Skip to content
Part 1 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

3 years ago.

A cikin garin kano, a unguwar Gandun Albasa, cikin wani d’an matsakaicin gida, kana ganin gidan kai tsaye za ka kira shi da na mai k’aramin k’arfi.

Daga waje k’ofa ce idan ka shigeta zaka biyo ta wani k’aramin soro, a soron akwai k’ofar d’aki mai band’aki a cikinsa kafin ka karaso cikin tsakar gidan wanda babu ko siminti rairayi ne a malale wanda ya ke nan a share duk da yana da d’an girma amman hakan bai hana an share shi tsaf ba!

Daga gefe guda akwai d’akuna guda hud’u a jere, daga can ta wajen k’arshen tsakar gidan kuma akwai bayi wanda aka sakaye shi da k’ofar langa-langa duk ta yi tsatsa, sai kuma opposite d’inshi kitchen ne da ko k’ofar langa langar ma shi babu amman baka iya hango cikin kitchen d’in saboda duhunsa sakamokon bangon da duk ya yi bak’i wuluk ta dalilin girki da itace.

Wata y’ar matashiyar budurwa da ba zata gaza shekaru 14 ba ce a tsakar gidan sai uban zufa take yi, ta yi kneel down ta d’aga hannayenta sama, a kan tafukan hannayen nata kuwa wasu maka makan takalman ball ne d’aya a kowanne hannu.

D’an motsi ta yi wanda hakan ya sanya takalmin dake kan hannun hagun ta ya kusan fad’uwa, tsabar yadda duk ta rikice ta fita a hayyacin ta ga rana ga tsoron bulala ne ya sanya ba ta san lokacin da ta yar da na hannun daman nata tai saurin rik’e na hannun hagun nata ba.

Ai kuwa ba ta k’arasa rik’ewa ba ya d’aga zabgegiyar bulalar dake rik’e a hannunsa ya zabga mata a kan hannayen nata, hakan yasanya ta k’arasa zubar da takalmin itama ta zub’e a nan k’asan saboda ba kad’an ba dukan ya shigeta.

Kamar jira yake yi kuwa ya rufeta ta duka! Babu ji babu gani, ihu take yi sosai tana kwala kiran “Mama!, Mama!! Mama!!!”

Mama da ke a d’aki, wadda tun farawar abun take jin su, ta runtse idanunta hawaye na gangaro mata tana addu’an Allah ya kawo wanda zai ceci ‘yar tata.

Kamar daga sama ya ji an fizge bulalar, juyowa ya yi a fusace zai yi masifa suka had’a ido da wani kyakkyawan saurayi! Mai manyan idanuwa. Yana da cikar gashin kai da na gira da dogon hanci sannan bakinsa bai cika girma ba, skin colour d’insa chocolate ne me d’an haske da shek’i, dan ko kad’an ba za ka kira sa da bak’i ba.

Cikin b’acin rai Junaidu yake kallon yayan nasa wanda suke mugun kama da juna bambancin kawai Junaidun ya fi yayan nasa kyau da manyan idanuwa da haske, sannan lips d’insa bai yi duhu ba kamar na yayan nasa da suka yi bak’ik’irin instead nasa shi light pink ne.

Tun cikin bacci yake jin hayaniyarsa a tsakar gida sama sama har ya kai ga farkawa ya wattsake yafara jiyosu sosai.

Kallon kwayar idanunsa Junaidun yayi a zuciye ya yar da bulalar a k’asa kafin ya doka wani uban tsaki sannan yace”yanzu fisabillillahi ya Ja’afar abinda kake yi ya dace kenan??idan za ka hukunta Yarinyar nan ka dinga hukunta ta a lokutan da kake cikin haiyyacinka mana!!! kalla fa idanunka!

Ka je ka yi high!! Kawai ka zo sai jubgar y’ar mutane ka ke yi so kake ka illatata? Kuma zan iya dafa Qur’ani akan cewa ba wani laifin kirki ta yi maka ba, a kan laifin da bai taka kara ya karya ba ka zo kanata dukanta haka! me ta yi maka??”

