Skip to content
Part 6 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Waiwaye Adon Tafiya

Domin tafiyar ta yi kyau, bari mu adonta ta da waiwayen bayan rayuwar Maryam mu ga me ya faru a jiyan rayuwarta? A wane yanayi yau ɗinta take ciki?

Maryam Ahmad Isah, shi ne sunanta cikakke na yanka, alaƙar da ke tsakanin su da Isah Tukur Isah (Khalifa) alaƙa ce makusanciya, wadda a Hausance ake cewa ‘yanmaza zar suke.

Alhaji Tukur Isah tare da ƙaninsa Alhaji Ahmad Isah, yadda suke su biyu jal kamar idanu su kenan nasu iyayen suka mallaka. Iyayensu ba su kasance mawadata ba sai dai rufin asiri da watar zuci, don haka sun sha gwagwarmayar rayuwa har zuwa lokacin da ƙafafuwansu suka kama ƙasa.

Mata biyu Alhaji Tukur ya aura, Hajiya Rahma uwargida Hajiya Fatima amarya.

Hajiya Rahma mahaifiyarsu Isah mace ce zazzafa kuma mai aƙida, tana da ɗabi’ar girmama buri, ta yadda ta yi komai don cim ma dukkan ƙudirin da ta sanya a gaba, don haka su Isah ke yawan fuskantar ƙalubalai daga gare ta saboda saɓawar hali, duk da kasancewar shi ɗan fari gare ta babu wani kau da kai tsakanin su, takan shata masa layi duk lokacin da ta fuskanci zai ƙetare iyakarta.
Suna da ‘yaya bakwai tsakaninta da Alhaji, maza da mata.

Hajiya Fatima kuma ‘ya’yansu biyu cal tsakanin su da Alhaji, wanda kana ya haɗa jimillar ‘ya”ya tara ga Alhaji Tukur.

Sai kuma shi Alhaji Ahmad da tashi zuriyar, Matarsa ɗaya Hajiya Karima, ita ma dai ‘ya’ya bakwai ta haifa kamar haɗin baki. Turaki wanda ainahin sunansa Sulaiman, shi ne ɗa na fari a gidan, sunan kakanaa ya ci na wajen uwa, ake masa laƙabi da Turaki.

An samu tsaikon ƙarin haihuwa dag kan shi tsawon shekaru goma, har Alhaji Ahmad ya ƙara aure, sai kuma wani akasi na rabo ya faru, wato amarya da uwar gida suka samu ciki kusan lokaci ɗaya. Mamansu Turaki ita ta fara haihuwa ta haifi ɗiyarta mace, kwanaki goma sha biyu tsakani ita ma amarya Maryam ta hau naƙuda ba ji ba gani, sai dai haihuwar tata ta zo da tangarɗa yadda ta kasa haihuwa da kanta sai da aka yi C.S aka shiri ɗiya mace. Allah da ikonsa ba a wuce mintuna arba’in da yin aikin ba ta ce ga garinku nan.

Murna sai ta koma ciki, Alhaji Ahamd ya dinga kukan rashin salihar mace koda dai ita ma Hajiya Karima ba baya ba wajen karamci.

Ita aka ba wa ɗiyar ta haɗa da tata mai suna Zainab ta cigaba ɗa shayar da su, ranar suna aka mayar wa da yarinya sunan gyatumarta, Hajiya Karima ta cigaba da kula da su suka zame mata tagwaye.

Koda ‘yan biyu da ake haifa ciki ɗaya, jakar mahaifa ɗaya waɗanda a likitance ake kira (identical twins) sukan zo duniya da mabambantan halaye da ɗabi’u balle su Maryam da Zainab da kowacce cikin uwarta daban. Tun yarintar su halayensu suka fara bayyana na yadda Maryam ta kasance yarinya mai ƙiriniya, fitina, rashin ji, ga kafiya da gaddama, ko za a yanka ta ba za ta fasa dukkan abin da ta sanya a gaba, yayin da gefe ɗaya Zainab ta kasance saliha mara kwaramniya, bar ta dai da yawan zance, amma sam ba ta iya rigima ba, duk da ita ce babba hakan bai hana Maryam zaluntar ta ba, sai dai ta zauna ta yi ta kuka.

