Safiyar yau zaune nake kan kujera ina wanke-wake, yayin da Adawiyya kuma ke shara tsakar gida bayan kammala wankin bayi da tayi, can gefe kuma Inna Zulai ce tana lissafa mafitai da take sayarwa, sai Gwaggona da ke kai da komowa zuwa madafa kasancewar yauma girki a hannunta yake. Inna Amarya kuwa na ɗaki bata fito ba, dan dama ita uwar ɗaka ce da wuya ka ganta a waje, in dai ba wai ranar girkinta ba ko kuma ya kasance duka iyalan gidan ana zaune a tsakar gida. Baba ne ya fito daga ɗakinsa yana gyara zaman hularsa yake cewa da Adawiyya,”kira min Kabiru”. Ta ajiye tsinstiyar da ta-ke shara ta fita cikin hanzari domin cika umarnin Baba. Ni kuma na dubi mahaifin nawa da kyau ina yaba kyawunsa da kuma jin ƙaunarsa na ƙara fizgar duk wasu hudoji na jikina, ban ankare ba sai ji nayi hawaye sun cika min ido saboda tausayinsa, na lumshesu zuciyata na daɗa bugawa da sonsa da ƙaunarsa.
“Baba Sannu da fitowa.”
Nace da shi ina miƙewa na ƙarasa inda yake na karɓi buhun hannunsa da zai fita da shi, ba komai bane acikin buhun sai kayan faskaran icce.
Babana Adamu Hashimu asalin mutumin garin bichi ne dake cikin jihar kano, kuma sannane ne aciki da wajen ƙauyen bichi saboda sana’arsa ta siyar da itace wadda ya gada a wurin mahaifinsa Malam Hashimu, babu inda zaka shiga ka fita acikin ƙauyen bichi ka tambayi Malam Adamu me faskare ace maka ba’a sansa ba, ko kuma ka tambayi gidansa ba’a kawoka har dakalin gidanmu ba, Haka zalika shi ɗin manomi ne domin kuwa yana da gonaki har guda biyu a fagolo, sai dai a sakamakon ƙwacen gonakin da gwamnati tayi Babana ya rasasu dan ciki har da nasa guda biyun, haka yanaji yana gani babu yanda ya iya dole ya haƙura dasu dan bashi da inda zai kai kukansa a karɓar masa hakkinsa, sai dai ya kai kukansa ga sarki Rabba adalin shugaba, dan yace ba zai yafe musu ba, domin da albarkar wannan gonaki biyunne Baba ke noma abincin da za’aci a gidansa har na tsawon shekara, shinkafa, wanke, gero, masara, dawo, maiwa, waken suya da barkono duka suna daga cikin abinda Baba ke Nomawa.
Malam Adamu mutum ne mai mutumci da tsananin kyautatawa, kamilin dattijo mai wadatar zuci, bashi da kwaɗayin abin duniya ko kaɗan, hakan yasa girmansa da ƙimarsa ke ƙara yawaita a wurin jama’ar garin bichi, matan Malam Adamu huɗu, Hajiya Hajara itace matarsa ta farko wadda ya kaita saudiya tun silalla na da daraja, ayanda tarihi ya nuna Hajiya itace jarumar matarsa dan babu ruwanta da duk wata harkar fitintinu na kishiya ko kuma dangin miji, matar rufin asiri domin ko a wancan zamanin da Baba ke da ƙarfinsa Hajiya ta ɗauke masa nauyin karatun yaransu uku, Ƴaƴan wurinta biyu dana abokiyar zamanta ɗaya, wanda kaf cikin yaran gidanmu su kaɗai ne suka sami ilimin zamani na boko har matakin da suke akai yanzu na diploma, ƴaƴanta uku Kabiru, Aminu sai autarsu Safiya wadda a lokacin haihuwarta ne Hajiya ta rasu, itama kuma ranar data cika sati a duniya tabi bayan mahaifiyarta.
