Skip to content
Part 10 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Yau ne! Yau ne ranar da mijinta zai auro ƙawarta, maƙociyarta da suka tashi tare. Wacca take ma kallon ƴar uwarta a da. Bata son tashi daga kan gadon. Bata so ta buɗe idanunta ba a yau. Zuciyarta ta yi mata nauyi, saitinsa kamar an ɗora mata wani dutse a kan shi. Sabo ne ya saka ta tashi sallar asuba. Daga kwance ta karanta Azkar ta maida idanunta ta runtse. Daga nan bacci ya ɗauketa.

Sai yanzu ta farka. Saboda bata son dogon tunani ta miƙe ta haɗa ma Hajja ruwan wanka. Shiryata zata yi ta tafi Islamiyya. Auren Hussaini a yau ba zai canza mata tsarin rayuwarta ba. Barinta ta yi tayi sallah ita kuma ta je ta ɗumama tuwon da tayi a daren jiya. Kafin ta gama ta tsara abunda zata dafa da rana. Da dare tsire zata aika a saya mata su ci buredi sai ɗan salad da zata yi musu su kora da ruwan shayi.

Tana fere doya Hajja na cin tuwo tana mata surutu.

“Mimi wai auren Abba za’a yi? Dama bai yi aure ba?”

“Hajja ki daina cin abinci kar ki ƙware. Eh auren Abba za’a yi. Ya yi aure da ni, ƙarawa zai yi. Kar ki ƙara magana sai kin gama cin abinci.”

Sai da ta gama cin abincin ta ce,

“Abba ya nuna min hoton Aunty Wisa a wayarshi. Mai kyau. Na ganta a gidan Mummy dinmu. Nace ma Abba sunanta Aunty Wisa ya ce Aunty Wawisa sunanta. Ita ce Aunty Amarya din?”

Ƙin bata amsa ta yi ta goge mata baki ta riƙe hannunta ta kaita Islamiyya da kanta ta dawo. Bata sani ba ko su Habiba zasu je Islamiyyar yau tunda ana bikin yayyensu.

Bayan ta dawo ta ci abinci ta kintsa kwanuka ta nufi ɗaki dan ta yi wanka. Ta gefen idanunta ta ga fitowarsa daga ɗakinsa ya sha shaddarsa sai maiƙo take yi. Abunda ya tsaya mata a wuya ya saka ta kasa gaida shi, ta wuce cikin ɗaki. Shi kuma ya biyo ta.

Ganin ya cika mata ɗaki da ƙamshin turare ya saka zuciyarta ƙara matsewa. Babu abunda ya dameshi ya shirya zai tafi wajen ɗaurin aurenshi da ƙawarta Lawisa. Surutun Hajja na ɗazu ya dinga dawo mata.

“Nabila.”

Sauri ta yi ta shiga banɗaki ta rufo ƙofa tana maida numfashi kamar wacca ta yi tsere. Nan da nan hawaye ya wanke mata fuska. Nan dan ɗan lokaci Lawisa zata aure mata miji. Lawisa. Kaf matan duniya babu wacca ta ƙyalla idanu ta ga Hussain sai Lawisa. Sai da ta yi kukanta ma’ishi sannan ta tashi ta yi wanka. Tana fatan ace Hussaini ya bar mata ɗakin.

Cikin sanyin jiki take shafa mai. Ɗinki zata je ta yi ko ya ɗauke mata hankali daga tunane- tunane. Matsalar bata da kayan ɗinki kuma bata gaya ma Hussaini zata fita ba balle ta je ta saya. Sai ta ɗauko wata atamfa mai sauƙin kuɗi. Doguwar riga zata ɗinka mara hayaniya. Ko zaman gidan sai ta dinga yi da shi.

“Wai ko basa nan ne masu gidan?”

Abunda ta jiyo kenan. Ta san muryar amma a lokacin ba zata ce ga mai muryar ba. Hijabi ta ɗauko ta saka tana saurin fita ta duba. Mutane huɗu ta gani a falon. Kannen Mummy ne guda uku sai wata ƴar uwarta da ke sa’arta. Nan take zuciyarta ta yi mata sanyi ta fara sakin murmushi. Sannu da zuwa ta yi musu tana nufar kitchen dan kawo musu ruwa.

“Ke je ki shirya ki fito. Gidan ai ba baƙonmu bane.”

Cewar Aunty Talatu tana cire mayafinta tana ƙare ma gidan kallon da murmushi a fuskarta. Dama Nabila ta gaya mata abunda ya faru. Ƴar uwarta ta biyota ɗaki.”Dannen ƙirji muka zo yi. Sauran dangi ma na nan tafe.”