Tabbas Hajiya Karima ta cancanci a yaba mata da irin karamci da kararta, domin kuwa dukkan abin da ke faruwa tsakanin Maryam da Zainab ba ta taɓa nuna bambanci tsakanin su ba, ko ta ɗaga ido ta kalla, a gare ta dukkansu ɗaya ne tun da duk daga gare ta suka sha. Ko a gurin shayarwa ma haka Maryam ke galla mata cizo mai tsananin zafi, amma sai da ta runtse ido kawai, idan kuwa Zainab ce ta cije ta wani lokacin takan kai hannu ta ɗan buge ta ko ma ta zare ta daga ba ta maman. Hakan ne ya sa kwata-kwata Alhaji bai taɓa fuskantar wanu abu na faruwa har sai zuwa lokacin da suka fara tasawa, lokacin Karima ta yaye su har ta yu musu ƙani.

Sannu a hankali Alhaji Ahmad ya fara fuskantar irin halaye marasa kyau daga Maryam, ko kaɗan bai zargi Karima ba don ganin yadda ita Zainab take kamammiya kamilalliya. A duk lokacin da Maryam ta zalunci Zainab zai kama Maryam ya yi ta kwaɗar ta ne har sai Karima ta zo ta janye ta tana faɗin, “Haba Alhaji! Don me za ka dinga shiga faɗan yara? Ka bar su mana tare su ci kansu, ta yaya Zainab za ta zama jaruma idan har kana rama mata duka?”

Yakan ce, “Wannan yarinyar baƙin hali ke gare ta, sam ba ta gaji halin marigayiya ba, dole sai na dinga hukunta ta in ba haka ba ba za ta gane tsakanin ta da ‘yar uwarta ba.”

Daga nan sai ya ja Zainab ɗaki ya ba ta kayan maƙulashe yana cigaba da rarrshin ta, yayin da ita kuma Karima za ta kama hannun Maryam da niyyar jan ta zuwa ɗaki, sai ta fizge hannunta ta koma gefe tana kumbure-kumbure.

Ire-iren waɗannan abubuwan da suka cigaba da faruwa sai tubalin tsanar Zainab ya fara ginuwa a zuciyar Maryam, sai take ganin ƙarara Abbansu na nuna bambanci tsakanin ta da ‘yar uwarta wacce duniya ke kallon su a matsayin tagwaye, duk da cewa ba a kama ko kaɗan, kowa kalar uwarsa ya ɗauko. Duk wannan na faruwa ne tun da kankantar shekarun Maryam tun ba ta fahimci ba Karima ba ce mahaifiyarta ba ma.

Akwai zumunci mai ƙarfi tsakanin gidan dangin junan biyu, wato kusan kowanne lokaci sukan ziyarci juna, sa’annan duk bayan ƙarshen wata sukan yi taro ya-su ya-su, idan wannan wata aka yi a gidan Alhaji Tukur, wata na gaba a gidan Alhaji Ahmad za a yi, wannan ta sa akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin dangin.

Duk lokacin da aka samu hutun makaranta zainab da Maryam akan kai su gidan Alhaji Tukur su yi hutu, a saboda ƙiriniyar Maryam ta sa babban yaya wato Isah ke yawan jan ta a jiki, saboda hakan nan a ransa ya ji yarinyar ta shiga ransa saboda a cewar sa ita ɗin jaruma ce, saboda duk tsararta babu mai kawo mata wargi, kai har na saman ta ma takan ba wa wasu kashi idan an gwada ‘yar ƙashi.

Duk lokacin da suka zo hutu wuni suke tare musamman idan ranar bai je tashi makarantar ba, ko kuma bai fita wajen sana’arsa ba, nan zai ja su zuwa ɗakinsu ya kunna musu kallo, in sun gaji da kallon ya kwashe su tafi cikin gari shan iska ko kuma ya kai su shagon sayar da kayan ƙwalam ya narko musu siyayya, amma fa sai ya nuna bambanci, don kuwa komai na Maryam daban yake, sai ya bambanta da na kowa.

Koda Mamansu (Mama) hankalinta ya fara kai wa ga wannan shaƙuwa ta tsakanin Maryam da Isah da yadda yake bambanta ta da kowa, har waɗanda suke ciki ɗaya ma, sai ta fara shiga damuwa, lissafinta bai ƙara dagulewa ba sai da ta fuskanci yadda ƙiri-ƙiri Isah ke jibgar Saliha idan wani abu ya shiga tsakanin su da Maryam ɗin ta saka ta kuka don dama ba sa’arsu ba ce, kuma ita ma Salihar ba baya ba ce wajen rashin ji.