Inna Zulai ita ce matar Baba ta biyu, kuma ita ce su kai zama tare da Hajiya, fitinanniyar mata ce, dan ko da yaushe tana kan hanyar zuwa wurin bokaye a burinta na a lalata zamantakewar dake tsakanin Baba da Hajiya, sai dai har Hajiya ta rasu burinta bai cika ba Allah bai sa tayi nasara ba, akaf Matan Baba ita ce wadda taci gida domin ta tara Ƴaƴa da yawa, Amadu shi ne Babba, Sunusi, Mu’azzam, Lukman, Sadiya, Adawiyya, Mubarak, Saleh, Jamila da Habiba sai auta Zubaida.
Sai Gwaggona Suwaiba da ta zo a mata ta uku, Mace mai sanyin hali dan bata faɗa ko kaɗan, sai dai akwai miskilanci, idan Inna Zulai zata zo tsakiyar kanta sau dubu ta sauke buyaginta Gwaggona ba zata ce mata kanzil ba, kuma mutane su na ta faɗin daga Hajiya sai Gwaggona a matan da Baba yayi sa’ar samu, saboda Gwaggo da Hajiya halinsu kusan ɗaya ne, banbacinsu Gwaggona miskila ce bata kuma ɗaukan rainin dangin miji ko kaɗan, Gwaggona ni ta fara haifa sai dana shekara goma ciff a duniya sannan ta ƙara samun arziƙin haihuwa ta haifi Basma, Gwaggo da kanta ta shawarci Baba ya ƙaro aure, dan tun bayan haifata da ta yi taga haihuwa ta tsaya mata tsawon shekaru daga ita har Inna Zulai, ga Baba da son ƴaƴa dan kullum a adu’arsa Allah ya ƙara azurta shi da ƴaƴa na gari yake duk damu goma sha biyar da Allah ya ba shi.
Aisha ita ce mata ta huɗu a wurin Baba wadda muke kira da Inna Amarya, ƴar gidan sarkin noman garinmu ce, Tsakanin Inna Amarya da Gwaggona sam babu wani abu wai shi kishi, illa iyaka mutunta juna da suke. shekaru kusan goma sha biyu da Inna Amarya ta shafe a gidanmu bata taɓa haihuwa ba har yau, ko ɓarin ciki wannan, kuma dama tun bayan aurota babu jimawa na koma wajenta da zama, a ganina ba jin daɗin zaman wurin Gwaggona nake ba, dan ita takan hantare ni a wasu abubuwan da nake ko tayi min faɗa, amma ita kuwa Inna Amarya zallar gata ne take nuna min da sangarta, dama tun a lokacin da ta cewa Gwaggona zan koma wajenta Gwaggo tace mata ai gani nan in dai zata iya da halina ta ɗauka.
Bayan auro Innata Inna Zulai taci gaba da haihuwa dan yanzu haka ma wani cikin gareta, duk da ƴaƴa goma sha ɗaya da ta mallaka tace har yanzu bata gama cin gida ba.
To tsakanin Inna Amarya ne ma da Inna Zulai ake samun ƴar tsama, dan ita Inna Amarya bata barin ta kwana, ko ba ita aka taɓa ba in har za’a taɓa Gwaggo to sai inda ƙarfinta ya ƙare, ita kuma Inna Zulai da shegen habaicin bala’i da bata gajiya da yinsa, martani kuma sai dai idan Inna Amarya bata ji ba, darajar Ya Amadu kaɗai Inna Zulai ke ci wataran har Inna Amarya ta ɗaga mata ƙafa, dan Ya Amadu mutum ne, idan baka sani ba zaka rantse kace Gwaggona ita ta tsuguna ta haife shi har Ya Kabiru, Ya Amadu sam bai ɗauko baƙin halin uwarsa ba, kuma baya goyon bayanta akan abubuwa marasa kyau da take, hasalima shi mai yawan yi mata nasiha ne wataran har ya tarasu duk ukun yay musu nasiha, idan ya gama ta kaɗe zane tace ita dama ai ta jima da sallama shi, dan ba tun yau ba ta gama gane Gwaggo ta shanye mata ɗa, to saboda haka yaje gashi ga Gwaggon nan, da ace shi ɗaya ta haifa sai tayi kuka, to amma Allah ya bata da yawa, dan haka ba zata bari takaicinsa ya kasheta ba. Ya Amadu yana kuka da wannan halin na mahaifiyarsa sosai, sau tari yakan zubar da hawaye agaban Gwaggo sai dai Gwaggo ta lallashe shi ta ƙara bashi haƙuri, tace masa yaci gaba da haƙuri duk lalacewarta uwa ce, yaci gaba dayi mata adu’a Allah ya ganar da ita.
