ayyana duk abin da zai faru ya faru!

Muryar Maryam ya tsinkaya cikin rishin kukan tana neman agaji tana ƙwala masa kira “Ya Khalifa! Me ya sa za ka yi haka? Me ya sa za ka bijirewa umarnin shugaba? Shin dama ba so kake ka ceto ni ba? Dama duk ƙaunar da kake faɗin kana min ba ta tsarga zuciyarka ba? Idan ka sake rasa ni a wannan karon ma to ka tabbata ka rasani har abada, ni da kai sai dai mu haɗu a lahira… ka bi umarnin shugaba ka cece ni….”

Kiran ya katse, yadda jikinshi ke rawa kwatankwacin tsohon baushen da ya yi arba da kiɗan farauta, gumi kuwa tuni ya gama wanke ƙwalisarsa, babu abin da ya ke buƙatar yi a yanzu face addu’a, idan akwai sharrin shaidanu cikin lamarin Allah ya maganta, haka yake ji a ransa!

Ya sake kallon wayar tashi, kamar kuma wanda aka ba wa umarni sai ya cire ta daga jirgin da ya saka ta, ai kamar jira ake yi sai ga kira shigo.

“Idan har ka matsu ka na son ganin Maryam to ka bi duk abin da na ce, babu tambaya babu nuna shakka da kokwanto, na yi maka alfarma ɗaya ba zan yi ta biyu ba, don ni alfarma ɗaya na ke yi a rayuwata, don haka in ka ga dama ka kunna motarka…”

Jiki na rawa ya yi wa motar makulli ta tashi, ya saka giya, sai ya ji a wayar an sake yin magana “…ka miƙe kan titin da kake…”

Ba musu ya ɗau hanya, sai da ya yi tafiya mai ɗan nisa ya zo shatale-tale sannan aka sake yi magana “… ka bi hannun damanka…”

Ya bi, sai dai abin da ya fara hangowa shi ne, ruwa, tabbas ruwa ne a gaban sa ya ke hangowa da tafiya kaɗan, gabansa ya faɗi, me ke shirin faruwa da shi ne? Innalillahi… ya soma maimaitawa a zuciyarsa, bai kuma dakata da tunkarar ruwan ba har sai da ya zamana bai fi saura tafiyar minti ɗaya ba ya isa ga ruwan ya ji an ce “… ka yi kwanar hannunka na hagu…”

A fili ya saki ajiyar zuciya, idnunsa suka yi wiƙi-wiƙi tamkar wanda ya kwana gudawa. “… idan ka yi arba da wasu matasan samari Yarbawa ma su sanye da baƙaƙen kaya ka yi parking gaba da su kaɗan…” Hakan ce ta faru, bayan ya yi parking sai ya yi shiru yana jiran umarni.

“ka cire key ɗin motar ka fita…” ya yi yadda aka ce, “… ka samu ɗaya daga cikin Yarbawan nan na ka ba shi key ɗin motar taka amma kar ka sake ka yi magana…”

A zuciyarshi bai daina roƙon Allah ba har ya aiwatar da umarnin, yana ba da mukullin motar sai gani ya yi wanda ya ba wa mukullin ya nufi motar ta shi ya shige ya kunna ya tafi.

Kuka ko ihu zai yi?

Ya dai yi zugudum yana ayyanawa a ransa lallai wannan kazar wahala da ya yanka wa kansa yana fige ta da tashin hankali.

Aka sake cewa a cikin wayar “… ka taka da ƙafarka zuwa ƙarshen lungun nan za ka tarar da shagon kanti ka tsaya a nan…”

Da ya isa ƙarshen lungun sai aka ƙara cewa “… ka ba wa mai kantin wayar taka…”

Hannunsa na rawa ya miƙa wa mai kantin wayar, sai ya koma gefe yana rarraba idanu.

Jim kaɗan ya ji an kira sunansa, ya kai dubansa gurin, wannan matashin Balarabe da ya gani a gidan abinci shi ne ya sake fitowa daga wani gida yana ƙwala masa kira.

Ba tare da shakka ba ya nufi gurin sa tun da dai a halin yanzu ba shi da zaɓin komai sai yadda aka yi da shi, ba waya ba mota.

Ya bi bayan Balaraben yana mamakin wannan al’amari, ashe dama gidansu za su kawo shi amma don mugunta shi ne sai da suka gasa masa aya a hannu?

Suna zuwa bakin wata ƙofa Balaraben ya tsaya cak tare da nuna masa ƙofar shi kuma ya yi baya.
Isah ya ɗan yi jim yana lissafi irin na wanda zai shiga rijiya, ya shiga ta ka ko ya shiga ta ƙafa.
Daga sama ya jiyo sautin magana, “Ka buɗe ƙofar ka shigo mana Malam Isah!”

