Skip to content
Part 8 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Turaki ya shigo ya samu Umma jikinta duk a sanyaye, bayan sun gaisa ya ke tuntuɓar ta maganar Maryam, “Ko ta je ta ba wa Abba haƙuri?”

Mirgina kai Umma ta yi cikin damuwa tare da fidda zazzafan hucin da ta ke saka ran fitar sa zai sanyaya mata ruhinta. “Turaki lamarin yarinyar nan yanzu tsoro ya ke ba ni… duk yadda kake zaton ta ta wuce nan… ba don Allah ya taƙaita lamarin ba ya nufa Zainab ta farka daga bacci da sai dai mu wayi gari mu shafa mu ga babu ita…”
Turaki ya zazzaro ido cikin kiɗima, duk taurin zuciyar Maryam bai taɓa tsammanin za ta iya ayyana guduwa ta bar gida ba, ya dinga jijjiga kai kamar mai karɓar rantsuwa gaban alƙali.

“Kin sanar da Abba ne?”

“Ban sanar da shi ba, ina shakkar abik da sanar da shi ɗin zai haifar…”

“Ɗole ya sani ai Umma, gwara ya sani sai a san matakin da za a ɗauka.”

Ya miƙe cikin ƙunar zuciya ya nufi ɗakinsu. Kwance ya same ta ringingine tana waya.

“… ban ce ba ni, ban kuma ba ka damar hakan ba, idan kuma ka zaƙe da yawa zan fito maka a Maryam ɗita wallahi AbdulNasir…”

Ta yi tsaki ta kashe wayar ta yasar gefe, juyawar da za ta yi ta ga mutum tsaye turus, ko ɗar ba ta ji a ranta ba ta baza masa idanu duk da jikinta ya ba ta babban dalili kawai ke kawo Ya Turaki ɗakinsu, don haka ta san maganar jiya ce dai ba ta mutu ba.

Duk da ran Turaki a ɓace yake matuƙa, sai dai bai gaza ba wajen ganin ya tausasa harshe ya ce. “Maryam tashi mu yi magana.”

Ba ta ja ba ta yunƙura ta tashi zaune, ɗankwalinta da ya faɗi ta ɗauko ta rufa a kanta sannan ta tattara hankalinta gare shi.

“So na ke in ji mene ne abin da kike buƙata a rayuwarki ne Maryam.”

Ta yi shiru kamar ba za ta yi magana ba har sai da ya ɗan kaurara harshe ya ce. “Ba ki ji ni ba ne Maryam?”

Ta motsa baki da ƙyar. “Na ji, ina shirin magana ne.”

“Tom ina sauraren ki.”

“Karatu na ke so na yi Yaya.”

Ya ɗan yi jimm a zaton sa zaren maganar tata zai yi tsayi, da ya ga iyakar abin da za ta ce kenan sai ya ƙara mata matashiya.

“Kina son yin karatu amma ba kyau son aure?”
“Ba aure ne ba na so ba Yaya, taura biyu ce ba na son taunawa lokaci ɗaya.”

“Ta yaya aure da karatu suka zama taura biyun da ba za su iya taunuwa lokaci guda ba?”

Ta yi shiru ba don ba ta da amsar bayarwa ba, sai don tana ganin amsar tata na iya yi masa zafi kamar yadda Abba ya ji a jiya.

“Kodayake ‘yar uwarki Zainab ita ba damuwa ta yi da zurfafa karatunta ba amma Hafiz ya ba ta damar cigaba da karatunta in har tana sha’awa bayan aurensu, hakan nan a nawa ɓangaren ni tuni na yarje wa Khalisat cigaba da karatunta bayan aurenmu tun da tana da ra’ayi… ke me ya sa ba zi ki yi haka ba?”

Ta gyara zama sosai. “Yaya ko ko jiya ma abin da na faɗa wa Abba shi ne ni ba zan iya haɗa karatu da aure ba.. Sai na yi karatuna na kammala na kai matsayin da na ke son kai wa sannan zan waiwayi maganar aure.”

Ya jima yana shan maɗaci a ransa, da ƙyar yake haɗiye yawun takaici, ba don yana ta ƙarfin halin danne zuciyarsa da ke hanƙoro ba da tuni ya wawwanke mata fuska da zafafan mari.