Ya yi masa tambayar still yana tsare shi da manyan idanuwansa.

Mitsi-mitsi ya Ja’afar d’in yayi da idanuwansa da suka yi jazir sannan ya yi baya kad’an ya d’an yi tangal tangal kamar zai fad’i sai kuma ya dawo daf da Junaidun ya tsaya ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa sannan ya zuba masa idanuwa kafin yace,

“Kai,dan uwarka ni sa’anka ne?”

Shiru Junaidun ya yi yana kallon shi kafin a hankali ya d’an sassauta murya yace “yi hak’uri, mai taimaka??”

Tsaki ya Ja’afar d’in ya yi sannan yace
“Akan gyaran d’akin da suke yi mini it da Jalila ne, Jalila ta yi mini bayanin ta ta wuce.

Ita wannan makirar sai ta tsaya shara wai Umma ce ta sakata sharar tsakar gida, abun haushin da na shiga d’akin nawa fa ko tsinke ba’a d’aga ba komai yana nan a yadda na barshi.”

Shiru Junaidu yayi don in dai zai iya tunawa to jiya da shekaran jiya duk ya ganta tana gyaran d’akin ya Ja’afar, kuma a ka’idarsa shi ya Ja’afar d’in kwana bibbiyu suke yi itada jalila, To ya za a yi kuma yau ma yace still itace za tai mishi gyaran d’aki.

Juyawa yai yana kallon hanyar d’akunan gidan kamar yana neman wani abun kafin da k’arfi ya fara kwala kiran “Jalila!Jalila!!Jalila!!!”
Ya jafar ne ya d’an tab’o hannunsa sannan yace masa “kai ta tafi jarabawa fa”.

Juyawa Junaidu ya yi ya kalle sa kafin yace “ya Ja’afar yau a ka’ida waye zai yi maka gyaran d’aki???”

hiru yayi kafin cikin maganarsa ta y’an shaye shaye yace,

“Kagane ko! A k’a’ida Jalila ce, to ita wannan makirar sharar da ta yi jiya da shekaran jiya duk ba su fita ba kai gyaran ma kwata-kwata bai yi ba shiyasa yau sai d’akin yayi kamar ba a tab’a gyarawa ba, sannan Jalila jarabawa ta tafi, shine na shigo na ganta tana shara kuma Jalila ta sameni a waje ta ce mini ta rok’eta ta gyara d’akin ita ta makara amman ta zazzageta har da marin ta fa tayi!!!
ita dan uwarta a gidan ubanta ba a alfarma ne eh? Shine fa na shigo na sameta tana kwashe shara, ni kuma na d’auki alwashin sassama mata kamanni a yau d’innan tunda ta raina ni, ai ba Jalila ta zaga ba ni ta zaga tunda d’akina ne, kai marin ma ni ta mara tunda ai dai duk akan d’aki na ne”.

Junaidu da ya fara fahimta makirci ne kawai Umma da Jalila suka had’a saboda sunga an kwana biyu ba a jibgi baiwar Allah ba, sannan su Baba ya hana su dukanta shine suka biyo ta hannun ya Ja’afar tunda sunga shi in dai ya bugu to ba iya gane gaskiya da k’arya yake yiba sannan ko baya ga hakama daman chan shi ya tsani Yarinyar.

Sunkuyawar da ya ga ya Ja’afar nayi yana k’ok’arin sake d’auko bulalar ne ya dawo dashi daga nazarin daya tafi, da sauri ya rik’e hannun ya Ja’afar ya shiga lallab’asa akan ya yi hak’uri ya barta za a gyara masa d’akin nasa, amman fur ya k’i hak’ura.


K’arshe dai naira ashirin Junaidu ya d’auko daga aljihu ya basa tukunna ya hak’ura ya karb’a yana murmushi yace ta bar gyaran d’akin ma gobe sai ta yi, idan kuma Jalila bata da jarabawa goben sai ta bari jibi ta karb’i aikinta.
Juyawa ya Ja’afar ya yi yai hanyar fita daga gidan.


