Skip to content
Part 12 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Kallon Safina da ke ta cije baki yake yi. A ɗofane take a kan kujera sai runtse idanu take yi. Gabaɗaya kan sa a juye yake ya rasa gane me ya faru. Mutum ɗayan da suka tarar kuma suke jira, ji ya yi kamar ta fi sa’a guda cikin ɗakin likita.

Murmushi matar ta yi musu bayan ta fito. Da sauri ya tashi ya tura kujerar tura marasa lafiya da aka basu da suka shigo asibiti saboda kasa tafiyar da Safina ta yi. Dama ko a gida ma shi ya ɗauketa ya kai ta mota.

“Me yake damunki Madam?”

Likitar mace ce wacca idan bata yi hamsin ba to ta kusa. File ɗin Safina take dubawa.

“Um bleeding ta yi”

Hassan ne ya bata amsa

“Tana da ciki ne?”

Hassan ɗin shi ma Safina yake kallo wannan karon wacca ke girgiza kai tana cije leɓe. Ita kaɗai ta san abunda take ji.

Likitan ta taso, tare da taimakon Hassan suka ɗorata a kan gadon duba marasa lafiya. Safar hannu likitan ta ɗauko tana duba Safina. Abunda ta gani ne ya saka ta kallon Hassan.

“Ita ce Safina Hassan? Haihuwarta uku kuma?”

Duk gyaɗa mata kai Hassan yake yi. Safar hannun ta cire ta saka a bola sannan ta koma kujerarta ta zauna

“Ɗinkinta ne ya lalace”

Kallon rashin fahimta yai ma likitar. Ɗinkin me? Su da suka zo asibiti me ya kawo zancen ɗinki kuma

“Ban gane ba”

Biron hannunta ta ajiye tana kallonshi kafin ta ce

”Ɗinki aka yi mata a gabanta. I’m guessing wajen bai warke ba or something kukai copulating ya lalace”

Sai da ya yi dogon nazari kafin ya gane me likitan ke nufi. Waya take yi tana ce ma wasu ta waya su zo akwai wani case da zasu duba. Ya juya ya kalli Safina da ke kwance kan gadon. Ya rasa gane dalilin yin ɗinkin Safina. Ba sai an haihu ake ɗinki ba?

“Doctor ina ganin kamar kin yi mistake. Ai bata haihu ba balle a yi mata ɗinki”

Murmushi ta yi masa

“Wasu matan sukan zama loose sai an yi musu ɗinki. I think that’s the case. Ai da kun bari an tabattar wajen ya haɗe tukunna”

Girgiza mata kai ya yi

“Aa wallahi ba wani loose she’s…”

Bai ƙarasa ba saboda nauyin da maganar ta yi masa a baki. Sai ya basar ya ce

“Lafiyarta fa ƙalau Doctor”

Ta ce mishi bari sauran likitocin su iso. Leƙawa waje ta yi tai magana da wasu ma’aikata sannan ta dawo. Babu jimawa wani likitan ya shigo. Suka ƙara duba Safina suka yi maganganunsu na likitoci. Jim kaɗan wani ma ya kuma zuwa. Da ƙyar suka samu Safina ta tabattar musu da cewa eh lallai ta je an mata ɗinki domin ta ƙara matsewa.

Aisha Tee ce ta bata wannan shawara ta yin ɗinkin da sukai ma laƙabi da ‘Back to virgin’.

“Wallahi kika yi shi, sai ya kasa bambancewa tsakaninki da budurwar matarsa. Ai dama abunda ake yi ma kenan. Kuma har ta saki ke kina nan zam zam!”

Washegari kuwa ta bita suka je wani private asibiti aka yi mata dinki. Ita kanta ta ji a jikinta irin ɗinkin da akai mata. Safina tana da ƙan jiki. Amma sai ta yi tunanin tunda ba ɗinkin haihuwa bane, nan da nan zai warke. Sai aka samu akasi.

Ta san abunda ta shirya shi yasa sai da ta bari yara sun tafi makarantar Islamiyya sannan ta ja hankalin Hassan. Bata san cewa haƙarta ba zata cimma ruwa ba.