Da ya ɗaga kansa sai ya yi arba da wannan budurwa da ya gan su a gidan abinci tana leƙen shi ta tagar bene.

Kaiii! Amma mutanen sun iya baƙar mugunta!

Ya tura ƙofar ya shiga, wani irin ni’imtaccen sanyi da ƙamshi ya marabci jikinsa, ya lumshe idanu, nan take sai ya ji gajiya ta saukar masa, yunwar cikinsa ta fara tasowa.

Yana nan tsaye ya ji an yi sallama an shigo ta wata ƙofa.

Budurwar nan ce dai ta shigo fuskarta kamar gonar audiga don fara’a. “Ka zauna mana Malam Isah.”
“Ina Maryam ɗin take?” Ya tsinci kansa da jefa mata tambaya.

Ta yi murmushi, “Maryam ko? Hmmm! A wannan duniyar dai Maryam ta yi maka nisan da duk tsananin gudun ka ba za ka iya cim mata ba!”

Ya watsa mata mugun kallo, “Kenan yaudara ta kika yi ta hanyar amfani da Maryam?”
Ta yi shiru tana cigaba da murmushi.

“Wace ce ke?”

Ya sake watsa mata tambayar, wannan karon ma dai ba ta tanka ba, nan ya shiga laluben aljihunsa yana neman wayar da ya manta an karɓe ta a waje.

Cikin tunstirewa da dariya ya ji ta ce “Ka manta ka ba wa wani wayar taka a waje?”

Hankalinsa in ya yi dubu ya tashi, Innalillahi… ina ya kawo kansa? Wace irin makantar zuci da ta idanu ce ta same shi har aka yi masa wannan muguwar yaudara haka?

Nan take sai ga hawaye sun fara sartu a kumatunsa. So masifa ne! So bala’i ne,! So ne ya jawo masa shiga wannan hali, so ɗin ma na wacce ta daɗe da mutuwa!

“Kuka kake yi Isah?”

Ya watsa mata harara.

Ta tako ta zo gaf da shi ta tsaya, “A halin yanzu cikin matuƙar yunwa da gajiya kake ni na sani, ba ka karya kumallo ba don haka ka zauna mu karya tare in ba ka labarin Maryam!”

“Ƙarya kike azzaluma! Kuma ki sani mugun nufinki ba zai taɓa cika a kaina ba!”

Yanayin fuskarta ya sauya zuwa damuwa, kafin wani lokaci hawaye sun kwace mata. Cikin rawar murya ta ce da shi “Ko kaɗan ba ni da mugun nufi a kanka, hasali ma dai taimako zan yi a kan haƙƙin ran Maryam da aka salwantar…”

“Kina so ki ce min Maryam ta mutu ne da gaske? Tukunna ma ke meye haɗin ki da ita, a ina kika san ta?”

Ta girgiza kai “Ka zauna, ina zuwa.” Ta wuce zuwa wata ƙofa, bai iya zama ba yana cigaba da wassafe-wassafe.

Jim kaɗan ta dawo hannunta ɗauke da wasu tarin takardu, tana zuwa ta zube su a kan teburin tsakiyar ɗakin, ta bubbuɗe takardun tana nuna masa.

Duk takaddun hotuna ne a jiki, hotunan maryam da kuma na wasu mutane.

Jikinshi na rawa yake duban hotunan Maryam, tabbas Maryam ce tare da wani matashi, kusan duk hotunan su tare suke, sai dai yanayin shigar da ke jikkunansu ta yi muni, kusan tsirara-tsirara suke.
Da sauri ya runtse idanunsa yana jin zuciyarsa na ƙara ɗaukar ɗumi.

“Waye shi wannan ɗin?”

“Ban san iya adadin sunan da ya yi amfani da shi ba tsawon rayuwarsa, amma dai sunanshi KABASA a duniyar UJOSA.”

“Me kenan?”

“DUNIYAR TSAFI.”

Ya zaro idanu a matuƙar tsorace, kafin ya kai ga cewa wani abu ta sake bankaɗo wani hoto, “Ka gane wannan?”

Ya kai dubansa ga hoton, nan take ya shaida Abdulnasir, “Na gane shi ƙwarai, ya so Maryam sosai”
“Yana ina yanzu?” Ta watsa masa tambayar.

“Ya daɗe da rasuwa.”

Ta samu guri ta zauna, “Ka zauna Isah, zan ba ka labarin Maryam!”

Tun kafin ta rufe baki sai ga shi zaune jaɓar a kan kujera.

Ta miƙe, “Yana da kyau ka fara karyawa tukunnuna, kafin sannan su Turaki sun ƙaraso!”

Da sauri ya kalle ta cikin shakku, ta watsa masa murmushi “Su Turaki dai da sauran ‘yansandan da kuka taho neman Maryam, na sa a taho da su ne don ba zan ba ka labarin kai kaɗai ba.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 4Siddabaru 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×