Shi kuma Junaidu ya juyo yana kallonta anan a durk’ushe tana kuka tana ajiyar zuciya ta kifa kanta a k’asa.

A hankali ya sunkoyo kanta, kafad’unta ya kama duka biyu ya juyo da ita sannan ya sa hannunsa a hab’arta ya d’ago fuskarta.

Da sauri ta runtse idanuwanta da suka yi luhu luhu fuskar nan ta yi jawur tsabar kukan da ta ci. Shiruu ya yi yana kallon ta, tun daga kan lafiyayyan gashin gaban goshinta wanda suka kwanta sukai lub lub akan farar fatar ta, zuwa kan gashin girarta masu kyau da shape kamar ta yi cavn da madaidaitan idanuwanta, zuwa kan dogon hancinta wanda yai kmr M daga k’arshe amman ba sosai ba da dan mitsitsin bakinta. Cikin seconds d’in da ba su fi uku ba ya yi mata wannan kallon.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya kira sunanta “Huda” saurin bud’e idanunta tayi ta kallesa!

Kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta yi saurin ture hannunsa daga jikinta ta tashi da gudu tai hanyar d’akin Mama.

Shiru ya d’an yi, chan kuma a hankali ya mik’e tsaye, ya juya da niyyar komawa d’akinsa.

Juyowar da zai yi ya ga Umma a tsaye tana kallonsa sai kuma Anty zainab wadda ke tsaye a can bakin k’ofar gidan tana d’an lek’a waje da alama bayan Ja’afar wanda ya fita yanzun ta ke bi da kallo. Daga gani ka san basu dad’e da shigowa cikin gidan ba dan ga lullub’i a kanta da kuma jaka a hannunta, itama anty zainab dake bak’in k’ofa haka, amman tabbas ta gansa tare da Huda dan gashi ranta a mugun b’ace yake!

Cikin in inar da bai san yana da ita ba yace, “um um Umma dddagaa ina ku ke?”

K’arasowa ta yi gaban sa ta tsaya sannan cikin b’acin rai tace”daga gidan ubanka nake!!”.

Shiru ya yi ya sunkuyar da kansa yana sauraronta tana fad’a baki da kumfa, Anty Zainab da ta k’arasa shigowa yanzun tana tayata.

Umma ce ta ce “wato da ka d’auka ba yanzu zan dawo ba ko? Shi ne kaje harda wani d’ago ta kana kallon ta, idan za ta had’iyi zuciya ta mutu Junaidu ina ruwanka da damuwarta?? Ka ga ta inda Ja’afar ya fi ka ko?Yaron nan ko kyalle ne indai nace banaso to kuwa shima ba zai so shi ba, anya ni na haifeka kuwa?a ce Yaro kwata kwata baya kishin uwarsa!! An bi an lashe ka an shanye ka to wallahi ba’a isa ba, ni naci uwar boka ma ballantana malam. Ka ci gaba da b’ata mini rai har sai ka ja nai maka baki tunda baka jin magana ta dudda dai na san ba yin kanka baneba.”

Anty Zainab itama tace, “ke kuwa Yarinya ta yo gadon munafurci ai ba zai tab’a ganin laifin taba,mu mun buga da wadda ta haifo ta ma ta hak’ura ta barmu, ballantana ita…”

Ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba haka nan suka yi ta habaici a tsakar gidan babu wanda yace musu ci kanku sukayi suka gama suka shige d’akin Umma suna huci, anan d’in ma maganar su kai tayi, da suka gaji Umma ta bawa Aunty Zainab sak’onta ta mik’e tai mata sallama ta fito ta tafi, har ta fita a gidan mamakin Junaidu take yi.

Ba irin yadda ba su yi ba akan ya fita harkar Yarinyar tun bata kai haka ba amman a banza ajiyar zuciya ta sauk’e a ranta tana adduar Allah yasa Junaidu dai ba gadon wahala ya yo daga wajen ubansa ba .

