Skip to content

Siradin Rayuwa 2 | Babi Na Sha Daya

3.6
(26)

<< Previous

Su Goggo Jummai basu tafi a ranar ba sai washegari Laraba, Baffa yace Intisar ta shirya su tafi tare ta karbowa Daddy rubutun da za’a fara yi mai na tsarin jiki duk sati, in yaso sai su dawo ita da direban da zai kai su. Suna ta jiran Ado da ya tafi cefane har shabiyun rana bai dawo ba sai Daddyn ya kira Faisal yace ya je ya kai su.

Ko kadan ranta bai so tafiyar nan da Faisal ba, ita yazu ko hanya bata so ta hada su sabida haushin sa da ta ke ji akan budurwar sa, har Addu’a take garin Allah yayi ya sake wayewa ya koma inda ya fito.

A motar Hajiya (bolbos6) aka yi tafiyar, Baffa da Goggo na gidan baya suna  taunar goron su  suna  hirarrakin su tamkar wasu yara sabbin aure ga sanyin A/C na ratsa su, Goggo har da su aje mayafi a gefe da ganin su dai kinga ‘yan gatan tsoffin da ‘ya’ya suka hucewa takaicin duniya, jikokin su Faisal da Intisar  na gaba.

A yau dressin din sa (bery-simple)  wato sanye yake da  caftan na shudiyar shadda  ‘yar mali  kalar ta kama sosai (dark-blue) kansa ba hula, silipas ne ‘chips’ a kafar sa yana murza sitiyari cikin gwaninta, kamar kullum parmanent (tabbataccen) kamshin sa na (5,000 Doller Perfum) ya na tashi a hankali cikin motar cooly, wannan kamshin dake sa mutum gyangyadin da bai shirya ba.

Ita ko ‘yar lelen gidan Makarfin sanye take da kamfala shadda ghanilla baka da aka yiwa dinki senegalese, maimakon dankwalin kayan ta yi amfani ne da  siririn farin mayafi da yake dinkin babba ne sosai, baka ganin komi nata sai shacin kayatacciyar fuskarta  dake manne da farin (medicated-glass) dinta sai ko santala-santalan yatsun hannunta farare sol kaman ka taba jini yayi tsartuwa data kawata da zobba na farin zinare wato (white-gold) kwaya biyu rak, ba abinda ke tashi jikin ta face sassanyan kamshin turare ‘zandaria’ bakin ta cike da chingum mai tsananin kamshi (hubba-bubba) tana tauna (bery-gently). Daga ita har Faisal kowanne shan kamshi yake wa dan uwan kaman bai taba sanin sa ba dadai duniya.

A haka yake (speading)  har suka fice jihar Neja ba wanda yace da dan uwan sa uffan, ya mika hannu ya karo karfin na’urar sanyaya mota  domin Faisal Allah  ya halicce shi mutum ne mai son ya ji shi jike cikin raba, ko kadan bai son zafi don haka fatar shi har wani santsi take irin na mazauna kasar sanyi nan ko tsabar hutu ne kawai, ya danna kaset na wakar Sani Aliyu ta (Shehu Kangiwa Jagoran Jihar Sokoto) yana kada kai cikin nishadi, yana rangaji da dogon wuyan shi yana buga sitiyarin da hannun shi daya, dayan ko yana cigaba da tukin sa hankali kwance yana bin wakar da ‘rhythm’ din da mawakin yayi amfani sak.

Inteesar ta kama  kanta da hannu bibbiyu, tuni kan ta ya soma sarawa, ta tsani ‘melody’ na wannan wakar domin ciwon kai yake haifar mata ba tun yau ba, ta sha gayawa Faisal duk cikin kasusuwansa ba wanda ta tsana irin wannan kaset din, tun kuma daga ranar bai kara sawa ba, to yau ko don yana jin haushin ta ne? Oho! Sai ta kwantar da kanta cikin cinyoyin ta tayi shiru, kanta na cigaba da sarawa.