“Har yanzu ban ji wani ƙwaƙƙwaran dalili da zai saka a yarda kina da hujjar ƙin aure ba a maganganunki… abin da na fuskanya kawai kin shirya bijirewa umarnin magabantanki ne saboda wani gurɓataccen ƙudiri naki… to ki sani, ni dai ba ni da ikon tilasta Abba yin abin da bai yi niyya ba, abin da kawai zan iya yi shi ne nema miki alfarma, idan ya amince shikenan, idan ko bai amince ba to shawara ta rage ga mai shiga rijiya…”

Ya miƙe ya fice ranshi a matuƙar ɓace, ita kuwa gogar juyawa ta yi ta yi kwanciyar ta, hawaye ke son zubo mata tana kora su, ba ta son zuciyarta ta karye, ba ta so duk rintsi burinta ya rushe… sai dai Allah ya haɗa ta da mutane masu tsananin son zuciya a ganin ta, masu son kansu, waɗanda ba su damu da damuwar makusantansu ba, ba sa girmama ra’ayoyin ‘ya’yayensu… Ba sa ciccuɓa yaransu su kai matakan da suke burin takawa… idan ‘ya’yan suka jajirce kan ra’ayinsu a ce sun bijire… to ita ko me za a ce ta yi, ko wane irin hukunci za a yi mata a shirye ta ke da karɓar sa duk tsananun muddin dai za ta kai ga cim ma burinta!

*****

A daren ranar Turaki da Zainab suka sami Abban a ɗakinsa kamar yadda suka tsara za su je su same shi su ba shi baki ko zai amince ya ba wa Maryam dama ta yi abin da ranta yake so, ita Zainab ɗin sai a yi mata auren ta, amma me?
Abba ya shayar da su gubar mamaki, domin kuwa runtse idanunsa ya yi ya balbale su da faɗa kamar ya ari baki, tamkar dai su suka kashe zomon… Ya rantse ya kuma rantsewa muddin Maryam ba za ta bi umarninshi ba to sai ta bar masa gida, ya yafe ta cikin ‘ya’yansa…
Suka yi cirko-cirko cikin tashin hankali, ba su san haka lamarin zai tsamama ba da ba su biyo ta wannan sigar ba… ga shi sun ɓata goma ba su gyara biyar ba.

Abba ya miƙe a fusace zuwa ɗakinsu Maryam, ya balbale ta da faɗa, ta inda ya shiga b ta nan ya ke fita ba… ya ce tattara kayanta ta bar masa gida in dai ba ta sauka daga dokin na ƙi ba da ta hau.
Umma ta taho cikin kuka tana ba shi haƙuri amma ya daka mata tsawa ya ce ko tak! kar ta sake ta furta… Maryam dai ‘yarshi ce ba ‘yarta ba don haka ba ta da hurumi cikin lamarin.
Umma ta shiga tashin hankalin da ba ta taɓa shiga ba a rayuwarta, yau ita Abba ke wa gorin ba ita ta haifi Maryam ba, wato ya manta cewa haifar ta ne kawai ba ta yi ba amma dukkan wani abu na uwa ta yi mata shi… ta rushe da kuka.
Hankalin gidan ya tashi gaba ɗaya, yara na kuka manya na kuka. Turaki ya ɗauki wayarsa ya kira Babansu Isah ya sanar masa da abin da ke faruwa.

Dayake Alhaji Tukur bai san komai ba kan wannan balahirar sai abin ya shayar da shi mamaki, ya dinga jinjina maganar korar Maryam da Abba ya yi.

“Shi yanzu Ahmad ɗin ne ya kori Maryam? Na rasa wannan zazzafar zuciya irin ta Amadu wallahi… kana ji na ko Turaki?”

“Ina jin ka Baba.”

“To ka yi duk yadda za ka yi kar ka bari Maryam ta bar gidan har sai na zo… ga ni nan zuwa.”

Ya kashe wayar cikin jimami, dayake suna tare sa Isah a lokacin suna tattaunawa kan maganar kasuwa wannan lamari ya kutso, Isah kuma ya ji komai don haka hankalinshi ya tashi, nan ya ce zai bi Baban su tafi tare.

