Skip to content
Part 14 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Banda ƙaran tukwane babu abunda ke tashi daga kitchen ɗin. Hakan na nuna halin da zuciyarta ke ciki. Girkin rana take son dorawa amma tana huce haushin da zuciyarta ke ciki.

Tun jiya ya kamata Hussaini ya dawo gidanta amma babu shi babu dalilinsa. Zuwa dare da bai dawo ba ta kira shi, niyyarta idan ya dauka, tace Hajja ke son magana da shi. Jiya da ƙyar ta iya bacci saboda tunanin halin da yake ciki. Gashi bata son kiran kowa balle ta daga musu hankali. Ta kasa bari ƙarfe goma na safe ta yi ta nufi cikin gida ko zata samu labari a kan Hussaini. Sai ta ga kowa na walwala alamun dai lafiya ƙalau.

Zuciyarta ta shiga ƙuna. Wulaƙancin ya kai inda ya kai. Idan so yake ya ƙara zama gidan Lawisa ai sai ya kira ya gaya mata. Hawayen ɓacin rai ya dinga sukar idanunta amma ta ƙi barinshi ya sauko. Ba dai ita ta yi kuka a kan Hussaini da Lawisa ba. Ta yi ƙoƙarin hawa keke ko zata samu abunda zai ɗauke mata hankali amma zare ya dinga tsinke mata. Shi ne ta shiga dan ɗora abincin rana.

Babu irin tunanin da bata yi ba a kan hukuncin da zata yi ma Hussaini idan ya dawo ba. Ta yi tunanin ta hada mishi kayansa gaba ɗaya tace ya tafi ta sallamawa Lawisa shi. Ta yi tunanin ma ba zata bar shi ya shigo gidan ba. Ƙatuwar tukunya ta cika da ruwa ta dora a kan wutan ba dan ta san abunda zata yi da shi ba. Kila kafin ya tafasa, zuciyarta ta fara sanyi.

Hussaini ta gani zaune a kan kujera mai cin mutum daya, ya jefa kan sa baya. Alamun gajiya ta gani a tattare da shi.

“Me kwanuka suka miki kike ta gwara su?”

Yi tayi kamar bata ji shi ba ta nufi hanyar ɗakinta, ranta na ƙara ɓaci. Ya shigo zai nuna mata kamar babu abunda ya faru, kamar bata isa a nemi afuwarta ko a yi mata bayani ba. Alwala ta yi ta fito ta ɗauki Alqur’ani mai girma tana karantawa, sautin muryarta na fitowa ƙasa ƙasa.

Waje ya samu ya zauna yana sauraronta. Jin bata da niyyar tsayawa ya saka shi dakatar da ita a lokacin da ta kai karshen sura. Rufewa ta yi ta kalle shi kafin ta tashi ta maida Alqur’anin ma’ajiyarsa.

“Lawisa bata da lafiya an yi admitting dinta shi yasa kika ji ni shiru. Ciki ne da ita”

Bata san dalilin da yasa gabanta faɗuwa ba. Ta san ba abun mamaki bane tunda ta riga da ta yi tunanin faruwar hakan ko ba dade ko ba jima. Ba haushi ta ji ba dan Lawisa ta samu ciki. Halin da take ciki ta tuna.

Wasu samun ciki baya yi musu wahala. Bata cikin waɗannan mutanen. Kafin ta samu ciki sai ta ji a jikinta. Sai ta dinga zaryar asibiti, sai ta dinga shan magunguna.

Kafin ta samu cikinta na farko, kullum tamkar tana kan gajimare. Tana waje kamar bata wajen. Tamkar a wata duniyar take ta daban. Sai ta samu ciki, abubuwa suka fara daidaita. Kwatsam sai cikin ya ɓare.

Ta dauka ciwon marar da take ji ba abun tada hankali bane tunda yakan yi mata loto loto. Ranar bata yi aikin komai ba. Bata kai ga ɗora abunda zasu ci da safe ba. Wanka kawai ta yi ta fito tana neman kayan da zata saka ta ji ɗumi a jikinta. Tana dubawa ta ga jini. Daga nan inda take tsaya ta kira Hussaini. A lokacin basu raba ɗaki ba. Bashi da magagin bacci dan haka ya buɗe idanunsa yana tambayarta abunda ya faru.

