Skip to content
Part 7 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

A tsari irin na hallitar wani kaso na daga cikin mutane, mace ko namiji, a duk lokacin da aka ce shekarun girma sun fara cim ma sa/ ma ta, sukan tsiro da wasu ɗabi’u marasa kyau, kamar zafin rai, saurin fushu da ganin kai ɗaya suke da kowa, da jin ƙwanjinsu ya yi ƙoshin da za su iya karon-batta da kona waye, don haka sai tsoro ya disashe a zuciyarsu, kafiya da taurin kai su samu wurin zama.

A irin wannan ƙadamin ne idan yaro bai samu kyakkyawar tarbiyya da ingantacciyar addu’a daga iyaye ba sai ka ga yaro ya bauɗe ya sauka daga layi.

(Don haka iyaye sai a ƙara kulawa, idan yara suka fara kai wa munzalin balaga suka tsiro da irin waɗannan ɗabi’u ba kyara ko zafafawa suke buƙata ba, tattashi da ja a jiki suke buƙata da kuma addu’a, don a kan siraɗi suke ko su tsallake ko su faɗa.)

Irin waɗannan baƙin ɗabi’u suka haɗu da halayen Maryam suka samar da wata kangararriyar budurwa marar jin magana da rashin shakkar kowa, ba wanda ya isa ya saka ta ko ya hana ta, idan ta hau kan dokin ra’ayi babu wanda ke da ƙwanjin sauke ta koda kuwa dokin ba hanya mai ɓullewa ya nufa ba.

Maganar da ake yanzu sun kammala sakandiri ita da ‘yar uwarta Zainab, har ana maganar sanya ranar auren ita Zainab ɗin da saurayinta Hafiz wanda suka kwashe tsawon shekaru biyu suna ɓarje soyayya. Saɓanin Maryam da ba ta ma buɗe kofar da samari za su shigo neman zuciyarta ba, ba rasa samari ta yi ba don kuwa tana da tsananin farin jini, sabosa ita ɗin kyakkyawa ce ajin farko, ita da Zainab ba a ce ga wadda ta fi wata ba, sai dai dukka a ce ma sha Allah, Allah ya yi halitta.

Isah (Khalifa) so yake wa Maryam wanda ya wuce gaban kwatance, so yake mata irin na _na yarda in mutu ke ki rayu_ duk da cewa ita har yanzum ba ta ba shi ammana ba, tana tafiya da shi ne a yadda ya zo mata, mijin da ta ke lissafawa kanta Isah ya tawa da kaso kusa sittin cikin ɗari na lissafin, don haka har wannan maganar da ake ba ta ce tana son shi ba, ba ta ce ba ta son shi ba.

Bayan Isah akwai AbdulNasir wanda shi ma ya zama mataccen rayayye a duniyar son ta, tsananin sa’a ta sa ya samu take ɗan kula shi, wataƙila babu mamaki ko don yawan hidimta mata da yake yi kasancewar sa ɗan masu abin hannu.

Shi ma so yake mata irin na a mutu gaba ɗaya, koda shi kalar nashi son ya bambanta da na Isah, wanda shi bayan so irin na zuciya da zuciya akwai kuma tasirin soyayya ta jini da ‘yan uwantaka, da kuma tsananin shaƙuwa ta aƙalla shekaru sha biyu. Ba kamar shi AbdulNasir da ya gan ta a budurwarta wani abu daga jikinta ya ja ra’ayinsa ya faɗa da ita ba.

Ana dai buga ‘yar ƙwanjin zuciya da farautar soyayyar Maryam a filin daga ƙauna, kowa na kallon kansa a matsayin barde sha-yaƙi da zai ci galabar mallakar zuciyar Maryam.