Sun fito za su tafi Mamansu Isha ke tambaya, “Ina za ku je haka ake ta gaggawar tafiya?”
Baba ne ya amsa. “Gidan Amadu za mu je.”

“Lafiya dai ko?” ta yi saurin tambaya idonta a kan Isah da ke ta alla-alla su fita.

“Lafiya lau.” Baba ya amsa a gajarce sannan ya yi musu sallama ya juya zai tafi.

Mama ta zabura “Amm Kai Khalifa magana fa na ke so mu yi da kai.”

Isah ya ɓata fuska, ya kau da kai, Allah ya taimake shi Baba ya saka baki.

“Abin da zai fitar da mu ma mai muhimmanci ne… kai mu je.”

Tuni Isah ya yi zaraf ya fice ya bar Mama da ƙunci a zuciya. Har ga Allah ta tsani sabgogin da suka shafi gidan Alhaji Ahmad musamman saboda Maryam, ta san kuma duk wannan rawar ƙafar da Isah ke yi na zumuɗin haɗuwa da ita ne, a fili ta saki dogon tsaki wanda ya sa kowa a falon watso mata idanu, ta sha kunu ta kawar da kai.

Sun isa gidan sun tarar da Abba na cilli da kayan Maryam, ita ma ƙoƙarin hankaɗa ta yake waje, tana fita zai mayar da ƙofar ya kulle. Ɗaiɗaikun mutane na tsaitsaye a gefe suna ganin abin kamar a wasan kwaikwayo. Tun Isah bai gama gyara tsayuwar motar ba ya kashe ta ya fito, shi ma Baban ya fito cikin hanzari yana faɗin “Subhanallahi! Subhanallahi, Isah lafiyarka kuwa…? Me ye haka kake aikatawa?”

Abin mamaki sai ga hawaye a idanun Abba, ya soma kuka yana faɗin.

“Na gaji da halin yarinyar nan yaya, wallahi na gaji, saboda na ce dole tare zan haɗa na aurar da su da ‘yar uwarta shi ne yarinyar take neman kashe ni da baƙin ciki… har an kai jallin da yainyar nan za ta haɗa kaya ta ce za ta bar gida..?”

“Ya isa haka Amadu, mu je ciki mu yi magana.”
“Kafin mu shiga daga ciki ta fara fice min a gida, na rantse na kuma rantsewa yau sai ta bar min gida, kuma wallahi ba zan yi kaffara ba!”

“Assha! Ahmadu ban so haka ba sam wallahi… amma duk da haka ina mai ba ka haƙuri ka rabu da ita mu shiga mu yi magana sai a san yadda za a ɓullowa lamarin.”

Ba dom ranshi ya so ba ya juya zuwa cikin gidan, yayinda shi ka Baba ya tasa Maryam zuwa cikin gidan, Zainab da sauran ƙannensu ke ƙoƙarin tattare kayan da Abban ya yi watsi da su.

Isah ko jikinshi rawa yake tamkar wanda kiɗan gangani ke ratsawa… addu’a yake a ransa Allah ya sa wannan taƙaddama ta zama silar da za a ce za a ɗaura musu koda nan take ne, in yaso daga baya a yi komai… ya shafe hannayensa a fuska sannan ya shiga cikin gidan.

Ya sha mamakin yadda ya tarar da Turaki a zaune ya yi jugum tamkar wanda saƙon mutuwa ya riska, ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan ya ka shi gefe don ya ji yadda kan zancen yake.
Turaki ya kwashe komai ya faɗa masa, hankalin Isah in ya yi dubu ya tashi, bai san lokacin da ya zabura ya yi wuf ya faɗa ɗakin Abban ba in da ya tarar da abin da ya ƙara girgiza zuciyarsa… wato yau Maryam ya gani tana kuka da idanunta… fuskar Abba da Baba duka babu mai annuri a ciki… abin da kunnuwansa suka jiye mashi Maryam na faɗi cikin kuka shi ne.

“…Ku yi haƙuri Baba… duk yadda na so sarrafa zuciyata hakan ya gagara… wallahi ko an yi min auren hankalina ba zai taɓa kwanciya ba… shi ma wanda aka aura wa ni ɗin nashi ba zai kwanta ba… amma na yi alƙawari da zarar na kammala karatun zan yi aure…”

Abba ya yunƙuro zai kawo mata mangari, da sauri Baba ya dafe shi.