Dariya Nabila ta yi tana girgiza kai. Sai da Hafsa ta ajiye wata jakar matafiya a kan gadon ta lura ma da abu a hannunta ashe.

“Ɗinkuna akai miki. Aunty Tala tace ki saka leshin nan farko.”Murmushi Nabila ta yi tana jin ƙwalla na tarar mata a idanu. Ƙwalla ne na farin ciki da godiya ga ubangiji. Tana da ƴan uwa masu so da ƙaunarta. Hakan yana rage mata raɗaɗin rasa soyayyar miji.

Shiryawa tayi, Hafsa ta ɗan yi mata kwaliyya ta fito ta ƙara yin fes abunta ta shiga cikin ƴan uwa. Kafin ka ce kwabo, gidan ya cika da ƴan uwanta ta wajen Mummy da Daddy. Harda guzurin abincinsu. Gaba ɗaya sai ta ji wannan nauyin zuciyar da ta tashi da shi babu.

Wajajen la’asar Habiba ta shigo da saƙo daga wajen Hajiya Mama. Wai ta shiga a ɗauki hoto da ita amarya ta zo. Har ta juya ta tafi babu wanda ya iya cewa komai. Bayan wasu daƙiƙai, sai aka ci gaba da hira. Babu wanda yace ma Nabila ta tashi ta je kiran da ake yi mata. Hakan sai yayi mata daɗi dan ko an ce ta je ɗin, laɓewa zata yi ba zata je ba.

Duk da anyi mata shara an gyare gidan, ta tashi ta sassaita filallukan da ya ƙara ƙawata kujerun dake falon. Tana ƙoƙarin shigewa ɗaki ya shigo da sallamarsa. Cak! Ta tsaya. Kasa juyowa tayi saboda zuciyarta da ke bugawa fat! Fat! Ta samu ta amsa mai amma bata tunanin ya ji dan muryarta kaɗan ta fito.

Ƙamshi yake zubawa wanda tana shaƙa wani abu wanda bata san ko meye ba ya tsaya mata a maƙoshi. Ƙarasowa yayi inda take a hankali. Ƙamshin turarenshi ya guaraya da ƙamshin gasashen nama. Hannunta ya riƙo ya jata zuwa teburin cin abinci ya zaunar da ita. Kwabar jera farantai ya buɗe ya ɗauko faranti. Ya baje mata gasashiyar kazar hausa da ya saya a can unguwar mahaifanta.

Tare suka ci, wanda ita ta fi shi ci. Bata ci rabi ba tace ta koshi. Ya zuba mata idanunsa “Me kika ci har?”

“Mun ci abinci tare da Aunty Tala”. Ta rasa dalilin da ya sa muryarta ta koma mai sanyi ta shagwaɓaɓɓu.

Ya ɗauki lemu ya bata ta sha sannan ya kaita ɗaki. Wanka ya jirata tayi wanda bata tsaya dogon tunani ba dan ta san yana nan. Ta saka turarenta daga bayangida wanda ya zame mata jiki sannan ta fito.  Ƴan riga mai kauri ta saka iya gwiwa ta saka hula a ka. Sai da ya lulluɓa mata bargo sannan ya kashe mata fitila.

“Sleep tight”

ya faɗa yana mai rufo mata ƙofa.

Bacci duk satarsa, nan ya barta. Shirun dare da kukan gyare su suka cika mata kwanya. Cikin dare aka ɗauke wuta dan haka zafi ya isheta. Tashi tayi ta buɗe tagogin ɗaki. Kasa kwanciya tayi tana tuna shekaru kusan takwas da suka wuce. Lokacin da aka kawota wannan gidan.

Tunowa tayi yanzu haka yana can wajen amaryarsa yana kwasar gara. Yanda suka kasance a darensu na farko ne ya zo mata. Sai ta ji wani kuka ya suɓuce mata. Ta saka hannu ta rufe bakinta gudun kar wani ya jiyota. Maƙiya suyi mata dariya har a goranta mata da safe. Dannan ƙirjin da akai mata ɗazu bai amfana mata komai ba. Sai yanzu ƙirjin nata ya kumburo ya fito ya tarwatse gaba ɗayansa!

Wani ciwon duk abunda zaka yi mai sai ka ji zafinshi. Komai dauriyarka komai jarumtarka sai kayi mai kuka. Ko da kuwa a ina ne. Ta san idan ta ɗauko Qur’ani ta karanta zata ji sassauci amma bata son ciwon ya sassauta mata. So take ta ji shi sosai. So take yayi mata illa idan da hali yayi ajalinta.