A wani hannun kuma, lamari ne ke neman kwaɓewa ko ma ya kwaɓe, domin kuwa alaƙa ta fara tsami tsakanin Maryam da Abbansu wanda shi a ƙudirinsa yana son ya haɗa ɗiyoyin nan nsa guda biyu ya aurar da su, yadda suka rayu tare haka yake fatan a ce ya aurar da su, amma Maryam na neman kawo wa wannan ƙudiri tangarɗa, domin kuwa ƙeƙashe ƙasa ta yi ta ce sam ita ba aure take buƙata ba a yanzu, jami’a take da burin zuwa don cimma wani ƙudiri nata.

Wasa-gaske! Da farko Abban bai zata kafaffen ra’ayi ba ne Maryam ta zo da shi don haka bai ɗauki lamarin da girman da zai kawo rikicewar lissafi ba, duba da cewa yana da labarin tsanin son da Isah yake mata, ga kuma wani a gefe ma AbdulNasir da aka ce shi ma ba baya ba ne wajen ƙaunarta.

Ya fi so a ce Maryam ta auri Isah, koba komai an yi tuwona-maina, zumunci kuma zai ƙara ƙarfi, a yadda ya san Isah jajirtaccen namiji gwarzo wanda yake da wayewar zamani da sanin ciwon kai, shi da Turaki nashi ba a ce ga wanda ya fi wani ba.

Har maganar suka yi da ɗan uwansa Alhaji Tukur, shi ma dai kamar an tona zuciyarsa, abin da yake da ƙudiri kenan na ganin dacewar haɗin nasu. Duk wannan ƙudire-ƙudire da ake yi ita ma Mamansu Isah da nata ƙudirin, ta ciki-na ciki.

Rana ta biyu da Abba ya sake zaunar da Maryam don ƙara tuntuɓar ta ya ji ko ta sauya ra’ayi duba da cewa ga shi har an saka ranar Zainab, Turaki shi ma ya nemo tashi za a haɗa a yi gaba ɗaya idan ta amince da auren Isah.

Amma sai tahalikar ‘yar nan ta shayar da uban ruwan madarar mamaki.

Idonta cikin nashi ta ce, “Abba ba yanzu zan yi aure ba, jami’a na ke son shiga don akwai ƙudirin da nake da shi.”

Duk da tafasa da zuciyarshi ke, hakan bai hana shi haɗiyar sassanyan yawu ba ce da ita cikin taushi, “Wane irin ƙudiri ne wannan haka da zai zame miki shamaki da aure?”

Har yanzu ba ta janye idanunta a kan nashi ba ta ce, “Matsayi! Matsayi Abba, na duba na gani a yanzu babu abin da ya wuce mace ta yi zuzzurfan karatu, hakan shi zai ba ta dama ta kai ƙololuwa yadda duk juyi da ita za a dama…”

“Wa kika kalla haka kike kwatanta kanki da zama kamar ta?”

“Akwai mata da yawa Abba a duniyar nan da ake damawa da su, ga su nan birjik…”

“Kin bincika kin ga su ɗin duk babu wacce ya yi aure?”

“Sun yi, amma ba a lokacin da suke kan fafutuka ba Abba, saboda aure kan zama katanga ne ga wasu burace-burace na ‘ya’ya mata yadda har su mutu ba sa cim…”

Ta haɗiye maganar sakamakon wani gigitaccen mari da ta ji saukar sa a kuncinta wanda ya haifar mata da ganin walainiyar taurari. Ta dafe kuncin tana ɗanɗana azabar raɗaɗi a zuciyarta, yayin da fusatacciyar zuciyar ke ƙara ɗora ta a keken ɓera tana ƙara kin ko za a sanya mata wuƙa a maƙohi to wallahi ba za ta yu auren ba, kai ƙarshe ma in ta ga dama ba za ta yi auren ba har gaban abada!
Gama ayyana hakan ke da wuya ta miƙe fuu kamar iska a fusace ta nufi hanyar fita daga ɗakin, yadda uban ke kwaɗa mata kira amma ko ta tsaya haka ta sa kai ta fice ta nufu ɗakin baccinsu ta faɗa gado tana cigabada lasar maɗaci.