A’a Amadu! Kar ka dake ta, magana kuma in sha Allahu ta zo ƙarshe… ba zan sa ka yin kaffara dole a kan rantsuwar da ka yi ba, saboda haka zan tafi da Maryam ta zauna a gidana zan nema mata jami’a ta je ta yi karatun in ta gama sai ta yi auren tun da haka take da buri…”

Nan take sai ga Maryam na dariyar farin ciki, ta rarrafa ta isa gaban Baba ta sunkuya kanta a kan ƙafarshi tana zuba godiya.

“Na gode Baba! Na gode, ban taɓa jin farin ciki irin nan wannan rana ba… wallahi Baba ka wanke min komai na zuciyata… ashe mafarkina zai tabbata? Ashe burina zai cika haka? Kaiii na gode Baba Na gode, na yi alkawari ba zan ba ka kunya ba…”

Isah sa ke tsaye ƙiƙam kamar gunki, abubuwa biyu ne ke yawo a ransa, na farko farin cikin yadda Maryam za ta ƙara kusanta ga rsyuwarsa, yana tunanin hakan zai ba shi damae sauya mata ra’ayi da salon soyayyarsa mai cike da sadaukarwa… Abu na biyu kuma zullumin jin maganarta ta ƙin yin aure har sai ta kammala makaranta… ga shi kuma Baba ya yi ammana kan hakan. Kenan hakan na nufin zai ta zaman jiran ta har sai ta je ta gama jami’a ta dawo?

In don ta shi ne, ko shekaru dubu za ta yi zai iya jiran ta, matsalar daga iyayensa ne, idan shi ya kwankwaɗi giyar soyayya ta saka shi hauka to su cikin hankalinsu suke, ba za su taɓa yarda da shashancin zaman jira ba, dole a tilasta masa yin aure! Ya zai yi da rayuwarsa kuwa in hakan ce za ta faru?

*****

Baba ya tafi da Maryam, Umma da Zainab da sauran yaran gida kuka suke kamar ransu zai fice, gani suke kamar Maryam ta bar rayuwarsu kenan har abada, yayinda shi kuma Abba baƙin ciki da takaici ba su bar shi ya leƙo ya ga tafiyarsu ba.
Isah ke tuƙa motar amma gaba ɗaya hankalinsa na kan Maryam wacce musamman ya saita mirron tsakiyar mota saitin ta, duk da akwai duhun dare amma hasken cikin motar ya wadatu yadda yana iya hango ta. Baba kuwa nasiha yake yi mata sosai, nasiha mai ratsa jiki kan kuskuren da ta ke tafkawa na bijirewa iyaye yake yi mata, kamar dai nasihar na wucewa zuwa zuciyarta daga kunnuwanta, kanta a sunkuye yake ita kaɗai ta san abin da take saƙawa a ranta.

Isar su gida Isah ya fara kinkimar kayanta yana shigarwa da shi cikin gidan, Mama idanu ta baza gabanta na faɗuwa kaɗan-kaɗan. Sai da ya kammala shigar da kayan sannan duka ɗunguna gaba ɗaya zuwa cikin gidan.

Mama ta zabura ta miƙe a gigice tana dafe ƙirji. “Na shiga uku me zan gani haka?”

Kowa ya zubo mata idanu cikin neman dalilin gigicewar ta.

Baba ya dubi Umma Fatima.

“Fatima ga Maryam nan za ta zauna a nan kafin wani lokaci.”

Cikin biyayya ta ce, “To Alhaji, Allah ya taimaka.” Ya amsa da amin ya wuce ɗakinsa.

Takaici kamar zai sanya Mama haɗiyar zuciya, wato don tsabar son tura takaici irin na Alhaji ita ba ta isa ya ba da amanar Maryan gare ta ba duk da ita ce babba? Kodayake ta san ya san yadda kanwa ba ta jiƙuwa tsakaninsu tabbas ba zai kawo ta gurinta ba, don kuwa kwaɓar jiƙewa za ta yi har sai ta yi ruwa, idan ma wani abu aka guda aka dawi da ita gidan to tabbas za a yi ƙarkon kifi, a fito daga ruwa a faɗa wuta!