Gidamu ginin ƙasa ne daga ciki, daga waje kuma ginin bulo wanda babu ko fulasta ajikinsa, shi ma ginin bulo ɗin anyi shi ne babu jimawa, dan waccen shekarar ne lokacin da Ya Amadu yabi Yayan abokinsa lagos ya tayashi aikin company ɗin mahaifinsa acan, to a wannan lokacinne Ya Amadu ya dawo da shatara ta arziƙi da Baban Joseph ya haɗa masa, Kuma ko da ya tashi dawowa Obi abokinsa shi ya dawo da shi ya kawo shi har ƙofar gida a danƙareriyar motar gidansu, shi ne har aka rushe ginin ƙasar ƙofar gidanmu aka tada na bulo, da shi dasu Ya Kabiru suka yi aikin dan ko ƙwandalarsu basu kashe ba a wurin neman me aiki, Sannan ni da Sadiya da Adawiyya da Lukman ya kaimu makarantar boko Government Secondary School Bichi, ya kuma ƙarawa Baba jarin itacce, itama mahaifiyarsa ya ƙara mata jarin Mafitai da ta-ke siyarwa, sannan ya sarowa Gwaggona kwalaben manja yace ta-ke saidawa, sauran abunda ya rage masa kuma ya biya kuɗin koyan ɗinkin da ya ke zuwa.
A wannan lokacin dai gidanmu an godewa Baban Joseph da kuma yi musu adu’ar samun hasken musulunci, ko ni idan naje makarantar boko sai na shiwa kafirin nan albarka, na kuma yi masa adu’ar Allah yasa ya musulunta, domin ta silarsa yau gani a makarantar boko da naketa fatan kasancewata aciki.
To ita dai Gwaggona da Yagana(Kakarmu ta wurin Uba) sam basa son hulɗar Ya Amadu da Obi kai harma da shi Joseph ɗin da ya ke ɗauka matsayin uban gidansa, ayanda ta-ke nunawa ta tsani ahalinsu gaba ɗaya dukkuwa da basu taɓa ganin ko mutum ɗaya daga cikinsu ba, acewarta Obi ba abokin hulɗa bane karya dulmiyar mata da ɗa, ko kuma shi Joseph ɗin ya cutar da shi, dan arna abun tsoro ne, Baba ya kan fahimtar da ita akan alaƙar tasu ba wani aibu bane, ta dalilin hakan ma sai shi Amadu ya zama silar jawosu cikin musulunci, Gwaggo dai ba zata tanka ba illa iyaka taɓe baki da takeyi, kusan kuma duk sanda Ya Amadu zai ce mata Oga Joseph na gaisheta sai tayi kunnen uwar shegu da shi, idan ya kuma magana tace ai taji, ranar nan kuma tace masa ita dai wannan gaisuwa da ake kawo mata kusan kullum tunda babu tsiyar da ta-ke ƙara mata a ƙyaleta, ko shi Joseph ɗin ya riƙe gaisuwarsa ko kuma shi Ya Amadu yake riƙe aiken saƙon iyaka shi, wani lokaci da sukayi waya da Oga Joseph tana zaune a wurin sai Ya Amadu yake ce masa itama Gwaggo na gaida shi, da alama shi Joseph ɗinne ya fara tambayarta, Ya Amadu na gama wayar ta dube shi tace ni Amadu a tarbiyar da nayi maka ban koya maka ƙarya ba, kuma daga yau idan ka ƙara cewa wannan zindiƙin kafirin ina gaisheshi wallahi sai ƙaga yanda zamu kwashe da kai acikin gidan nan, to fa daga wannan lokacin Gwaggo ta fara share Ya Amadu, ta koma komai zatayi sai dai Ya Kabiru, dan ko gaisuwar Ya Amadu sama-sama ta-ke amsa masa, babu shiri kuwa ya fara janyewa daga Oga Joseph koma nace ya janye gaba ɗaya, yana tare da shi ne dama saboda a rufawa kai asiri, tunda duk sanda ya buƙaci yay masa rakiya zuwa Lagos yana samun kuɗi sosai a wajensa, harma yayi masa alƙawarin zai yiwa Daddynsu magana a nema masa gurbin karatu a jami’a dan ya ɗora degree nasa tunda yana da diploma.
