A tsari irin na hallitar wani kaso na daga cikin mutane, mace ko namiji, a duk lokacin da aka ce shekarun girma sun fara cim ma sa/ ma ta, sukan tsiro da wasu ɗabi’u marasa kyau, kamar zafin rai, saurin fushu da ganin kai ɗaya suke da kowa, da jin ƙwanjinsu ya yi ƙoshin da za su iya karon-batta da kona waye, don haka sai tsoro ya disashe a zuciyarsu, kafiya da taurin kai su samu wurin zama.
A irin wannan ƙadamin ne idan yaro bai samu kyakkyawar tarbiyya da ingantacciyar addu’a daga iyaye ba sai ka. . .