Kasa kallon Hassan ta yi. Tun a ofishin likita bai ce mata komai ba har aka bata ɗaki ta kwanta. Likitocin sun ce aiki za’a yi mata sannan sun yi mata allurar kashe zafi. Yanzu haka allurar ta saketa amma tana ɗan jin ciwo kaɗan. Yanzu ma idanu ya zuba mata sai dannan waya yake bayan ya kira mahaifiyarta yace suna asibiti. Bai gaya mata abunda ya sa aka kwantar da ita ba.

Haka nan suka zauna shiru har ta ƙaraso. Fita ya yi ya basu waje dan su tattauna.

“Wai ba zaki gaya min me ya same ki ba?”

Sai da ta ga ran ta ya ɓaci sosai ta ɗau zafi zata tafi sannan ta iya labarta mata abunda ta aikata. Salati Umma ta yi ta sanar da ubangiji

“Kinga abunda kishinki na banza ya janyo miki ko? Kina zaman zamanki kin janyo ma kan ki jinya. Ke yanzu ba abun kunya bane kishiyar taki ta tambayeshi abunda ya faru ya gaya mata? Babu abunda zai hana ta yi miki dariya kuwa”

Kuka Safina ta saka. Bata ma kawo tunanin hakan a zuciyarta ba. Roƙon Umma ta dinga yi kan ta kira mata Hassan. Da ƙyar da suɗin goshi ta yarda ta kira mata shi.

“Dan Allah dan annabi Hassan kar ka gaya ma kowa abunda ya faru. Kaga daga ni sai kai sai Umma da likitoci muka sani. Ka riƙe min sirri na ka ji Hassan”

Hannayensa sarƙafe a kan ƙirjinsa yana kallonta. Haushinta kawai yake ji.

“An gaya miki ni mahaukaci ne irinki da zan iya buɗe baki na faɗi wannan ɗanyen aikin da kika aikata ma kanki?” Tsaki ya ja ya fice daga ɗakin ita kuma ta fashe da kuka.

Zama ya yi ya jira aka yi musu bill ya biya. Washegari za’a yi mata aikin. Idan sun ga sauƙin jikin nata sai su sallameta. Komawa ya yi ya gaya ma Umma abunda ake ciki. Ita kaɗai suka bari suka koma gida dan shiryawa.

Afrah ta yi mamaki da aka ce aiki za’a yi ma Safina. Ashe rashin lafiyar gaske take yi. Sai ta ji babu daɗi a ranta dan batai mata kyakyawan zato ba. Ta so zuwa ta dubota amma Hassan yace ta bari sai washegari bayan an yi aikin sai ya kai ta. Nan ya danƙa yara a hannunta ya fita dan yin sayayya sannan zai koma ya ɗauko Umma su koma asibitin.

“Idan kin ga dama an tambayeki aikin me akai miki ki gaya musu gaskiya. Ni appendix zan ce an cire miki.”

Ko da ya dawo ya kawo musu abincin dare bai shigo ba. Yara da masu aiki ya ba suka kai musu. Basu yi minti goma a cikin ɗakin ba suka fita dan yana jiransu a mota ya mayar da su gida.

*****
A falo ta same shi zaune yana kallo. Tunda ya shigo yake ta wani muzurai. Gaisuwarta ma a ciki ya amsa mata. Ko Hajja bai kulata kamar yanda ya saba ba.

“Kai nake ta jira kuma ka dawo baka ce komai ba gashi dare yana yi”

Kallonta ya yi cikin rashin fahimta. Ɗazu katse mishi waya ta yi alamun bata yarda ba. Ran shi ya ɓaci a kan abubuwan biyu

“Nabila bata da matsala, zata yarda”

Abunda Lawisa ta gaya mishi kenan lokacin da yake wasuwasi a kan kiran Nabila. Abubuwan da Lawisar ta fara yi mishi ne ya saka shi kiran Nabila.

“Ta kashe wayar, bata yarda ba.”

Shiru suka yi daga shi har Lawisar suna kallon juna. Fuskarta abar tausayi. Sai anjima suke saka ran zata yi wankan musulunci. Ko da zai tafi gidan Nabila sai da Lawisa ta yi kuka. Kafin ya shiga gidan ma suka yi waya take gaya mishi murya a sanyaye cewar ta yi wankan ba da jimawa ba. Ji ya yi kamar ya koma.

“Ka ce na sayar maka da kwana ko ka fasa?”