A gigice ya tashi jin abunda ta gaya mishi. Doguwar riga ta zura bayan ta gyara kanta ta saka audugar mata. Kafin su isa asibiti ciwon cikin ya sakata durkushewa ƙasan mota. Bata yi kuka ba saboda tsabar ciwo. Kafin su isa asibitin cikin ya ɓare.

Bata san yanda ta yi rayuwa na wata guda ba bayan hakan. Ta yi kuka har idanunta sun gajiya. A hankali ta fara dawowa Nabilarta. Amma akwai abunda ya canza a tattare da ita. Da ƙyar Safina ta lallaɓata komawa wajen likita. Ji tayi ta haƙura saboda ciwon da zuciyarta ya yi sakamakon rashin cikin da ta ɗauki SOYAYYA ta dora mishi, take jin tamkar yanzu ta fara RAYUWA.

Ta ɗan ɗau lokaci kafin ta samu cikin Hajja. Amma bata wahala sosai ba saboda rage magungunan da ta yi. Bata ƙwallafa rai a kan cikin ba saboda tsoron rasa shi. Har rana irin ta yau bata ƙwallafa rai a kan Hajja ba.

Kafin Hussaini ya gaya mata zai ƙara aure, ta koma ta ga likita. Bata gaya mishi ba. Sai maganar auren ya rushe komai. A ƴan kwanakin nan ta koma.

Kitchen ta nufa bayan ta yi karfin halin ce mishi bari ta duba ruwan da ta ɗora. Ta ɗan jima tana kallon ruwan da ke tafasa cikin tukunya.

Tun ba yau ba ta san ciki yana wahalar da Lawisa. Kullum ana cikin waya tana asibiti. Sai cikin ya kai watanni kusan huɗu take daina laulayin. Laulayi ne mai azabtarwa. Taliya ta ɗauko ta juye a cikin ruwan tana kallo har ya dahu ta juye a kwalanda ta ɗauraye ta bashi lokaci kafin ta yaryaɗa mai ta saka a cikin flask. Bata san ko zata iya yin miya ba.

“Zan wuce asibiti”

Ta ji muryarsa daga bayanta. Ta juyo ta kalle shi. Da alamu wanka ya yi ya canza kaya.

“Ko zamu je tare ne?”

Ta haɗiyi wani yawu ta ɗan girgiza kai. Har zata juya kuma ta tambayeshi

“Me yasa baka kira ni ka gaya min ba?”

“Wayar na bari a gida har yanzu ban ɗauko ba ma. Kin san a asibitin na kwana”

Ta runtse idanu ta kawar da kai kamar mai son daina ganin wani abu a cikin ƙwaƙwalwarta kafin ta ce

“Da… Da na yi miscarriage (ɓari)..”

Wani yawun ta ƙara haɗiya kamar maganar da zata faɗa mai ɗaci ce

“Da na farka ban gan ka ba. Na yi ta jiranka har na kasa haƙuri na tambaya, Aunty tace ka tafi Kasuwa”

Ta yi murmushi mai ciwo kafin ta buɗe baki ta ce

“Amma yau…”

Ta ɗaga kafaɗa tare da girgiza kai. Take wani tunani ya faɗo mata, sai kuma ranar da suka fara haɗuwa da Hussaini ya faɗo mata.

  • *****

Banda tsaki babu abunda Lawisa take yi. Ita kuma Nabila murmushi kawai take yi. Tun a gida Lawisa ta ɓata lokaci tana tsantsara kwaliyya

“Ke Lawisa kwaliyyar me kike mu da zamu je walimar saukar Al’qurani?”

Ƙara saka tsinken kwalli Lawisa ta yi ta tisa baƙin layin da ta kewaye labbanta da suka sha jan janbakin kan ta waye da kuma wani mai kyalli da ta saya.

“Yarinta na damunki Nabila. Ke baki san sai ka haɗu da mijin aurenka a hanya ba? Ai bazan so haɗuwar farko ya gan ni ina naso ba”

Girgiza kai kawai Nabila ta yi ita kuma Lawisa ta ɗiga baƙi a ƙasan hancinta. Ta kalli kanta a madubi ta ga tayi yanda take so, tana ɗaukar ido sai ta miƙe ta ɗauko hijabinta ta saka. Kamar tace ma Nabila ta ɗan shafa hoda sai ta fasa. Duk da ta fi Nabila kyau gwanda a ganta tana maiƙo ko a yi tunanin mai aikin gidansu ce.