Umma tare da Zainab suka shigo ɗakin don ba ta baki, kasancewar sun ji ƙarar marin, suka tarar da ita ta yi da rub-da ciki a kan gado, ba kuka take ba, amma gwara mai kuka da ita a wannan lokaci.

Kafin wani daga cikin su ya ce wani abu suka ga an banko cikin ɗakin, dukkan su suka zabura cikin tsoro, Abba ne ɗauke da narkeken reshen bishiya ya fita ya karyo, yana zuwa bai yi wata-wata ba ya hau Maryam da jibga yana cigaba da masifa.

“Duk iskancin da kike yi ƙyale ki kawai na yi, ba wuce duka kika ba… ban haifi yarinyar da za ta ki jin maganata ba wallahi…” Ya cigaba da jibgar ta Umma na ban baki da ƙokarin kwatar ta, ya nuna mata kar ta sake ta ƙaraso in ba haka ba zai haɗa da ita, ya ci alwashin yau sai ya kakkarya ta in ya so ya biya kuɗi a ɗora ta.

Zainab da sauran yara suka fashe da kuka ganin yadda Abban ya zama tamkar mahaukaci sai surutai yake yana cigaba da zambaɗar Maryam, duk wannan uban duka da yake mata babu hawaye ko ɗis a idonta sai dai gunji kawau da take yi irin na kangara.

Umma ba ta ji kashedi ba isa gare shi da zummar riƙe bulalar, ai tun ba ta ƙarasa ba ya shauɗa mata ɗaya ƙwaƙƙwara sai ga Umma a gefe tana haɗa gumi.

“Maza dauki waya ki kira Yayanku!” Umma ta umarci Zainab, cikin rawar jiki ta ɗauki wayar ta kira Turaki, sai dai wayar ta ƙi shiga.

“Idan bai daga ba kira Alhaji Babba (Babansu Isah).”

A nan kuma garin rawar da hannunta ke yi wayar ta sufce ta faɗi, batirin wayar ya fita, ta tattaro wayae ta haɗa ya kunna sai wayar ta ce caji ya ƙare.

Abu goma da ashirin.

Sai da Abba ya kusa halaka Maryam sannan Turaki ya faɗo gidan kamar an cillo shi, hankalinsa ya yi matuƙr tashi da abin da ta tarar, koda dai Abban nasu da zafi amma bai fiye yin duka ba sai an kai shi maƙura, lallai yau Maryam ta ƙure shi ƙut!

Da ƙyar ya shiga tsakani ya ƙwaci Maryam, sannan ya janye Abban nasu wanda kamar zai yanke jiki ya faɗi.

“Ka yi haƙuri Abba, ka sanyaya zuciyarka, samun kanka cikin wannan yanayin a yanzu akwai matuƙar hatsari… Don Allah ka yi haƙuri Abba.”

Huci kawai Abban ke yi ƙirjinsa na hawa da sauka, Turaki ya je da sauri ya ɗauko ruwa mai sanyi a firji ya tsiyaya a kofi ya kawo masa. Da ƙyar Abban ya haɗiye ruwaɓ da ya ji shi tamkar ruwan magani, amma ya ɗan ji sanyi a ransa bayan shan ruwan.

Kamar ƙaramij yaro haka Turaki ya sake cicciɓar Abban ya kai shi ɗakinsa ya ajiye shi ksn gado, kana ya fuskance shi sosai ya ce.

“Abba don Allah ka ƙara sanyaya zuciyarka, ka rage yawan zafafawa a kan lamarin Maryam, ka riga ka san hali da ɗabi’unta, a yanzu da ta ke kan wannan tsinin sam zafafawa ba zai yi mata ba, don Allah ka ƙara haƙuri Abba.”

Muryar Abban a dashe ya kalli Turaki, “Kenan sai dai a zuba mata ido ta yi abin da ta ga dama Turaki? A ce wannan yarinyar har ta kai jallin da za ta bijere min har in yi mata magana da mayar da ni banza?”