Sun yi nisa sosai kuma ya gyara murya ya kure sautin sosai ta yadda su Goggo da ke baya ba zasu iya jin me yake cewa ba yace

“wayyo Ronke, nayi missing dinki amma ‘by the way, gobe I’yanzu da yardan Allah ina Ilorin”  tayi tsaki baya ga wani tukuki daya zo ya tokareta a kahon zucci, ashe ma kabila ce Yayan da bata hada shi da kowa a duniya zai auro masu?

Tuni idanin ta suka cicciko da kwalla, ta dago ta dubeshi da wutsiyar ido kana ta maida duban ta a tsirrai dake tsere a gefen titi tace.

“Ai sai ka aje mu, ka koma can garin naku wajen Rakiyar tunda kuwa kuna wanka tare ba dole kayi kewar ta ba?”

Yayi dariya sosai sabida Rakiyar da tace ya bala’in bashi dariya yace “ke Sis wanka da Ronke shine ya dameki, ni ko kyakkyawar fuskar ta nake kewa, da kissable-lips dinta, gata da iya dressing dan kuwa shigarta tana burgeni” ta kuwa shaka, ta kule ta haye suntum, fiye da tsammanin sa ko numfashi da kyar take furzarwa, wai a gaban ta? Ya Faisal ke baro wannan kazamar magana? Amma Allah wadaran wannan Ronke data gurbata mata tarbiyyar dan’uwa.

Shi ko Faisal ko a jikin sa, har wani lumlum yake da ido wai yana tunanin Ronke.

Basu bata lokaci ba a Makarfi suka karbi sakon su suka fito  sai ta bude kofar baya ta kame abinta  domin bata son kuma jin zancen wofinnan na Ronke. Faisal ko ya kudure zancen Ronke yanzu ya fara, ya kai hannu ya shafi kyakkyawan saisayen kanshi zuwa dokin wuyanshi, ya dubeta idanuwan shi sunyi kasa sosai kaman suna neman rufewa don kansu yace “nayi maki kama da Ado direba ne?

Allah ko Ronke dana ke mutuwar so bata isa ta kame a ‘owner-side’ in tukata ba, Allah  wallahi kuwa baki isa ba don haka cikin biyu dole zaki zabi daya.

Ko dai ki koma gidan tsoffin da kika fito, ko kuma ki komo mazaunin mai zaman banza don kowa ya ganki ya san zaman banza kike” sai ta gyada kai kamar kadangaruwa, zuciyar nan ba sai an tona ba don takaici, ta fito ta banka kofa ta fada gidan.

Goggo na sharar tsakar gidan da yayi kura futuk sabida kwankin da sukai basa nan ta ganta ta jawo kujera ‘yar tsugune ta zauna daga can gefe tana cika tana batsewa, kiris take jira ta fashe tace “ke lafiya? Me kuke jira tun dazun baku tafi ba, anya ‘ya’yan nan kuna jiyewa kanku tafiyar daren nan da ake jiye maku?”

Tace “a’ah Goggo ba laifina bane, Ya Faisal ne yace in dawo a bani kudin mota in je ni tasha in shiga motar kasuwa” Goggo ta ce “akan wane dalili? Ki ga mun dan nema, bari inje In tadda shi” taja mayafin ta data rataye a jikin kyaure ko tsayawa yafawa bata yi ba tayi waje.

Kafar sa daya cikin motar daya a waje yana bin wakar Hassan Sarkin Dogarai ta Dacta Mamman Shata, don shi Faisal wadannan wakokin namu na gargajiya sune (hobby) din shi, ya kan ce yakan tsinci kansa cikin nishadi a duk lokacinda yake sauraron su, musamman cikin halin kunci, damuwa, confusion, ko a yayin da ya rasa sanin hakikanin abinda ke damun zuciyar sa.

