Skip to content
Part 11 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Idan tace bata cikin farin ciki to ta yi ƙarya. Tana tsaye bakin window tana jira ta ga ko Hassan zai dawo daga masallaci da wuri saɓanin jiran da zai yi rana ta fito ya dawo. Sai ta ga hakan bai sauya ba. Sai da ya bari gari ya fara haske. Da sauri ta koma ɗaki ta kwanta lokacin da ya turo gate. Ta shiga bargo ta ƙuɗundune tunda dai a saninsa ita mara lafiya ce.

“Ya jikin naki?”

Ya tambaya yana saka hannu a kanta da wuya sai kace wacca ta yi zazzaɓi. Sai da ta sauke numfashi wanda ya fito kamar mai jin jiki, sannan cikin sanyin murya ta ce

“Alhamdulillah da sauƙi.”

Ta kama hannunsa ta riƙe tana wasa da ƴan ƴatsunsa.

“Ka yi haƙuri na hana ku bacci. Anjima zan je asibiti In shaa Allah a rubuta min magani”

“Bayan mun ci abinci sai na kai ki”

Tunawa da yayi babu mai musu abinci ya saka shi zaro wayarsa daga aljihu yana kiran waya. Bayan sun gaisa yake cewa

“Hajiya Mama Safina ce bata jin daɗi, ko za’a aiko mana da abinci?”

Ya san tunda Safina ce, Hajiya Mama ba zata ƙi ba. Tana ƙaunar Safina sosai. Ta yi mata addu’ar samun sauƙi suka yi sallama. Maimakon ya tashi kuma sai ya samu kan shi da zama. Tausayinta yake ji sosai musamman da ta zauna ta ƙurawa waje ɗaya idanu. Ya san akwai damuwar ƙarin aurenshi a tattare da ita. Sai ya fara jan ta da hira tana amsawa kamar mai jin jiki.

Nan banɗakinta ya shiga ya yi wanka ya fito ya shirya. Lokacin aka kawo abinci ya je ya amso ya dawo ya tashi yara saboda Safina tace gwanda a tashe su ba sai yunwa ta musu lahani ba. Shi ya yi musu wanka saboda mai aikinta bata zo ba tukunnan. A rashin saninsa, Safina ce ta yi waya yana banɗaki tace kar ta zo da wuri sai ta neme ta.

Nan ya bar Safina ya ce zai kira Afrah ta zo su ci abinci. A falonta take zaune da cup a hannunta tana shan shayi, ta yi kwaliyya mai sauƙi cikin wata doguwar rigar atamfa da bata kama ta ba amma ta amsheta.

“Ina kwana Boo”

Ta gaishe shi tana mai murmushi a kunyace. Ran shi ya yi masa daɗi ganin bata yi fushi ba. Ya amsa gaisuwarta yana maida mata murmushi tare da ce mata ta taso su ci abinci. Ɗaki ta koma ta ɗauko hijabin da ta yi sallar asuba ta saka ta bi bayanshi.

Akwai waina sannan akwai dankali da ƙwai sai ruwan shayi wanda ya ji kayan ƙamshi. Ce mata ya yi ta zuba wanda zata ci. Wainar ta ɗiba ƙwaya biyu ta bar shayin saboda yanzun shayin ya iske ta tana sha.

“Meye wannan kika zuba?”

Ya tambaya yana kallon waina guda biyun da ta ɗiba. Murmushi ta yi tana sunkuyar da kai. Ƙwaya biyu ya ƙara ɗiba ya saka mata.

“Bazan ce kina da ci ba. Idan baki ƙoshi ba ki ƙara.”

Cikin sanyin murya ta yi mishi godiya. Safina ji ta yi kamar ta haɗa wuta ta jefa Afrah a cikinsa. Hassan ya zuba ma yaran da Safina sannan ya zuba ma kan shi. Gaba daya hankalinsa na kan Safina da take nuna alamun tana jikinta baya yi mata daɗi. Yana yi yana mata sannu. Tunda Afrah ta saka idanunta kan abinci bata ƙara ɗagowa ba har ta gama ta tashi ta koma ɗaki.

Bayan kimanin awa guda da dawowarta sashenta sai ga Hassan ya shigo. Talabijin take kallo dan bata da wani abu da zata yi a lokacin. Zama ya yi a gefenta yana gaya mata zai je ya kai Safina asibiti a duba jikinta.