Wa yace kishiya tana da daɗi? Ina wacce take jin idan an yi mata kishiya ko a jikinta? Fada kawai take yi. Kishiya ko da mahaukaciyace bata da daɗi! Bata taɓa tunanin zata yi kuka ba, bata taba tunnin zata shiga damuwa ba. Yau gata tana kuka da idanunta ba dan an yi mata wani rashin adalci ba. Ba dan an nuna mata rashin so ko kulawa ba. Kawai saboda ta san mijinta yana tare da wata. Kishiya bata da daɗi.

Haka nan ta zauna ta saka hannu ta rufe bakinta tana gurzar kuka. Wuta aka kawo ta ƙure fanka ko dan ya tafi da sautin kukan da take yi. Ta janyo window ta rufe amma bata cire hannunta daga bakinta ba domin tana tsoron kar a jiyota.

A kunnen Nabila aka soma kiraye kirayen sallar asubahi. Alwala tayi ta soma jera nafulfuli tana rokon Allah ya bata ikon tunkarar rananr gaba ɗayanta ba tare da bugawar zuciyarta ba.

*****
Daurewa kawai take yi. Yaƙe kawai take yi ana hotuna. Bayan ƙuncin da ta shiga jiya, ƙarfin hali take yi kawai. Ba dan kishiyarta ta fi ta kyau ba, ba dan an yi wani abu da ta ɗauka cin fuska bane a wajenta.

Ita kanta bayan ta gama shiri ta kalli kanta a madubi ta san cewa ta haɗu. Ta gode ma Allah da baiwar kyawun da ya yi mata. Ga kuma iya ɗaukar wanka. Motoci uku suka cika ita da ƙawayenta waɗanda suka taso unguwa ɗaya sai wasu da ta yi bayan aure.

Waƙar uwargida na Shaba aka buƙaci DJ ya saka a yayin da suke shigowa. Tafiya suke yi na ƙasaita, na manyan mata. Ga walwali suna yi. Kowacce ta yi kwaliyya ta kece raini. Suka ƙarasa tsakiyar fili suka tsaya. Nan suka fara yi ma Safina liƙin kuɗi. MC ya fara koɗa uwargida kasancewar duk kuɗin liƙin nashi ne shi da DJ. Magana a bakinshi kamar numfashinsa zai ɗauke.

Suka nemi waje suka zauna aka kawo musu abinci. Da Safina ta ɗaga idanu ta hango Hassan ɗinta zaune da ƙwailar yarinyarcan sai ranta ya ɓaci. Amma haka ta cije tana yaƙe.

Bayan an kira amarya da ango, sai aka kira uwargida. Safina ta ɓalle bakin jaka tana liƙa musu kuɗaɗe. Hassan bai kunyatata ba, shi ma ya dinga zaro kuɗi daga cikin babban riga yana liƙa mata. Kafin ka ce wani abu, sai ƙawayen Safina suka zagaye su suna musu liƙi. Abun mamaki, amarya tana gefe daga Hassan sai Safina a tsakiya. Har ya ranƙwafo yana raɗa mata irin kyawun da ta yi. Ta saki tafin hannayenta ta rufe idanunta alamun ta ji kunya.

Basu tsaya an tashi taro ba suka tafi. Suka ajiye wasu a hanya. Aisha Tee ce take tuƙa motar. Maganar da ta gaya mata ne ya saka ta a matsananciyar damuwa. Shi yasa ma tana jin dawowar Hassan ta yi maza ta hau baccin ƙarya.

Suna gama hotuna ya wuce ɗaurin auren dan ya so ya yi latti ma saboda sanaben da Safina take ta yi. Yana ficewa ta kira Aisha Tee ta ɗauketa suka fita inda zasu je suka dawo.

*****
Guɗar ƴan kawo amarya sai da ya haddasa mata faɗuwar gaba. Ji take wani mummunan abu ne ya kusantota. Wani irin jiri take ji, bata jin daɗin jikinta. Nan ta fara karanto addu’o’i na neman tsari.

A falon Hassan suka zauna saboda tana tsoron kar a ɗauko wani mugun abun a saka mata a nata wajen a cuceta. Gabab ɗaya abubuwan da aka faɗa duk bata ji su ba dan ƙwaƙwalwarta ta tafi wani lissafin na daban.

Ta shirya tsaf cikin wasu kayan bacci masu ɗaukar hankali, wanda ta san Hassan yana so. Ga ƙamshin turarukan da ta san suna kiɗima shi. Ta zauna kan kujera a falonta tana canza tasha. Bata kalle shi ba ta amsa sallamarsa. Kusa da ita ya zauna yana ta buga murmushi. Ya riƙe hannunta ta ƙwace.

“Hakan bai kamata ba, kar mu shiga hurumin da ba namu ba.”

Ya langwaɓar da kan shi.

“Hannunki fa kawai na riƙe.”

Ya miƙo mata leda ya yi mata sai da safe.

“Tunda kin kore ni.”