Goggo ta tsaya a kan shi na ‘yan dakiku ba tare da ya sani ba, ta nazarci abubuwa masu dama a tare da shi cikin ‘yan dakikai, sai ta koma lallashi tamkar mai magana da yaro karami ta ce

“wane irin neman magane ne wannan Faisal, wai maiyasa kuke hakane kai da ‘yar kanwallen kuma ai sai kowa yayi maku dariya, na dauka tun jiya zancen ya mutu? Ban san ka da riko maras dalili ba.” 

Ya rage sautin radiyon yace “sai ki tambayeta dalilin ta na kamewa a baya in tukata, an ce da ita ni direban gidan su ne?”

Goggo Jummai tayi dariya irin tasu ta manya, amma zuciyar ta tayi nauyi, har yaushe zasu dauwama suna boyewa jinin su da sauran jama’ar dake tare da su wannan boyayyen sirri, musamman yanzun data fahimci yana neman zama cutuwa ko kwara ga Faisal da ita kanta Intissar? Har yaushe za’a dauwama a hakan? Ko makaho ya shafa idanun su zai bada tabbacin soyayya suke su kan su basu sani ba.

Ita kam tana ganin da Bello yayi tunani da bai dauki matakin boye wannan al’amari ga kowa ba tunda ko watarana, Saratu za tayi aure, zancen duniya baya taba boyuwa koda kuwa a karkashin gado aka sanya shi.

Auren daya cikin ‘ya’yan shi shine gata na karshe da zai yiwa rayuwar yarinyar in har kaunar da yake ikirarin yi mata ta gaskiya ce.

Su kadai suka san asalin ta suka san ciwon ta duk tabon dake jikin ta baza su taba kin ta ba, to boyon na mene ne? Idan babu wannan akwai mutuwa, zai iya mutuwa a sanda komi zai bayyana garesu suzo suna cewa ashe da bai mutu ba da bazasu sani ba ina amfanin haka?

Ita kadai take tunanin ta, tama mance a inda take tsaye, da wadanda take tare da su, duk suka dubeta, kamin Intisar din ta kai hannu ta bude murfin kofar bayan motar, karar kofar ne ya maido ta hankalin ta ta dubeta tace “a’ah, shiga gaban ku tafi” ta dubi Faisal tayi murmushi tace

“Da abokan wasa kuke sai ince son junan ku kuke, amma duk wannan ce-ce-ku-ce banga dalilin sa ba, sai aka ce wani abu zai ragu a jikin ka don Saratu ta zauna a bayan mota ka tukata?”

Yayi saurin cewa “Allah Ya so ba su din bane, ko su din ne Allah Goggo ban ga me zan ci da wannan kodaddiyar yarinyar ba”.

Intisar ta kai hannu a hankali ta shafo dogon karan hancin ta, ta kare masa kallo tsaf cikin ‘yan dakiku, ta so ace akwai makusa tattare da Faisal a yau ta rama wannan cin fuskar amma BABU! Komai nasa yayi masa dai-dai ya kuma dace da yadda Ubangijin halitta ya tsara mishi abinshi kai kace shi ya zabawa kansa, tako’ina, Faisal Bello bai da makusa.

Ita ko tasan fara ce jazur, kenan farin ta yayi yawa har ta kode? Wasu kwalla suka zubo sharr, tayi saurin sharewa da bayan hannun ta.

Goggo ta rasa ma abinda zata ce tace “oh ni Jummai! Allah kayi mun maganin abinda yafi karfina, ka iya min abinda bazan iya ba, nace shiga gaban ku tafi Saratu jayayya ba ta da amfani, Allah ya kiyaye hanya”.

*****

Tafe suke tamkar tafiyar kurame, to ba wanda yace da dan uwan sa ci kanka, har suka fita shiyyar Kaduna  kwata-kwata, yace a ransa bari dai ya kara tsokanota. Ya dibi yanayin ta kana ya maida hankalin sa a titi yace,

“kin san meye ne baby? Abinda ke kara sawa in so Ronke, shine murmushin ta, tamkar na ‘yammatan hurul-eeni yake, tafiyar ta ko kin san catwalk to haka take. Idan tayi dariya jerarrun hakoran ta masu haske kamar kankara na sawa in mance da kowacce ‘ya mace a duniya, muryar ta tamkar sarewa na kwantar da hankalina.