Duk yadda ta so ta ji kan zance a bakin Isah ya ƙi ba ta haɗin kai, ƙarshe ma sallama ya yi mata ya fice ya nufi ɗakinsa.

Washe gari da safe aka yi kiciɓus a falo tsakanin Mama da Maryam, Mama ta ɗaure fuska, ciki-ciki ta amsa gaisuwar Maryam ta kawar da kai ta nufi kicin.

Maryam ta taɓe baki ita ma ta bi bayan Mama da wulaƙantancen kallo, ɗakin Baba ta nufa ta gaishe shi sannan ta dawo falo ta miƙe a doguwar kujera hannunta riƙe da wayarta.
Kira ya shigo mata, AbdulNasir ne, ta ja dogon tsaki ta ƙi ɗaga kiran har ya katse, wani kiran ya sake shigowa ta ƙi ɗagawa, daidai lokacin Umma Fatima ta fito daga nata ɗakin. “Maryam ba wayarki ake kira ba ne?”
“Ita ce Umma, kiran ba mai muhimmanci ba ne shi ya sa ba zan ɗaga ba.”

Umma Fatima ba ta ja maganar da tsayi ba ta wuce.

Isah ya yi sallama ya shigo, fes ya ke ya cakare cikin jigar tsadajjiyar shadda sai zuba ƙamshi yake.

Maryam ta lumshe idanu, ƙamshin ya yi mata daɗi a hanci kamar yadda mamallakin ƙamshin ya yi mata kyau a idanu. Kai ma sha Allah! Shi ma fa Isah babu laifi, ko AbdulNasir da yake ji tashen kuɗi ba zai nuna masa iya gayi d gogewar rayuwa ba.

Tabbas da a ce a kan ƙadamin yin aure ta ke da ta shiga matuƙar ruɗani na rashin sanin wa za ta zaɓa a tsakanin su.

Fuskarsa a faɗaɗe ya ƙaraso gare ta ya tsaya a kanta.

“Marry, ke fa dama na san ki ba gwanar baccin safe ba ce…”

Ya haɗiye maganar sakamakon kiran da AbdulNasir ya ƙara yo mata, kuma karaf idanunshi a kan sunan.

A fili furta “AbdulNasir!”

Ya ƙara da tambaya. “Waye shi haka?”

Tashi ta yi zaune fuskarta ƙunshe da murmushin mugunta.

“Akwai wani sharaɗi ne a tsakanin mu na cewar ba ni da damar ajiye lambar wani a wayata?”

Zuciyarshi ta sosu. “Maryam me ya sa kullum burinki ki ga kin jigata min zuciya? Me ya sa ba za ki killa ce min zuciyarki ni kaɗai ba?”

“To tabbatace marar kunya! Allah ya yi dare gari waye ko? Dama saboda haka ka ke ka ɗauko ta daga gidansu ka kawo ta nan don ka ji daɗin nuna tantirancinka ko? To wuce mu je ina son magana da kai.” Mama kenan, bayan ta fito daga kicin ta tarar da shi yana furta waɗancan kalamai.

Ji ya yi tamkar ya nutse ƙasa, har ga Allah Mama ba ta kyauta masa, kwata-kwata ba ta kawaici a kanshi duk da kasancewar ɗanta na fari… shi bai san me ya sa Mama ta ƙi jinin Maryam ba sam, ta bi ta mayar da ƙanƙanuwar yarinya abokiyar gabatarta.

Yana tafiya yana waigen Maryam da ta haɗa rai har ya shige ɗakin Mama, ta mayar da ƙofa ta rufe. Faɗa ya hau yi masa ba ji ba gani kan rawar ƙafar da yake nuna a kan Maryam, ta tabbatar masa da kar ma ya taɓa sakawa a ranshi cewa zai auri Maryam don ita sam ba za ta haɗa zuriyya da mai hurɓataccen hali ba. Ta ƙaraci faɗanta bai ce mata uffan ba har ta gaji ta sallame shi a kan sharaɗi mafi tsauri da ta gindaya masa na sam ba ta amince masa ya sake kula Maryam a gidan ba har ta gama iya adadin zaman da za ta yi ta tafi!