Gyara zamansa ya yi, wani abu kamar farin ciki na ratsa shi

“Na ɗauka ba zaki sayar ba.”

“Ina cikin mutane ne ba zamu iya maganar ba a lokacin. Kwana nawa kake so a sayar maka? Kuma nawa per kwana?”

“Ke zaki faɗa. Kwana ɗaya”

“Ka bada fifty thousand”

Murmushi ya yi mata

“Fifty bai yi tsada ba?

“Ai na ɗauka amaryaryar take mai tsada ce.”

Ƴar ciniki suka taɓa ta yi mishi ragin dubu goma. Ya ce zai bata da safe ta ce bata san zance ba. Ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa. Nan ya yi mata tiransfa ɗin dubunta arba’in

” Na ƙara muku kwanaki, sai ta cika sati ka dawo. That’s my wedding gift to you (wannan shi ne kyautar auren naka daga wajena)”

Jiki a sanyaye ya tashi ya yi mata sallama ya tafi. Ta kulle gida ta je ta kwanta.

Bata yi niyyar sayar mishi da kwananta ba. Tun tana wayar Aunty Tala ta lura da ita. Sai da baƙin nata suka tafi take tambayarta me ya same ta shi ne take faɗa.

“Meye a ciki? Ki sayar mai da shi”

Sakin baki ta yi tana kallon Aunty Tala a mamakance. Sai kace bata san zafin kishi ba

“Haba Aunty Tala, wannan ai cin fuska ne.”

Ta fashe da kuka mai cin rai

“Me yake nufi? Ni bashi da buƙatata sai dai ita? Kenan ta fi ni komai da komsi?”

“To ko kece kika yi sabon abu Nabila ai kakan ɗan ba tsohon sarari. Kwana nawa ne ya gama ɗokin amaryar ya dawo gare ki?”

Nabila ta goge hawaye daga fuskarta, murya a sanyaye ta ce

” Ni dai bana so. Zuciyata ba zata iya daurewa ba”

Kafaɗa Aunty Tala ta ɗaga cikin nuna damuwa

” Da zaki bi shawarata, da kin sayar mishi. Idan ya zo ma amfanin me zai miki? Karshe ma idan baki yi sa’a ba ke za’a bari da mummunan ɓacin rai. Nuna mishi baki damu ba, kuɗi sun fi shi. Baya gabanki. Idan ma dan a ɓata ranki aka yi to ki tura musu aniyar su. Zoben gwal ɗina na fari da kuɗin saida kwana na saye shi. Kar ki yi biyu babu uku bata gyaru ba”

Kamar ba zata iya ba. Amma sai ta yi tunani. Ko da ya kawo kanshi, babu abunda zata iya tsinana mishi saboda zuciyarta babu daɗi. Da babu ai gwanda babu daɗi. Kuma raba mugu da makami ibada. Dan haka ta yanke hukuncin amshe kuɗaɗenta. Kuma ta amshe. Ko faɗuwa kuɗin suka yi bata jin tana da asara.

*****

Ranar Lahadi ta shirya zuwa duba Safina da aka yi ma aiki. Ta haɗa kayan abinci cikin ƙaton kwando ta saka mai gadi ya tarar musu ɗan sahu ta saka Hajja a gaba suka tafi asibiti.

Safina na zaune kan gado tana kurɓar shayi. Umma na daga kan kujera a ɗakin tana jan carbi. Gaisawa suka yi suka shiga hira. Ta zuba ma Umma farfesun kifin da ta yi tana sha.

“Ƙawarki bata da hankali”

Abunda Umma ta faɗa kenan tana fitowa daga banɗaki bayan ta wanke hannunta.

“Da fatan ke ma ba ɗinkin kika je kika yo ba”

Dariya Nabila ta yi. Safina ta yi mata maganar ranar dinner ɗin su Hassan tace ba abunda zai sakata wani ɗinki ana zaune ƙalau. Bata manta na haihuwar Hajja da aka mata ba. Ko da ta ji appendix aka cire ma Safina ta kira Umma ta zayyane mata gaskiyar abunda Safinar ta aikata.