Tana kishina kamar mijin ta, ranar da kika yo mun waya kwana tayi tana kuka. Idan ta rungume ni Intissar mancewa nake da kyawun kowacce diya mace a duniya sai ita Ronke Adeyemi Olayemi…”

Sai a lokacin ya lura Saratu kuka take haikan, kuka take tun karfin ta baka da zuci. Zuciyar sa ta tsinke hadi da wani mummunan faduwar gaba da ya sameshi duka a lokaci daya, komi ya tsaya mishi cik. 

Duk wani haushin ta da yake ji sai ya kau, tausayin kansu ya maye tunani mafi rinjaye cikin zuciyar sa har bai san shi kansa Faisal yake tausayi ba ko ita Saratun?

Shi fa ba mahaukci bane, hakannan a shekarun sa, tunanin sa da matakin ilminsa, ya isa ya fahimci irin kaunar da sukewa juna daban take da wadda ‘yan uwan jini daya ke yiwa junan su. Kar dai ya kasance Allah ya jarrabcesu da son junan su alhalin suna uba daya? Mai yasa Ubangiji zai jarrabce su da wannan musiba? Yayi saurin jan istigfari ga sabon da zuciyarsa ta bijiro tare da kokarin kawar da wannn bahagon tunanin.

Idan yasan zuciyar sa, ya san abin da ke damun ransa, ya san nata ne?  Yanzu haka ma ita a binda ke damun ranta daban ne,. to in ba haka bane mai yasa suke kishin juna? Bai sani ba! Ba kuma ya son ya sanin, don sanin baya da amfani.

Idan kuma ya dage sai ya sanin ba abinda sakamkon binciken nasa zai haifar face (bakin-ciki) tunda ko ko a garin gaba-gaba ake ba za’a taba barinsu su auri juna ba, to suma suna hauka ne? Kai Allah ya sauwake su ce suna son junan su, yaya ma hakan zai taba kasancewa? Ba komi ke kimsa masu wannan halakar a zuci ba face Iblis dan lis, (diabolical feeling). Don haka ya rage gudun motar ya safka a titi yace da karfi “A’uzu billahi minash-shaitanir-rajeem!”

To bata zaci wannan kalamin ba daga bakinsa ba kwata-kwata a dai-dai wannan lokacin don haka ta tsorata, a tsammanin ta hatsari suka kusan yi, idanuwanta suka firfito cikin firgita dai-dai sanda ya kashe motar a gefen titi.

Ya kwantar da kansa bisan ‘steering’ suka kurawa juna ido yayin da kowanne ke kokorin fahimto boyayyen sirrin da ke zuciyar dan uwan sa, to amma ba wanda yayi nasarar hakan, ita ta fara kawas da kai ta maida duban ta ga motocin da ke gudun fanfalaki bisa kwalta, zuciyar ta cike fam da kuncin da bata san dalilinsa ba.

Cikin karfin hali yace “ Inteesar, baby, haba Sis, na hada ki da girman Allah kiyi hakuri, ni wasa nake Allah, amma da alama naga kin maida abin gaske?”

Daga Intisar no response (ba amsa) kai kace da zaunannen dutse yake magana, yayi shiru, yama rasa ta inda zai faro, ya langabar da kai jikin ‘seat’ din shi abin tausayi don dai ta tabbatar yayi nadamar, cikin tattausar muryar shi yace.

“Yanzu ke Sis (sister) in aka ce dake ina aikata abinda nake fadi sai ki yarda? Nayi zaton ke ce mutum na farko da zai shaideni a bisa norms and status (akidu da tsayayya) na Daddy Makarfi, ke ce (first) da zaki shaide ni (no matter what) al’amarin ‘may be’ (koda a wane irin al’amari ne kuwa)?”