“Ka yi haƙuri dai Abba, ka sani duk wannan abin nata na ɗan lokaci ne, nana gaba kaɗan ko an ce ta yi wani abin ba za ta iya ba.”

“To wallahi muddin ba za ta bi umarnina ba to zan mance da ita cikin lissafin ‘ya’yana, kuma dole ta bar min gida ta je can duniyar da take ruɗar ta ta riƙe ta a matsayin uwarta da ubanta.”
“Ba za a yi haka ba Abba, in sha Allahi ba za a kai ta ga haka ba ma.” Turaki ya ce lokacin da ya ke miƙewa.

Ɗakinsu Maryam ya sake komawa inda ya tarar da su jugum-jugum tamkar waɗanda ke gadin gawa. Ita kuwa gogar na zaune ta cusa kanta tsaƙanin gwiwoyinta ba wanda zai ce ga abin da ta ke yi.

Ya samu guri ya zauna yana fuskantar su.

“Wai me ya faru ne Umma?”

“Ni wallahi ba zan ce ga abin da ya faru ba, Abbanku dai ya kira ta ɗaki ban san maganar da ya yi mata ba sai ƙarar mari muka ji muna daga ɗaki, muka gan ta ta fito daga ɗakin cikin fushi, to mun biyo ta don mu rarrashe ta sai ga Abbanku da reshen bishiya ya hau jibgar ta, ni ma da na je ceto sai da na samu rabona ya fyauɗe min hannu.” Ta ƙare maganar tana nuna masa gefen hannunta da ya yi burɗi.


Cikin rashin jin daɗi Turaki ya jijjiga kai. “Ayya! Lamarin dai duk bai yi daɗi ba… ke Maryan ɗago kanki.”

Idan Maryam ta motsa to ginin ɗakin ma ya motsa, ita fa Maryam gawurtarta ba ya kuɓuta daga kan kowa ba, hatta shi kan shi Turakin da ya ke babban yayansu ba wani shakkar shi take sosai ba ko da can balle yanzu da lamuranta suka giga, ta ƙuna ba ta tsoron hayaƙi.

“Maryam magana nake miki.. Na ce ki ɗago kanki mu yi magana.” Ya sake yi mata magana karo na biyu.

An taki babbar sa’a ta ɗago kan, gasassun idanunta da suka yi fi gaushi ja sun ba wa Umma tsoro, fuskarta ta kumbura suntum, gaba ɗaya kamanninta sun sauya ta juye tamkar wata fusatacciyar zakanya.

Zainab da take matsoraciya ta yi luf a jikin Umma, ita ma Umman sai ta yi ƙam-ƙam da ita.
“Maryan ina so ki nutsu sosai ki ba ni hankalinki mu yi magana.”

Har ilayau dai ba ta tsinka ba, ta dai baza musu idanu tana kallon su da gululun idanu, amma zuciyarta na can ta lula a duniyar cin alwashi, alwashin ko za a saka kanta a yamma a ɗora kakkaifar wuƙa ba za ta sauka daga dokin ra’ayinta ba.

“Maryam da a ce ba ki makaranta ba da sai ya zame min babban aiki da zan zauna kawo miki darasussuka kan muhimmancin iyaye ga ‘ya’yensu, to Alhamdulilahi kin samu ilimi daidai gwargwado, tun kina mitsitsiya ake ɗora ki a layin bin iyaye, abin da ya rage kawai yanzu a tunatar da ke.” Ya ɗan ja fasali sannan ya ɗora.