Ta so ta ce mishi ya dai kori kan shi amma ganin irin kallon da yake mata sai ta ji haushin da ya bata babu shi. Ya yi mata sallama ta buɗe kaza ta ci, sauran ta ajiye ma yara. Ganin babu sauran amfanin zamanta a nan ya saka ta kashe kayan wuta ta nufi ɗakinta.

A nan aka samu matsala. Mugun sabon da Hassan ya yi mata ya fara damunta. Bata saba bacci ita ɗaya ba. Dan haka ta je ta ɗauko dukka yaran uku ta kwantar a kan gadon. Hakan bai yi mata ba. Kawai hoton Hassan take ganowa yana kwance ƙwaƙume da wata ba ita ba. Da sauri ta tashi ta fita ta nufi hanyar da zata kaita wajen Afra.

Zata iya cewa kamar a mafarki ne ko kuma bata san yanda aka yi ba sai tsintar kanta ta yi tana bubbuga ƙofar da ta murɗa ta ji ta a kulle. Bugu ba na wasa ba, irin mai nuna emergency ɗinnan.

“Waye?”

Muryar Hassan ta jiyo daga ciki yana doso ƙofar.

”Hassan, Ni ce ka buɗe dan Allah”

Cikin hanzari yake kokawa da mukullin saboda a tsorace yake yana tunanin babu lafiya.

“Ƙoƙarin buɗewa nake yi hakuri.”

Yana buɗe kofa ta gan shi sanye da vest da gajeren wando, jiri ya ɗebeta saboda tashin hankali ta tafi luu zata faɗi. Ƙoƙarin riƙota ya yi amma kasancewar bai shirya ba sai da ta kai ƙasa ta zauna. Ya tsugunna a gefenta yana tambayarta lafiya.

Saboda sharrin kishi ji ta yi yana kamshin wani turare na daban. Ƙwalla ya cika mata idanu sai hawaye.

“Zaki iya tashi?”

Bata bashi amsa ba sai ma kokarin kwanciya da take yi a ƙasa.

“Hassan jiri, kai na zai juye. Zan faɗi.”

A zahirin gaskiya babu wani jiri da take ji. Kawai dai tana son shiga rayuwarsu ne a yau.

“Sannu”

Abunda ya ce mata kenan yana ɗagota a hankali. A jikinshi ya kara ta suka shiga cikin falon Afra. Ya zaunar da ita a kan kujera tana maida numfashi. Kwanciya ta yi a kan kujerar tana ƙarewa falon kallo. A zuciyarta ta ayyana nata ma ya fi wannan kyau tana buga ma kayan wajen harara.

Ruwa Hassan ya kawo mata na roba mai sanyi ya taimaka mata ta sha. A nan ne aka buɗe ƙofa Afra ta fito sanye da hijabin ta har ƙasa. Jin Hassn shiru ne ta leƙo ta ga Allah ya sa lafiya. Ganin Safina kwance a kan kujerarta ya saka ta yin turus ta tsaya a bakin ƙofa.

“Bata da lafiya ne. Har faɗuwa ta yi.”

Abunda ya ce mata kenan da ya ganta a tsaye. Ya juya yana ma Safina sannu. Ita kuma ta lafke a jikinshi tana nuna mishi kirjinta alamun zafi yake yi mata. Ya tambayi Afra ko tana da maganin ulcer tace bata da shi ta koma ciki ta yi kwanciyarta. A gajiye take, ta gane sarai abunda Safina take yi. Bata da lokacin ɓatawa a kan ta a yau, hutu take buƙata.

Dakin Safina ya je ya ɗauko mata magani ya bata ta sha. A hankali numfarfashinta ya ragu.

“Zan sha Tea Hassan. Kazar nan ce akwai maiƙo da yaji.”

Babu musu ya haɗo mata madara ya zauna yana bata a cokali tana sha. Ta sha rabi ta kuma kwanciya tace ta gaji zata huta. Sun fi ƙarfin awa guda a falon nan kafin Safina ta haƙura ya raka ta ɗaki yana jadadda mata ta kira shi idan ta ji wani abun kuma.

Da ya samu Afrah ta yi bacci sai shi ma ya kwanta amma hankalinsa gabaɗaya a tashe yake yana wajen Safina. Bayan ɗan lokaci ya kira wayarta ya ji bata amsa ba sai ya tashi ya je ya dubata yaga tana kwance bata dai yi bacci ba. Ta ce mishi ƙirjin ne yana mata zafi kaɗan amma kada ya damu zata ji sauki.

Anya hanyar da Safina ta ɗauko mai ɓullewa ce?

Hussaini angon Wisa Wise, ko yaya zata kaya?

Mu haɗu a comment section.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 9Soyayya Da Rayuwa 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.