Banda ƙaran tukwane babu abunda ke tashi daga kitchen ɗin. Hakan na nuna halin da zuciyarta ke ciki. Girkin rana take son dorawa amma tana huce haushin da zuciyarta ke ciki.
Tun jiya ya kamata Hussaini ya dawo gidanta amma babu shi babu dalilinsa. Zuwa dare da bai dawo ba ta kira shi, niyyarta idan ya dauka, tace Hajja ke son magana da shi. Jiya da ƙyar ta iya bacci saboda tunanin halin da yake ciki. Gashi bata son kiran kowa balle ta daga musu hankali. Ta kasa bari ƙarfe goma na safe ta yi ta nufi cikin gida ko. . .