Idan tace bata cikin farin ciki to ta yi ƙarya. Tana tsaye bakin window tana jira ta ga ko Hassan zai dawo daga masallaci da wuri saɓanin jiran da zai yi rana ta fito ya dawo. Sai ta ga hakan bai sauya ba. Sai da ya bari gari ya fara haske. Da sauri ta koma ɗaki ta kwanta lokacin da ya turo gate. Ta shiga bargo ta ƙuɗundune tunda dai a saninsa ita mara lafiya ce.
"Ya jikin naki?"
Ya tambaya yana saka hannu a kanta da wuya sai kace wacca ta yi zazzaɓi. Sai da ta. . .