Murmushi ta yi mishi har kumatunta ya lotsa. Ya saka ɗan yatsansa manuni ya taɓa inda ya lotsa ɗin. Ba haka ta hango daren farkonta a gidan mijinta zai kasance ba. Balle kuma wayewar ranar da aka kaita. Bata yi tunanin tun jiya zata fara karo da matsaloli ba duk da ta san matar tasa tana da matsala dan tunda ta tare su a shago ta gane hakan. Amma zata yi maganin abun sannu a hankali.

*****

A kan Gado ya tarar da Safina sai cika take tana batsewa.

“Me ya same ki? Wa ya ɓata miki rai?”

Ji ta yi kamar ta rufe shi da duka dan baƙin ciki da ɓacin ran da ya haddasa mata. Zuciyarta tafarfarsa take yi. Ta gama shirinta tana jiranshi ya zo su wuce asibitin ta ji shiru. Zagayawa ta yi baskwata inda masu aiki suke zama dan ta kira mai aikin nata kuma har ta zo tare da sabuwar yarinyar da zata dinga kwana. Dai dai windon ɗakin Afrah take jin muryar Hassan ƙasa ƙasa. Matsawa sosai ta yi jikin windon dan ta ji abunda yake cewa. Sai da ta yi mugun dana sani. Wani jiri ne ya kwasheta sai da ta zube ƙasa shirim! Ƙwaƙwalwarta ta daina lissafi ga kunnuwanta basu daina jiyo mata abunda take jiyowa ba.

Bata san yanda aka yi ta koma ɗaki ba. Ita zai yaudara ya wulaƙanta? Ya barta tana jira shi ya tafi can yana lallaɓa ƙaramar yarinya yana mata magiya? Abunda ya daɗe bai yi mata ba? Zai dawo, zai kawo kanshi. Sauran kwana shida. Amma babban baƙin cikinta duk yanda ta hana kan ta bacci ta kuma hana shi sai da ya lallaɓa ya ci amanarta?

“Tashi mu je asibitin. Ina so mu dawo da wuri I need to rest”

Dole yace yana bukatar hutawa mana ta faɗa a ran ta. Amma zata yi maganinshi. Ba sai ya kara samun sarari ba kafin ya ƙara cin amanarta ba? Tashi ta yi ta janyo mayafinta ta bi shi a baya suka fita.

A asabitin sai da suka dan bi layi kafin su samu ganin likita. Yai mata ƴan tambayoyi ta amsa ya bada test aka yi mata. A nan ne suka ɗauki lokaci sosai kafin su samu a yi musu sannan suka jira test. Duk abubuwan da likitan yake tunani basu bane. Dan haka ya bata maganin ulcer da pain reliever ya sallame su.

Shawara ta bashi kan su sayi dan abun da zasu ci kafin su koma gida. Ta saka ya kira Afra take tambayarta

“Amarya me kike so a taho miki da shi?”

“Bana jin daɗin bakina, pepper soup nake so na kifi”

Hakan ba ƙaramin ɓata ma Safina rai ya yi ba. Sai ta ji kamar ma so take ta san wani abun ya shiga tsakaninta da Hassan. Ƙwafa ta yi a zuciyarta. Suka sayi abunda zasu saya suka koma gida.

Ɗakin Afrah ya wuce tare da kai mata nata abincin. Ita kuma ta kira yara suka baje suka ci nasu abincin. Ta gaya ma mai aiki ta dafa musu taliya su ci tare da mai gadi da yaron gida da zai dinga yi musu wanki da guga sai aiken da ba za’a rasa ba.

Wajajen goma sha ɗaya na dare ta kira Hassan a waya tana numfarfashi da ƙyar wai cikinta na mata ciwo. Kallo Afrah ta bi shi da shi lokacin da ya fita daga ɗakin a ruɗe. Wacce irin rayuwa ce wannan? Haka auren mai mata yake dama? Ko dai ita ce bata yi dace da abokiyar zama ba? Ta fi tunanin haka dan ta san kishiyoyi fin cikin ƴan yatsun hannunta da suke zaune ƙalau. Har ta gama tunane tunanenta yi bacci Hassan bai dawo ba.