“Kishin banza kishin wofi. Wallahi ku saka ma zuciyoyinku salama. Kar ku kashe kawunanku a kan mazan nan da basu da tabbas. Yau wani mugun ciwon ya kama ki ko kika mutu babu abunda zai hana shi ci gaba da rayuwarsa. Kila kafin ki yi arba’in ma ya dallo wata dalelliyar budurwar”

Ita dai Safina sai murmushin yaƙe take yi. Ita ta san abunda ke damunta. Ga ciwon jikinta ga na zuciya. Ɗazu da Hassan ya jero da Afrah sai da zuciyarta ta kusa daina bugawa. Ita tana nan kwance a kan gado su kuwa sai baza soyayya suke yi. Da Umma ta tashi ta bar wajen har wani leƙa wayar da Afrah ke dannawa yake yi yana mata magana ƙasa ƙasa ita kuma munafukar na murmushi. Dama a kwance take dan haka ta ja mayafi ta rufe fuska tana zubar ƙwalla. Har suka tashi suka fita bata buɗe fuskarta ba.

Umma ma da ta dawo ta yi banza da ita kuma sarai ta ga hawayen nata. Sai taɓe baki ma da tayi ta ce

“Duk tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ke duka”

Magana wannan Hassan baya yi mata. To yaushe ma ya zo? Tana buƙatar kulawarsa. Tana kewarsa sosai. Da yanzu da shi za’a yi jinyar nan. Idan ba dole ba bazai fita daga ɗakin ba. Da Umma ta kore shi ya fi sau a ƙirga saboda damun da zai dinga mata amma bazai fita ba.

“Umma ki mata a hankali dan Allah.”

“Na ji abincin da yaji Umma ba zai dameta ba ko?”

“Yanzu da wannan ruwan zaki mata wanka? Idan fatarta ta kwaye fa?”

Ta tambayi Umma wayarta take cewa bata sani ba ta bari idan Hassan ya zo ta tambaye shi. Amma wannan Afrah ta yi bake bake. Dan rashin mutunci ma ai tana gani mahaifiyarta ta basu waje ita ba zata yi hankalin tashi ba. Duk abunta ba zata shiga tsakninta da mijinta ba. Ita da Hassan nan gani nan bari wallahi.

Ƙwanƙwasa ƙofa aka yi aka buɗe aka shigo da sallama. Hussaini ne, bayanshi kuwa Lawisa ce. Suka gaida Umma suka tambayi mai jiki.

Tun lokacin da Safina ta zo gida ta yi mata ɗiban albarka bayan ta san cewa ita ce amaryar Hussaini basu ƙara haɗuwa ba. Ko a da, tana shakkar Safina balle yanzu da ta zama Hajiya matar Alhaji. Tana basarwa ta amsa sannun da tai mata. Sai ta yi shiru, bata iya yi ma Nabila magana ba saboda muguwar kunyarta da ta ji ya lulluɓey. Ba ta yi tunanin zasu haɗu nan kusa ba sannan bata yi tunanin zata ji abunda take ji a yanzu ba.

Shi kan shi Hussaini a ɗar ɗar yake. Ya ɗauka ta riga da ta zo ta duba Safina har ta koma gida dan da ya fita da safe ta yi wanka ta shirya. Sai satar kallonta yake yi tana danna wayarta. Hajja na zauna kusa da shi tana ta yi mai surutu yana ƙoƙarin bata amsa. Ji ya yi rashin gaskiyarsa da rashin kyautawarsa sun ɗaure shi tamaumau. Tashi ya yi ya riƙe hannun Hajja suka fita.

Har ya je ya dawo babu wanda ya yi ma wani magana a ɗakin. Lawisa kunya ya rufe bakinta. Nabila kuwa zuciyarta ke tafarfasa. Safina halin maza ke mata yawo a kai yayin da Umma ke gyangyaɗi tana jan carbi da ya zame mata ɗabi’a.

Sannu ya ƙara yi ma Safina ya ce mata zasu wuce gida. Lawisa ta tashi ita ma ta ce

“Allah ya ƙara sauƙi”

A ciki Safina ta amsa. Sai Umma ce ta amsa da fara’arta tana yi musu godiya. Hussaini ya kalli Nabila

“Mu je muma gidan zamu wuce Lawisa zata gaida su Hajiya Mama”

“Da kai ka kawo ni? Bana buƙata”

*****

Gaskiya dai ba shi ya kawo ki ba Hajiya Nabila

Su Safina Allah ya ƙaro sauƙi

A daure a yi like da comment

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 11Soyayya Da Rayuwa 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.