Can d’akin Mama kuwa Hudan ce kwance akan gado ta d’aura kanta a kan cinyar Mama tanata kuka, Mama bata hanata yin kukan taba sai da taji ta d’an sassauta kukan nata tukunna a hankali ta shafa kanta tace ”Huda ba na hanaki shiga harkar Junaidu ba?? Duk da a cikin y’an gidan nan shi kad’ai ne baya zaluntarki yake kuma kare ki amman na san kin san cewa ba na son alak’ar ku ko? Yanzu duba ki ga irin zagin da kika ja mini da ke kanki”.

Shiru Hudan tayi da kukan da takeyi kafin ta dago kanta ta share hawayenta ta kalli mama sannan a hankali cikin sanyi tace, “Maamaa ni fa ban kula shi ba Allah, kawai dai ya karb’e bulalar da Ya Ja’afar yake duka nane ya bashi hak’uri amman ni ban ce masa komai ba.”

Shiru Mama tayi tana kallon y’ar tata kafin tace, “to ke Huda mai yasa da Jalila tace ki gyara mishi d’aki kika k’i kika hau shara??”

Raurau Hudan ta yi da idonta kafin tace “Mama jalila k’arya ta yi mini, daman jiya akan ya Junaidu ya hanani wanke mata uniform d’in makarantar ta tace mini wallahi sai ta saka ya Ja’afar ya zaneni, wai tunda na shiga tsakaninta da d’ayan yayan nata bara sai ta sa d’ayan ya zaneni.”

Shiru kawai Mama tayi tana tunani, ko ba a fad’a ba daga yanayin fuskarta ka san ranta a b’ace yake.

Gaskiya ita dai hak’urin ta ya kusan k’arewa, taya still za a mayar mata yarinya kamar wata jaka, dan ma ta samu sauk’i tun lokacin da ta je wajen Kaka (Baba Bashir) ta kai masa k’orafi akan su Umman da jalilan.

Ran kaka ya yi mugun b’aci a lokacin hakan yasa ya kira Baba ya ja masa kunne akan yayi musu gargad’i mai zafi dan in har ya sake jin ko da marin Hudan ne anyi a tsakanin Umma ko Jalila to bai yafe masa ba.

Baba ya shiga rud’u a wannan lokacin domin kuwa a duniyar nan idan akwai abunda yake jin tsoro to shine b’acin ran Umma amman kuma yanzu ga abunda mahaifin sa ya fad’a wanda ko hauka yake yi ba zai bari Allah ya isan iyaye ta hau kansa ba, hakan yasa yana dawowa gida ya rufe ido ya tara su a d’akinsa ya cewa Umma da Jalila.

“Kar su k’ara dukan Huda, sannan kar a sake d’aura mata talla, wankinsu su dunga yi da kansu ko sukai gidan wankau, sannan wanke wanke da wankin band’aki tsakanin Huda da Jalila duk ranar da mamanka ke da girki kai ne zaka yi, indai har kuwa aka k’etare abunda ya fad’a to a bakin auren Umma.

Abunda kawai ya yarda aikin Huda ne parmanent shine sharar tsakar gida domin ita Jalila na zuwa makaranta.”

Umma a wannan lokacin kusan daskarewa ta yi tsabar mamaki. Mutumin da ko maida mata magana ba ya iya yi shi ne yau harda ik’irarin cewa ‘a bakin aurenta!!’ Tabbas da sake, kasa yin shiru tayi dan haka ta yi gyaran murya sannan tace “Alhaji ka bani mamaki matuk’a amman ba zan yi ja in ja da kai ba a gaban Yara. Abu d’aya wanda na sani shine kana dab da b’ata tarbiyar Yarinyar nan kai da uwarta dan ba zai yiwu ace kab gida Yaro babu mai kwab’arsa ba, ga yayunta nan maza amman an nuna mini iyakata, Alhaji ance babu mu ba Huda ko? Saboda ita shafaffiya da mai ce? Ni za ka yiwa haka akan wad’annan mutanen???”

Ta yi maganar tana dukan k’irji da kafe Baba da manyan idanunta wadanda yake hango tsantsar b’acin rai a cikinsu.

                 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

So Da Buri 2 >>

1 thought on “So Da Buri 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×