*****

Sai bayan sallar asuba Nabila ta samu bacci ya ɗan kwasheta. Ta ji daɗi sosai da Umma ta ce ta bar Hajja ta kwana a wajenta. Da yanzu dole sai ta tashi ta sama mata abunda zata ci sannan ta mata shirin tafiya Islamiyya Duk kuwa da cewa ɗumama mata abincin jiya zata yi wanda Aunty Tala ta ɗiba mata

Wayarta ce ta tasheta daga bacci saboda kiran da ake mata. Ta so ta share amma ƙarar ya hanata bacci. Tana ɗagawa ta ga sunan Hussaini ya bayyana a kai. Tunani ta faɗa a kan dalilin kiran nashi har wayar ta tsinke. Cire ƙarar ta yi dan bata son damu. Tashi ta yi ta shiga wanka ko jikinta ya ɗan yi mata ƙwari.

Tana kitchen tana ɗumama abinci ta ji sallamar mai gidan. Ƙasa ƙasa ta amsa ta ci gaba da abunda take yi. Me ya kawo shi? Ƙin amsa wayarshi da ta yi bai nuna mishi cewar bata buƙatar jin mutyarsa ko ganinshi ba? A nan bakin ƙofar kitchen ɗin ya tsaya yana kallonta. Sarai ta san yana nan amma bata juyo ba dan ko kallonshi bata son yi.

”Nabila”

Ya kira sunanta a hankali. Kasa amsawa ta yi, sai jikinta ya ƙara yin sanyi. Inda take tana juya shinkafar dan kar ta kama ya ƙarasa ya kara kiran sunan nata. Nan ma shiru. Ganin bata da niyyar amsa shi, ya saka hannunshi ya riƙe nata da ke juya abincin. Yanayin da ta shiga ne ya saka ta ƙara matsawa jikin gas cooker ɗin tana cewa

“Um um meye haka?”

Baya ya matsa taku biyu

“Magana nake baki ji ba”

“Ina kwana?”

Hannu ta saka tana jin zafin shinkafar. Jin yayi mata yanda take so ta ɗauko faranti ta juye tare da ɗauko cokali ta raɓa ta gefenshi ta bar kitchen ɗin ta fita falo. Nan ya biyota inda take zaune har ta fara cin abincin.

“Kuna lafiya? Ya Hajja?”

”Kalau”

Ta bashi amsa a taƙaice

“Abinci na zo karɓa.”

Cokalin da ta kai baki ta mayar ta ajiye kan farantin, goshinta na tattarewa, fuskarta na nuna alamun rashin fahimta.

“Abinci? Abincin me kuma. Na ga ba a nan gidan kake ba balle ka ce abincinka na kai na.”

“Ai ke ya kamata ki mana abinci.”

Kai take girgiza mishi. Bata san wannan karatun ba. Yau ko budurwa Hussaini ya aura, wacca bata sani ba kuma suke zaune gida ba zata bata wani abinci ba balle Lawisa da babu abunda zai hanata tashi ta ɗora musu abunda zasu ce. Ko kunya basu ji ba ita zata ba Lawisa maciyiya amana abinci? Ta san dama maza ba kunya ce da su ba. Amma Lawisa? Ashe ita bata ma san Lawisa ba. Ba zata yi mamaki ba idan ma ita ta yi kutin kutin ta san yanda ta aiko shi. Tunda ta aure mata miji babu kunya, to kuwa babu abunda ba zata iya aikatawa ba.

”Wannan magana ba haka take ba baban Hajja. Mun yi da kai zan dafa na baku ne?”

Ta tsare shi da idanunta kamar yanda ya tsareta da shi. Ganin bashi da niyyar bata amsa ya saka ta ɗauki cokalinta ta ci gaba da cin abinci. Har ta gama bai motsa daga wajen ba kuma bai ce mata komai ba. Tana gamawa ta kwashe kwanon ta shiga kitchen ta wanke sannan ta wuce ɗaki ta kwanta ba dan ta yi niyya ba.

Nan ya sameta tana kan gado tana latsa waya. Sakonnin ƴan uwa da abokan arziƙi take amsawa. Tunani take ta kira Safina ta ji yaya ta kwana amma sai ta fasa. Lamarin Safina ne kamar wacca bata san me take ciki ba. Ta kira ta gaya mata abunda ta je ta yi ranar ɗaurin aure. Idan ta rantse Safina bata da hankali to ba zata yi kaffara ba. Gashi bata jin shawarar kowa idanunta sun rufe ruf! Fatanta Allah ya sa dai ba zata yi dana sani ba.