A nan ne ta dubeshi da dukkan idanuwan ta da suka kada suka yi jawur, wasu kibbau masu tsananin kaifi yaji sun gilma cikin zuciyar sa, ya runtse idon shi gam da karfi, baya iya jure kallon cikin idanun Saratou, baya son jin wadannan ‘feelings’ din da yake ji game da ita a kullum amma a koyaushe ya dubeta tamkar ana linkawa ne, wayyo!

Ya kai hannu saitin kirjin sa ya matse da karfi idanun shi a rufe, shi kadai ya san me ya ke ciki? Ji yake Saratu na huda bargo da tsokar zuciyar sa wani ‘feeling’ ne da ba zai iya suffantawa ba, ba tun yau ba, ba tun jiya ba, a tun ranar da ya dawo Abuja, sanda mahaifin su ke kulle, Inteesar taki gaishe shi don sun yi biris da tallafin Mamar ta, sunyi watsi da taimakon karatun ta.

Abin ya cigaba beyond edpression (fiye da kimantawa) da har zuwa gidan ya gagaresa, yana ganin idanun Saratu sune magnet da ke jefa zuciyar sa cikin halaka da kaka-ni-kayi.

Ya sha tambayar abokan sa masu kanne mata su gaya masa yadda suke a zuciyar su don ya kwatanta da nashi amma bai taba jin mai irin nasa ba. Akwai wani abokin sa Sagir da yace

“ni kanwa daya ce da ni, duk sauran kanne na maza ne, amma yadda nake son su haka nake son ta ba wani banbanci, yo wane irin so ne zan mata da ya wuce in sa ido akan tarbiyyar ta? A kan me zan yi tunanin ta ina makaranta ko wani waje sai kace wata budurwata?

Kai Faisal, gaya mun gaskiya, Inteesar, kanwar ka ce da kuke UBA DAYA?” Sai yace wallahi Allah kanwarsa ce. Sagir yace “to sai a nemi tsarin Allah kada ya kasance aikin Shaitan ne”. 

To kamar kullum, ya soma rokon sauki cikin zuciyar sa har ya samu ya dawo hayyacinsa, bugun da zuciyar sa ke yi ya lafa, sai da ta gama shan kamshin ta tace.

“Ya Faisal ni ina ruwana ne? Me ka ji na ce? Kai kadai fa kake ta maganar ka, kake kidan ka kake rawarka ba matse ma baki nayi ba, in ma kayi din meye? Ba Mama tace lokacin ka ne ba?”

Yayi murmushi a ransa ko cewa yake yaushe Saratu zata girma ne, komi nata akwai kuruciya a ciki, at 27, ya bata rata na akalla shekaru goma don haka lallashin ta ba zai yi wuya ba, ya ce,

“Alright, na amsa wannan, ni dai so nake kiyi hakuri na san ranki ya baci, gashi mun kusa isowa gida, bana so Mamar mu ta ganki haka ‘bery-upset’ (a birkice) don zata tambayeni ko? Gashi kuma ban san me zan ce mata ba.”

Ta tura baki sabida matukar haushin da ya bata, ta soma motsi da bakin ta a hankali cikin tadin zuci, bata san har maganar ta subuto ta shiga kunnen sa ba.

“A wane dalili raina zai baci? Sabida Yayana yayi budurwa? This is sheer nonesense!” (Shirmen banza ne kawai). Ta girgiza kai da sauri sai kuma hawaye suka zubo.

Ya lakato hawayen yana murmushi ya ce,

“you see, ranki ya baci. Hawaye su kan zubo a dalilai guda biyu ne kawai Intisar; bacin rai ko tsananin farin ciki. Saratu da ki zubar da hawayen ki a domina, gara kisa dorina ki yi ta duka na har ki huce bacin ranki. Your tears mean a lot to me, (zubar hawayenki na nufin abubuwa da dama a gareni) amma bazaki gane hakan ba a yanzun.