Ran Mama ya ɓaci matuƙa, ta ji ta tsani yarinyar, haka nan yarinyar ba ta kwanta mata a rai ba ko kaɗan, musamman wani lokaci da ta dinga yi mata gunguni kan ta tsawatar mata bisa rashin jin ta. Ranar wuni ta yi cikin nunkufurci, ta ƙi yi wa kowa magana, da Anty Sa’adatu ta yi mata magana ma sai ta yi mata rashin kunya, Sa’adatu ba ta ɗaukar wargi don haka ba tare da ɓata lokaci ba ta kwakkwaɗe ta, ai ko Maryam ta tuburr ta dinga zuba tijara da rashin kunya har Isah ya dawo daga makaranta, koda ya tarar da Maryam na kuka ya tambaye ta ta faɗa masa dukan ta Anty Sa’adatu ta yi, ai bai ɓata lokaci ba ya wuce ya samu Sa’adatu ya yi mata tas, ta dinga kuka.

Ran Mama in ya yi dubu ya ɓaci, ta gaji da wannan hali da yaron nata ya ɗauka na ƙin ‘yan uwansa a kan wata Maryam don haka ta rufe shi da faɗa.

“Wane irin sakarai ne kai da za ka zauna kana bautar mitsitsiyar rayinya har kana tsanar ‘yan uwanka jininka a kan ta? Shin tsakanin su da ita wa ya fi kusanci da kai?”

Ya yi saurin cewa “Amma Mama ba kya ganin yadda suka takura wa marainiyar Allah? Don me ya sa kowa zai tsane ta…?”

“Don me ya sa ba za a tsane ta ba iye? Na ce don me ya sa ba za a tsane ta ba tun da ba ta da kunya ba ta da mutunci? Mitsitsiya da ita sai baƙin hali da rashin kunya, to wallahi ka shiga taitayinka, kar ka sake taɓa min yara a kan wannan figaggiyar, ranka zai mugun ɓaci wallahi…” Ta ƙare faɗan cikin masifa, idanunta har ƙanƙancewa suke.

“Mama bai kamata fa ki dinga nuna bambanci tsakanin su Saliha da Maryam ba, ni duk ɗaya suke a wajena, dukkan su ‘yan uwana ne…”
“Ni kake faɗawa haka Khalifa? Wato har an fara kai wa jallin da za ka dinga faɗa min dukkan abin da ya zo bakinka a kan Maryam? Nan gaba me zai faru kenan?” Ta zuba masa idanu tana girgiza kai cikin matuƙar mamakin yadda yaronta ya sauya lokaci ɗaya, kuma duk a kan zuwan Maryam gidan.

“To wallahi tun wuri zan yi wa tufkar hanci, Maryam ɗin ma zan hana ta zuwa gidan nan, kuma dole gobe su koma gidansu su ƙarasa hutunsu a can, hutun ma sun daina zuwa…”
“Amma Mama…”

“Yi min shiru, shashasha wanda bai san inda ke masa ciwo ba.”

Ta nuna masa hanyar ƙofa da yatsanta, “Fice ka ba ni guri.”

Ya juya ya fice cikin rashin jin daɗin abin da ya faru tsakanin sa da Mahaifiyarsa.

Da dare Mama ta je ta samu Alhaji ta kalallame shi da maganganu a kan a mayar da su Maryam gida saboda rashin jin ta ya yi, ga tsokana ga rashin kunya, a cewar ta kullum sai sun raba su faɗa tsakanin ta da Saliha.

Da mamaki Alhajin ya ce, “Wace Salihar wai? Yanzu ita Salihar gototo da ita ta zauna suke faɗa da Maryam? Ina ce duka tsakanin Maryam bai wuce watanni biyu ba?”

“Kwana saba’in ne tsiransu, amma ai ka san ita Maryam da raina na gaba da ita, kwata-kwata ba ta faɗa da sa’annin ta sai da wanda ya Jgirme mata, don haka gwara su koma gida ko ma huta mu ma.”

Murmushi kawai ya yi ya canza musu magana, duk da ita ɗin ba haka ta so ba, so take sai ya amince gobe sai an mayar da su, don haka duk maganarta ta kushe Maryam ce.

Dole ba don ta so ba sai da suka ƙarashe hutunsu sannan suka tafi, a ɗan tsukin lokacin kuwa abubuwa da yawa sun faru marasa daɗi.

*****
“Umma wai ni marainiya ce?”

Kwatsam Hajiya Karima ta ji wannan tambaya daga bakin Maryam a wani lokaci bayan dawowar su daga makaranta.