Bayan an yi sauka a makarantarsu ta Islamiyya, wasu masu hali duk sai aka yi musu nasu a gida daga baya. Tare Mummy ta haɗa ta yi musu ita da Lawisa. Yanzu Na Zahra zasu je tunda ƙawarsu ce kuma ta zo nasu. Safina sun yi tafiya amma da tare zasu tafi.

Tsakin da Lawisa ke yi, a tunanin Nabila rashin wanda ya taya ne. Bata ga wani namiji da ya tsayar da su ya ce yana son ma Lawisa magana ba. Ɗazu kafin su shiga gidansu Zahra ta ji tana addu’a kan Allah kar ya sa asarar janbaki da hoda ta yi. To da alama dai shi ɗin za’a yi.

Tunda wanda suka tambaya ya tabattar musu da cewa eh lallai nan din ne gidansu Zahra Mai saƙa da ake walimar saukar Al’qurani Lawisa ta ji wani daɗi ya mamayeta. Ta san su Zahra suna da hali amma bata san masu kuɗi bane. Irin wannan tangamemen gida haka? Allah ya sa wani ɗan gidan ya ganta yace yana so. Ko makarantar ba zata ƙarasa ba zasu yi aure idan ya so a ɗakin nasa tayi jarabawar WAEC din nata.

Abun takaici duk samarin da ta dinga gani a gidan babu wanda ya nuna ma kamar ya san da ita a gidan. To ko kalar hijabin ne bai yi ba? Da ma mayafi ta saka da wannan doguwar rigartata da ya dameta ne ta saka. Wallahi da duk abunsu sai sun kulata. Ta banka ma Nabila da ke can tana kallon hotunan da ake yi harara. Duk ita ta janyo mata. Da bata biyo mata da zumbulelen hijabinta ba da ba zata saka ba. Dan idan bata saka hijabin ba sai dai mamansu ta hana ta tafiya.

Idanunta ne suka hango mata wani ɗan saurayi sanye da yadi mai launin ƙasa mara turuwa. Take ta ji ya burgeta. Tayi mijin aure! Dole ta dage da ƙawance da Zahra. Yarinyar bata wani yi mata ba amma zata shige mata har ta samu gayen ya kula ta. Har ta fara ganin yaran da zasu haifa a tsakar wannan gidan suna wasa. Mace da namiji farare tas kamarta. Macen ma sak komai da komai nata ta ɗauko. Shi kuma namijin haske kawai ya fi wannan gayen. Ita kuma tana zaune gafenshi ya rungumeta ta ɗora kanta a kafaɗarsa suna kallon yaran suna dariya. Kamar dai wannan littafin da Safina ta karanta musu, wanda shi kaɗai ta nace ma. Ya ma sunan littafin? Tana koktarin tunawa Nabila ta taɓata wai Zahra ta ce su je su yi hoto.

Da saurinta kuwa ta ƙarasa ta rungume Zahra dan ta ji wata ƙaunarta ta mamayeta. Ƙanwar mijinta ce dole ta so ta. Allah ya sa ma dai yayanta ne uwa ɗaya uba ɗaya. Dagewa zata yi ta fito a hotuna da dama dan idan yana kallonsu yai ta ganin fuskarta.

Tsabar baƙin ciki bata ma san tana tsakin ba. Bata ƙara ganinshi ba. Ta so ta ji muryarsa ko ta ji daɗin tunaninsa amma ya wani shige gida ya maƙale.

Mota ce ta tsaya a kusa da su

“Salamu alaikum ƴan mata ina zuwa haka ne?”

Da masifa Lawisa zata yi musu amma sai ta hango handsome guy dinta. Nan da nan ta saki murmushi tana buɗe musu haƙoranta masu kyau da ke jere reras abun gwanin ban sha’awa. Ta amsa gaisuwarsu ta ce gida zasu je.

“To ku shigo mu kai ku mana. Ba ƙawayen Zahra bane?”