“Baba to kaje a aske maka gemun mana tunda naga yana damunka.”
Na faɗa idanuna ƙyar akan haɓarsa da yake sosawa, ya bani amsa da cewa, “yau insha’Allahu zani a aske, ni nafi ganewa askin wanzamai su kuma su Amadu sai suce ba haka ba”. Ina murmushi nace, “to Baba ai na kilifa ɗin yafi yin kyau, kuma kaga shi ance ba’a fiye ɗaukan cutukan zamani ba.”
Kafin ya bani amsa Ya Kabiru ya shigo, ya tsuguna yana cewa da Baba gashi.
“Yauwa Kabiru nace ya za’ai anjima dan Allah ka nemo mota ƴar ƙurƙura akai itacce gidan galadima”. “babu damuwa Baba sai a nemo, zanwa Hamisu magana idan baza shi cikin gari ba saina karɓi tasa”. “to Na gode Allah yayi muku albarka. Ina Amadu yana nan ko ya wuce makaranta?”. “ehh naji dai ya fita ɗazu to amma ban sani ba ko makarantar ya wuce tunda banji ya min sallama ba.”
Baba yasa hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mishi,”Dubu huɗu ce ka bashi ya auno masara da shinkafa ya kawowa Suwaiba”. Yasa hannu biyu ya amsa tukunna ya fice, shi ma Baba yay sallama da Matansa ya fita, mu kuma yaran mukabi shi da adawo lafiya.
Da yamma muna zaune ƙarƙashin rufin kwanon ƙofar ɗakinsu Lukman wanda yake kallon ɗakin Baba, Inna Amarya ce ta gama yi min yankan farce ta-ke kuma saka min lalle kasancewar gobe zamu koma makarantar boko hutu ya ƙare, an gama sawa Adawiyya nata tun ɗazu, Adawiyya itace sakuwata dan tsakaninmu shakara guda ne ta bani, komai namu tare Inna Amarya ta-ke haɗamu tayi mana, mun zama tamkar ƴan biyu duk da cewar uwarta ba son hakan ta-ke ba, dan wani lokacin Inna Zulai har kulleta take a ɗaki ta zaneta akan shige mana da ta-ke yi, haka zataci kukanta ta gama, tana buɗeta kuma ta kuma dawowa wurinmu, burinta ma bai wuce ta koma wurin Gwaggona da zama ba dan kayanta da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai ta kwaso ta maida su can, shi yasa abin da ke shiga tsakaninta da uwarta harara da hantara.
Ya Kabiru ne ya shigo hannunsa riƙe da baƙar leda, yasa Zubaida ta miƙo masa kujera ya zauna gefe kusa damu, fuskar nan tasa ɗauke da murmushin da baya rabo da shi, marabar shi da Ya Amadu kenan, Shi mai fara’a ne da son mutane saɓanin Ya Amadu da baya son mutane kuma miskili ne na ƙin ƙarawa, shi idan ka ganshi a gidan yana hira to da Baba ne ko Gwaggo ko Ya Kabiru wanda suke tamkar ƴan biyu dan tsiransu shekara ɗaya ne a haihuwa.