Share hawayen nan maza-maza, don Allah ba don ni ba” muryar ta na rawa, kasa-kasa cikin rishin kuka tace “naji”. Yayi murmushi yace “ba haka nake son amsar ba, cewa zakiyi shikenan Ya Faisal di na, komi ya wuce, na hakura, sa’annan ‘regain your mood (dawo da yanayin ki) Inteesar di na?”

Ta shafi goshin ta zuwa siraran labbanta da ‘yan yatsun ta na dama, ita dai har yanzu RONKE na ranta, Ronke na damun ta, ta hana ta hadiyar miyau, da kyar ta hadiyi wani makalallen miyau daya bushe mata a makoshi, duk da taji matukar kunyar yadda yake mata magana a yau (lobing and romantic) tamkar ba Yayan ba, ta daure tace

“shin wacece Ronke tukunnah?”

Ya riga ya tsammaci tambayar, don ya san abinda ya tsaya mata a rai kenan don haka tuni ya shiryawa amsar ya ce,

“kin san Allah Ronke class-mate (‘yar ajin mu) ce, ina koya mata karatu bayan wannan ba wani mu’amala tsakanin mu…” “wane irin ba affair (mu’amala) tsakanin ku to me ya hada ta da wayar ka?” Ya murmusa kadan “dauka tayi, tun kan in kai hannuna” “to amma tace da ni wai kana wanka?”

Yayi dan jim, yana tattara amsar daya dace ya bata, sai ta sake jeho mishi wata “kuma karatun ba’a makaranta ake yi ba, in haka ne ya akai har tazo inda kake wanka?” Ta kafe shi da nakasassun idanunta dara-dara farare kal, sai yace cikin kosawa tare da kokarin kaucewa kaifin idanun ta.

“Amma dai kin san binciken abinda ya wuce baya da amfani, kuma rayuwa irin ta karatun jami’a cudanya da mata dole ne, abobe all ma Ronke kawata ce, tana zuwa gidan Major T. Ekiti inda nake zaune.

Ta zo ne in koya mata karatu ina wanka, ta zauna jirana in fito a sanda ke kuma kika kira ta dauka, dama anan falo na ajiye, that’s all I know (wannan ne kadai abinda na sani).”

Yadda ya fitittike yana bayani da sauri-da sauri duk sai ya bata tausayi, ya kuma bata dariya duka a lokaci daya, da gani zancen ya isheshi kuma iyakar gaskiyar shi ya ke fadi, amma sai bata nuna tausayin ba, ta sha mur sosai tace “ina na taba jin mace da namiji suna kawance? Wannan haramun ne” Yace “ni dai nace kiyi hakuri ko, komi ya wuce, daga yau nayi miki alkawarin ba zan sake kula ta ba tunda ranki baya so, ke da duk wasu matan duniya ma. Mace daya nake so, mace daya ke burge ni, mace daya nake so da kauna da dukkan ruhi na, mace daya nake sha’awar in aura amma ba zan taba iya auren ta ba.

Don haka kar ki kara sawa ranki wai ni Faisal ina son wata diya mace bayan ita, ba kuma zan sake kula wata mace da sunan ina son ta ba har sai kin yi aure intisar, beliebe me or not, (ki yarda da ni ko kada ki yarda) ba zan kuma bata miki akan Ronke ba.”

Yasa ma motar giya aguje suka harba kan titi basu sake ce da juna uffan ba. Maimakon zuciyar ta tayi sanyi da gane wasa yake zancen Ronke,  kuma Yayan nata na masifar gudun bacin ranta, a’ah, sai ta kara yin bakikkirin ninkin ba ninkin kishin Ronke Adeyemi da kishin wannan da yake son bazai iya aure ba, don ta san koma wacece wannan son ba kadan bane ba kuma na wasa bane, he really mean it (yana nufin abinda yake fadi), ta gane hakan ta hanyar gesture (motsi mai nuna zahirin abinda ke zuciya) dake zane baro-baro cikin kyawawan kwayan idanun sa. 

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

8 thoughts on “Siradin Rayuwa 2 | Babi Na Sha Daya”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×