Waiwaye Adon Tafiya
Domin tafiyar ta yi kyau, bari mu adonta ta da waiwayen bayan rayuwar Maryam mu ga me ya faru a jiyan rayuwarta? A wane yanayi yau ɗinta take ciki?
Maryam Ahmad Isah, shi ne sunanta cikakke na yanka, alaƙar da ke tsakanin su da Isah Tukur Isah (Khalifa) alaƙa ce makusanciya, wadda a Hausance ake cewa ‘yanmaza zar suke.
Alhaji Tukur Isah tare da ƙaninsa Alhaji Ahmad Isah, yadda suke su biyu jal kamar idanu su kenan nasu iyayen suka mallaka. Iyayensu ba su kasance mawadata ba sai dai rufin asiri da watar. . .