Ina bala’in son duka yayyuna biyun nan saboda kyawawan halayensu da ke burge kowa, da kuma yanda suke nuna min tsananin so, dan komai suka rakiito da tsarabarsu nawa ne ni da Adawiyya, Ni yarinyace wacce ta san kyau kuma nake son kyau, saboda hakane na gane duka yayuna biyun da nake matuƙar so kyawawan gaske ne, hancinsu har baka irin na Baba, ga fararen idanu da dogon gashin ido, na kan kasa tantance acikinsu waya fi wani kyau, idan na tambayi Adawiyya sai tace ai Ya Kabiru yafi kyau tunda yafi Ya Amadu haske kuma yana da wushirya, sai nace mata a’a shifa Ya Amadu har dimple ne da shi kuma bakinsa yafi na Ya Kabiru ƙanƙanta, haka muke zama muyita wannan musun da junanmu, ƙarshe sai Yagana ce ta raba mana gardama tace ai Ya Kabiru yafi kyau tunda shi ingarman namiji ne, Kalar mazan da mata suka fi so, ba ƙaramin daɗi naji ba da batun Yagana domin akomai ina so naji ance Ya Kabiruna yafi, haka itama Adawiyya akomai tafi so ace Ya Amadu yafi.
“Sannu da dawowa”. Inna Amarya tace da Ya Kabiru wanda yake latsa ƴar ƙaramar wayarsa. “yauwa Inna Amarya”. Ya amsa mata yana buɗe kwanon abincin da Basma ta ajiye masa agabansa yanzu.
Gwaggo ta fito tana ce mishi, “Kabiru kuma saina jiku shiru daga kai har Amadu baku kawo cefane ba. Shi ne kawai saina bada aka siyo taliya ƴar murji akayi jalof, Allah yasa dai zaka iyaci”. Tun shigowarsa idona yake akansa na kasa ko da ƙiftawa, babu wanda ya lura dani harta shi ɗin dana ke ta aikin kallo, gani nayi ya ɗan yatsine fuska kaɗan kamin yace, “zanci mana Gwaggo, ba dai abinci bane kuma duka kowa yaci zai rayu lafiya. To ni wane da bazanci ba”. Ya numfasa bayan ya sosa girarsa sannan yace, “Gwaggo kiyi haƙuri da mukaje kai itacen gidan Galadima ne bamu dawo da wuri ba, sai yanzu ne dana dawo na miƙa mishi kuɗin.”
“Ai tunda ansamu wanda za’aci ɗin shikenan, dama bana son yin abinda ba kwa son ci ne, na bada a siyo ƴar gwamnati naji tayi tsada shi ne nace to kawai a karɓo taliyar murji.
Allah sa shi wancan ɗin idan yazo ya iya ci”. “zaici mana Gwaggo, yanzu ma na baro shi shagon ɗinki yana nan tafe”.
Gwaggo ta wuce dan ci gaba da hidimarta, shi kuma ya buɗe kwanon abincin bayan ya wanko hannu ya fara ci da bismillah, ba ma’abocin cin abinci bane shi dan haka kaɗan yaci ya aje gefe kusa da shi yay masa adani mai kyau yanda wani ba zai shigo yagga saura ba yace masa zaici, domin nawa ne ya ajiye min, haka muke da shi a gidan, idan banci sauran abincinsa ba to zamuci tare.
Ɗagowar da zaiyi muka haɗa ido sai nayi saurin saka hannu na rufe bakina zuwa hancina, murmushi me bayyanar da haƙora yayi ya ƙura min ido yana kallona tare da min nuni da ƙunshina da idonsa da kuma ledar da ke hannunsa.