“Ba zaki taimaka ki ɗan mana ko dankali ba Beela?”

Kallonshi ta yi ta ƙara, ita zai yaudara? Harda wani kiranta Beela?

“Nabila dai. Ita matar taka me ya hana ta tashi ta yi? Bata cikin amaren da wani zai tashi ya girka musu.”

“Uhm Nabila, kin gane ko, ina ƙoƙarin saya miki girma da mutunc…”

“Bana so. Bana bukatar na yi ƙima a idanun waɗanda suka ci amanata. Ko da yake baka bani mamaki ba Hussaini. Tun ba yau ba na san na fice maka a rai. Idan ka so ni a da to yanzu baka so na.”

Ganin yana shirin magana ta katse shi.

“Abinci ne bazan dafa na ba Lawisa ba. Yanda kuka zaga ta bayana kuka yi aure, haka zaku bi ku san yanda kuka ci abinci da safen nan”

Juya mishi baya ta yi tana mai ci gaba da danna wayarta dan ta lura shi magana ma yake son yi. Tana jin shi ya rufe mata ƙofa ya fita ba tare da ya bata haƙuri ko ya ƙaryata rashin son da take iƙirarin yana mata ba.

*****

Text ta yi mishi kan cewar zata je duba Aunty Tala ta zame ta gurɗe ƙafarta. Har ta fidda rai kafin can ya kira ta yace sai ta dawo ta kuma gaida ita. Tana shiryawa tana tunanin sabon iyayin da ya tsuro mata. Ko murnar angwancin ke kan shi?

Ta biya ta ɗauko Hajja suka hau ɗan sahu ya kai su ƙofar gidan. Hajja ta shiga wajen yara suna wasa ita kuma ta zauna Aunty na mayar mata yanda aka yi.

“Na rasa wa ya zubar da ruwa Nabila. Ina fitowa daga ɗaki, na ɗauka jiri ke ɗibana ashe zamewa nake. Kinga hannuna har yanzu buguwar da nai bai sauka ba.

Babansu da ke ɗaki ya jiyo salati na ya fito da saurinsa ya gan ni riƙe da ƙafa ashe har kuka nake. Daga baya har cewa yake ni ma na ji abunda ya ji lokacin da na damƙi hannunsa da ina naƙudar auta.”

Ƴan uwa da abokan arziƙi sai zuwa suke suna dubata. Wasu su zo hannu rabbana wasu su bada kuɗi wasu kuma kayan dubiya suke ta kawowa irinsu kayan marmari. Ita Nabila shirin wuni take yi. Bata san lokacin da Hussaini zai dawo ba dan yau zai dawo ɗakinta. Bata jin zata wani iya tarɓarsa. Gida ne dai a gyare sannan abinci ma ta yi na dare kaɗan. Jiya gaba daya bai kira ba kuma bai zo ya duba su ba. Ta yi tunanin ko ba komai zai zo ya gan su tunda dai shi ya ajiye su.

Saƙon waya ma da ta aika mishi dan dai ya zama kamar dole ne. Ta san in dai ya dawo gidan da ƙyar ya barta ta je kuma idan ta je ɗin ma ba zata wani jima ba.

Wayarta ce ta shiga tsuwwa, ta duba ta ga Hussaini. Mamaki ya cika ta, ta amsa tana fatan lafiya.

Tambayarta mai jiki ya yi ta kalli Aunty Tala da ke gaisawa da wasu maƙota da suka shigo ta bashi amsar tana lafiya.

“Um I want to ask you a favor” (Ina son tambayarki wata alfarma ne)

“Dan Allah idan babu damuwa, ko zaki ƙara ma ƴan kwanaki?”

Shirun da ta yi, bai san mutuwar zaune ta yi ba. Sai ya ƙara da cewa

“Zaki iya sayarwa, ko nawa ne zan saya.”

*****

Mai karatu ko Zaki iya saida kwananki? Nabila zata sayar? Ko kyauta zata basu? Ko kuma zata hana?

Wai me Safina ta je ta yi ne?

Ina neman afuwarku na ji na shiru da kuka yi. Life happened.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 10Soyayya Da Rayuwa 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.