“Mutum bai isa ya kawo kanshi duniya da kanshi ba, kowa akwai ta sanadin da ya ɓulla ya zo duniya, don haka kenan ya zame dole ga kowa ya yi biyayya ga dukkan wanda ya yi sanadin zuwan sa duniya, wanda inda ya so sai ya bi duk hanyar da zai bi don kar ya haifo kowa… Maryam ko da wasa aka ce min yau ke ce Abba ya saka a gaba yana duka kan bijire masa wallahi mamaki ba zai bar ni in yarda ba… amma abin takaici da idanuna na ha haka… me ya sa haka Maryam? Me ya sa? Mahaifi fa? Anya kina da makwafinsa a duniyarki?”

Ya cigaba da girgiza kai, “Ba ki ɗauko hanyar tsira ba a rayuwa Maryam, wallahi duk wanda halinsa ne ƙuntata wa iyayensa ba zai gama da duniya lafiya ba. Maryam ke mace ce, da rauni aka san zuciyarki, a wajenku ake saka samun tarbiyya ga ‘ya’yayenku, shin ya za ki ji a ce yau ke cw wanda kika haifa ya yi miki haka? Ko kin manta cewa rayuwarki taƙaitacciya ce? Lokaci kaɗan ya rage miki ki tafi ki gina naki zuriyar, shi ba za ki so ki zama abar koyi da kwatance ba?

Don Allah Maryam ki gyara, ki sanya wa zuciyarki salama ki samu ki rabu da duniya lafiya… kuma ki je ki nemi yafiyar Abba domin kuwa fushinsa a kanki na tafiya ne da fushin Allah da Mala’iku a kanki… iyaka nasihar da zan miki kenan matsayina na yayanki.”

Ya miƙe yana kaɗe jiki, ya dubi Umma. “Umma ki ƙara tattashin ta ki lallame ta har zuciyarta ta yi sanyi, ni na fice sai da safe.”

“Allah ya kai mu Turaki.”

Ya juya ya fice yana cigaba da jijjiga kai.
Miƙewa Umma ta yi tsam ta koma kusa da Maryam ta saka hannunta ɗaya ta sarƙafo ta, ɗaya hannun kuma tana ɗan bubbugar ta da sigar rarrashi.

“Maryam don Allah ki sanyaya zuciyarki, ki nutsu ki yi nazari, dukkan abin da Turaki ya faɗa miki gaskiya ce ya faɗa, a rayuwa mutum ba shi da wani abu da ya ɗarawa iyaye, shi ya sa wanda ba shi da su yake kuka don ya rasa bangon jigina… ki saka wa zuciyarki salama, gobe da safe ki je ba wa Abbanku haƙuri, na tabbata zai yafe miki, kuma ba zai sauya daga yadda yake mu’amalantar ki kin ji.”

Ba ta amsa ba kamar yadda ba ta motsa ba. Umma ta miƙe, “Ki tashi ki cire kayan jikinki ki kwanta, ku tabbatar kun yi addu’a kuma.” Ta ƙare umarnin idonta a kan Zainab. Gyaɗa kai ta Zainab ta yi Umma ta fice zuwa ɗakin Abba don ta kwantar masa da hankali shi ma.

Bayan fitar Umma Zainab ta tashi ta gyara musu gadon bacci, ta sauya kaya ta hau gado ta kwanta ba tare da ta cewa Maryam ci-kanki ba, don tsoron ta take ji da gaske.

Har cikin ranta tana jin damuwa kan halayen ‘yar uwar tata, da tana da dama da ta sauya mata hali, sai dai ko kaɗan ma ɓa ta samun fuska a wajen Maryam ɗin tamkar ba ita ce gaba da ita ba, tamkar kuma ba tare aka shayar da su ba, tsakanin su sai magana da zafi-zafi daga Maryam ɗin.

Tana cikin wannan saƙe-saƙen bacci ɓarawo ya saɗaɗo ya saɗaɗa da ita gaba. Ba ta san tsawon lokacin da ta kwasa cikin baccin ba, Allah dai ya ba ta ikon farkawa, tana buɗe idanu caraf sai a kan Maryam wacce ta buɗe sif ɗin kayansu tana zaro kayanta tana cusawa a jaka.