Da yamma kuma sai ga AbdulNasir a gigice ya zo gidan tare da Mabarak autan su Maryam da ya rako shi.

Ya saka Maryam a gaba kamar zai saka mata kuka.

“Sweety hankalina ya tashi da jin cewa kin bar gida, haba! Me ya sa za ki yi min haka?”

“Dole ce ta sa hakan, nan gaba kaɗan ganina ma wahala zai yi maka!”

Ya zaro ido “Sabod me?”

Ba ta iya amsawa ba saboda shigowar Isah, ya watso musu wani irin kallo, haka nan ran shi ya ba shi wannan shi ne AbdulNasir abokin takarar shi. Ranshi ya ɓaci, ya jefa wa AbdulNasir mugun kallo sannan ya wuce ciki, ba don sharaɗin Mama da a yanzu zai fatattaki AbdulNasir ɗin.

“Shi kuma wancan waye? Sam ban gamsu da irin kallon da yake mana ba!”

Ta yi murmushi da ya bayyan tsurar kyawunta.
“Hmm! Yayana ne kuma masoyina?”

“What?” Cikin ɗimuwa.

“Tabbas abin da ka ji na faɗa, yadda kullum kake maimaita mini kalmar so haka shi ma yake yi mini.”

“Me ya sa haka Sweety?”

“Da aka yi me kenan?” Tana kallon shi a kaikaice.
“Me ya sa kike tunanin raba zuciyarki ga mutum biyu?”

“Me ya sa na kasa hana zuciyoyinku sona?”

Ya yi shiru, ta ɗan yi ƙaramar dariya. “Kamar yadda ban isa hana zuciyoyinku kamuwa da sona ba haka ban isa in ce duk ba zan so ku ba… so kawai ka ɗauƙa me rabu shi zai ɗauko allura cikin ruwa….”

*****

Abubuwa da yawa sun faffaru biyo bayan haka, tun daga kan yadda Isah ya dage wajen jadadda wa Maryam irin ƙoluƙuwar matsayin da ta kai a zuciyarshi kamar yadda shi ma AbdulNasir ya buɗe nashi ƙwanjin yana ganin yana da zarrar da zai iya mallakar Maryam ko ta halin ƙaƙa.

A hannu ɗaya kuma lamari ya ƙara dagulewa tsakanin Mama da Maryam, kullum Mama cikin nuna mata ƙiyayya take, yayin da ita kuma Maryam a ɓangaren ta tana ɗaga mata ƙafa ne don darajar Baba da Ya Khalifa.

Gefe guda kuma Baba na cigaba da ƙoƙarin ganin Abbansu Maryam ya haƙura ya yafe mata ta koma gida, sai dsi ina Abban ya hau doron zuciya sosai, saukowar shi ba yanzu ba!

Shirye-shiryen bikin Zainab da Turaki sun kan kama, Abba so ya yi a ce Isah ma ya haƙura ya nemo wata an haɗa an yi bikin tare amma y kafe kan cewa a ƙara ba shi dama zai shawo kan Maryam duk kuwa da irin tasgaron da yake fuskanta daga Mama.

Sosai Umma da Zainab ke zuwa gidan akai-akai don su ga Maryam, musamman yanzu da biki y matso gab, Zainab ba ta da babbar ƙawa sai Maryam, don haka ita aka lallaɓa ta yi uwa da makarɓiya a bikin har aka ci aka cinye. Sai dai har lokacin Abba bai ba ta damar dawowa gidansa ba duk ya ɗan sakko musamman albarkacin biki.

Bayan biki da kaɗan Baba ya samu damar sama wa Maryam admission a jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi kasancewar dama ta zana jarabawar shiha jami’a, don haka sai shirye-shiryen tafiya ta ke…

Tana ta shirye-shiryenta ba tare d sanin cewa ƙoƙari take matuƙa wajen buɗewa kanta ƙofar gagarumar ƙaddarar da za ta gigita rayuwarta har ma da waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, Jami’a da take kalla a matsayin wani ginannen tubali na cimma dukkan muradanta ba tare da sanin ta ba ashe tubali ne na ginuwar baƙin ciki, tashin hankali da ɗimauta a rayuwarta ba…
Mu bi ta Jami’ar mu ga me zai faru?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 7Siddabaru 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.