Zaro idanu ta yi waje cikin maɗaukakin mamaki. Da sauri kuma sai ta ce.

“Ke a ina kika ji wannan maganar ta shirme?”
“A wajen Mamansu Ya Khalifa, da muka je hutu gidan kullum sai ta yi mishi faɗa idan ya yi min siyayya ko in muka yi faɗa da su Saliha ya rama min sai ta yi ta cewa a kan wannan figaggiyar marainiyar zai dinga dukar mata ‘ya’ya?”

Umma ta janyo ta jikinta, “Ba da ke take ba Maryam, ke ai ba marainiya ba ce, kina da uwa da ubu, shi ko duk wanda kika ji an ce wa maraya ko marainya to wanda ya rasa uwa ne ko uba.”

“To amma umma…” Ta haɗiye maganar tata ganin shigowar Zainab sanye da hijabinta, ta zabura ta miƙe ta je ta cukwikuye Zainab ɗin tana masifa.
“Uban wa ya ce ki saka min hijabina? Ba na hana ki taɓa min kayana ba?”

Suka fara kiciniyar kokowa, daga inda Umma take ta soma yi musu tsawa amma funfurus Maryam ta ƙi sakin Zainab, ƙarshe ma sai ta rufe ta da duka, ta dinga jibgar ta har ta sanya ta kuka.

Da ƙyar Umma ta shiga tsakani, “Ke ce ba ki da gaskiya Zainab, wa ya ce ki saka mata hijab ɗin ta?”

Kuka kawai Zainab ke yi, ta san da ace Abban na nan ba zai ba ta rashin gaskiya ba tun da ita ma Maryam ɗin tana taɓa mata nata kayan.

Ba wai Umma ba ta damuwa da damuwar Zainab ba ne, tana yin kawaici ne a kan don ta yi abik ake cewa ka ƙi naka duniya ta so shi. Kuma ko ba komai tana so ta kuɓuta daga bakunan ‘yan gaza-gani, waɗanda za su ce tana fifita tata kan ‘yar riƙo.

Ba ta san me mai gidan na ta ya gano ba sai ga shi da dare ya ɓullo mata da zancen Maryam.
“Karima dayake Allah ya sa na san yadda kike iyakar bakin ƙoƙarinki a kan yarinyar nan ba zan taɓa zargin cewa kina sane kika bar ta ta zama mara jin magana ba, na tabbata idan aka samu uba mara fahimta kai tsaye zai ce don ba ke kika haife ta ba ne ya sa kika bar ta ta zama haka, wallahi halin yarinyar nan ya fara isa ta…”

“Wai me ya faru ne Alhaji, wani abun ta aikata?”
“Hmmmm!” ya fidda numfashi, sannan ya ɗora, “Tsokana mana, ta samu ɗiyar Alhajin Lawan, Mabaruka ta jibge ta da uwar yarinyar ta fito ta yi mata magana sai ta hau yi mata rashin kunya.”
“Oh Ni Karima, Maryam kam ta ji daɗin ta, Allah ya sani ina iyakar bakin ƙoƙarina, da a ce ina da damar sauyawa mutum halinsa wallahi da sai na mayar da Maryam ta zama kamar Zainab, ko ma ta fita nutsuwa amma…” Sai ta yi shiru.

Maryam da ke tsaye a bakin labule ta ji dukkan tattaunawar, yanzu dai ta tabbata da gaske ba Umma ce ta haife ta ba, ita ummanta ta rasu, sai ta fashe da kuka.
Koda suka zo kwanciya ma kuka ta dinga yi, tambayar duniyar nan Umma ta yi ma ta ko kanzil kafiyayyiyar yarinyar nan ba ta tofa ba, ƙarse ta haƙura ta ƙyale ta.

Tun daga wannan rana kuma sai Maryam ta sauya ɗabi’a, sai mutum ya rantse da Allah zama aka yi aka koya mata janye jiki daga Umma, kwata-kwata ya daina yi da kowa a gidan, ta ware kanta ta zama marainiyar gaske.

Hankalin Umma ya tashi sosai, ta samu Abbansu da maganar, ya kira yarinyar ya saka ta gaba da tambayoyi, amma funfurus ta ƙi, a juya ta damu-taliya ba za ta ce komai ba, har ranshi ya ɓaci ya hau jibagar ta, amma abin mamaki zuciyar yarinyar ta ƙeƙashe, hawaye ko gamin-gafara babu a idanunta…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 5Siddabaru 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.