Rass! Gabanta ya faɗi, ta zabura ta dafe ƙirji, sam ba ta san tana da ƙwarin gwiwa ba sai da ta tsinci kanta a gaban Maryam tana riƙe mata hannu.

“Maryam! Me kike shirin aikatawa ne haka?”
Ko kallo ba ta ishi Maryam ba, maimakon hakan hakan ma fizge hannunta ta yi ta cigaba da zaƙulo kaya tana cillawa a jaka.

Zainab ta yi caraf ta cukwikwiye jakar da Maryam ke cusa kaya, “Haba Maryam, yaushe zuciyarki ta zama shaiɗaniya? Yaushe kika sakacik da zuciyarki ta mamaye tunaninki? Yaushe huɗubar sheɗan ta gama narka miki zuciya? Ashe za a wayi gari Maryam a gan ki kina haɗa kaya za ki bar gida? To ina za ki je?” Ta soma hawaye.

Maryam takawar da kai. “Ki sakar min jaka idan har ba so kike in gilla miki rashin mutuncin da ba ki taɓa zato ba Zainab.”

“Ba zan saki ba Maryam! Na ce ba zan saki ba, idan zuciyar ba ta taɓa saƙa miki yin kisa ba to ta saƙa miki a yanzi ki kashe ni, amma na tabbatar miki ba zan bari ki je ko’ina ba.”

Takaici ya ƙume Maryam, ba ta so ta biye wa Zainab su yi jayayyar da za ta ka hankalin mutanen gidan su farka daga bacci, ita a yadda ta tsara tafiyar tata so ta yi a ce kawai an wayi gari an ga babu ita, ga shi Zainab na shirin kawo mata tasgaro, don haka ta haƙura ta sakar mata jakar tana ayyanawa cikin ranta ai akwai gobe, kuma kamar yau ce don haka ta watsar da kayan da ta nufi gado ta kwanta, ganin haka sai ita ma Zainab ɗin ta wuce ta kwanta.

Washegari da safe kafin su fita falo don karyawa, Maryam na zaune ta takure kanta, fuskarta ta ƙara hawa, idonta ɗaya ya yi taruwar jini da hakan ke alamta an same ta a idon yayin bugun ta da Abba ya yi.

A yadda take a zaunen ta yi jugum sai Zainab ta yi tunanin Maryam ta huce ta samu sanyin zuciya, kamar za ta saurare ta su yi magana don haka matsa sosai kusa da ita zuciyarta cike da fatan Maryam ɗin ta saurare ta, amna me? Wata uwar harara Maryam ɗin ta watso mata, ta maze ta basar, cikin taushi ta fara yi mata magana.

“’Yar uwata, Allah ya sani bana jin daɗin dukkan yadda abubuwan nan suke faruwa… da ace ina da yadda zan yi…”

“Dakata Malam! Ina so ki riƙe dukkan wani wa’azinki da faɗin gaskiyarki, akwai lokacin da za su yi miki amfani… in za ki kwana dubu kina maganganunki ba sauraren ki zan yi ba, waɗanda suka fi ki ma sun yi bai shiga kunnena ba balle ke… tafiya kuma babu fashi, zan bar gidan nan in tafi in za a karɓe ni da hannu bibiyu a girmama ra’ayina… Inda za a so ni a ƙaunace ni… dama duk wanda ya rasa uwa to rayuwarsa na cikin garari…”
Umma da ke tsaye a bakin ƙofar shigowa ɗakin ta yi saurin toshe bakinta da hannu biyu sakamakon kukan bazata da ya so ƙwace mata. Abin da take ta gudun faruwar sa yau ga shi ta ji da kunnuwanta dukkan abin da Maryam ɗin ta ce. Ta fasa shiga ɗakin ta juya ɗa sauri zuwa ɗakinya ta faɗa gado ta cigaba da zubar hawaye, ƙananun yaranta suka yi jugum-jugum suna kallonta…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 6Siddabaru 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.