“Ƙawayenta ne. Kar mu ɗora muku nauyi. Nan ba da daɗewa ba zamu samu abun hawa”

Ya nuna mata babu komai su shigo. Suka shiga ya tambayi unguwar da zasu je ta mishi kwatance ya ce ai can ɗin ma suka nufa. Sunanta ya tambayeta, sai da ta saisaita murya ta ja sunanta ta gaya mishi.

Banda ƙunshe dariya babu abunda Nabila ke yi. Ji take kamar ta janyo kwanaki huɗun da ya rage ma su Safina su dawo take. Ta zo ta sha labarin iyayin Wisa Wise.

“Ƙawar taki bata magana ne”

Shi dai mai tuƙa motan ke ta magana tunda suka shigo. Ko dayan kurma ne?

“Gentle?”

Ta tsinci muryar Lawisa na faɗin sunan da wani makocinsu ɗan gidan Mamansu Amira ke ce mata. Wai sonta yake yi. Yai ta mata aiken gullisuwa da alawar madara su Lawisa na zugeta ta amsa suna sha.

“Da sauƙi maganar tata. Shi ma abokin naka baya magana?”

“Yana yi mana, kunya ce kawai yake ji”

Kamar Nabila ta kwashe da dariya amma ta ƙara ƙunshe bakinta da hijabi. Wai namiji da jin kunya. Wasu dai da kinibibi suke wallahi. Ko kunyar me yake oho mishi.

Ƙofar gidansu Nabila ta saka aka ajiyesu. Bata taɓa so ya san gidansu sai bayan sun yi aure dan kar ajinta ya zube.

“Yaya Hallleer mun gode a gaida gida Allah ya saka da alheri”

“Ba komai Lawisa. Sai ƙanin nawa ya dawo kawo muku ziyara ko Gentle?”

Ji tayi kamar ya saka guduma ya daki ƙirjinta. Gentle kuma?

“Wani ƙanin naka?”

Ƙarfin hali ta yi kafin ta iya wannan tambayar. Allah ya sa ba Handsome dinta yake nufi ba. Hannunta Nabila ke ja su shiga gida.

“Wannan Hussaini mai kunya. Kinga Shy da Gentle…”

Sanyin da jikinta ya yi ne ya ba Nabila damar jan ta su shiga gidan. Dariyar da Nabila ke yi sai ta ji kamar da gayya take mata.

“Kai Wisa Wise kin ji yanda kika ce Halliru kuwa? Wai Hallleer. Maddul me kika yi a wajen?”

“Na tafi gida”

Abunda ta iya cewa kenan ta juya. Tana jiyo Nabila na mata tunin awarar da suka ce Mummy ta aika a saya musu kafin su dawo gudun kar ta kare. Bata ƙara jin ɓacin rai ba sai da ta fito ta ga babu motarsu. Niyarta ta dawo tace musu auren Nabila nan da sati biyu. Amma zata je har gidan ta san yanda zata yi ta haɗu da Halliru kafin Hussain Handsome guy dinta ya zo wajen Nabila. Ko uban me ya gani a wajen wata banzar Nabila? Yarinyar da bata kaita kyau da gayu ba? Share zancen Nabila ta yi ta ci gaba da tunanin rayuwarsu tare da Hussain Handsome guy ɗinta dan ta yanke hukuncin raba su ko ta halin yaya ne.

Sai dai kuma tun asuba aka aiko da hatsarin motar da babanta ya yi ana tunanin ma ko bai kai labari ba dan haka ana idar da sallah ƙanin babanta ya zo ya ɗauketa suka wuce tasha. Tunda motar ta ɗauki hanya take kukan baƙin ciki har ta isa asibitin da baban nata yake. Fashewa ta yi da kuka ganinshi zaune kan gadon asibiti kan shi da bandeji ana bashi abu a kofi.

Amma wannan kanin babanta ya cuceta da ya maka musu ƙarya.

“Haba ke kuwa Lawisa ba gashi kin ga jikin da sauƙi ba? Tunda muka taho take ta kuka. Na ga jikin da sauƙi. Aka ce motar tintsirawa ta dinga yi ya fi sau hamsin”

Tana ji ana dariya amma ji ta yi kamar ta rufe shi da duka dan baƙin ciki. A zuciyarta ta ce

“Shege matsiyaci ɗan masu ƙaryar jaraba!”

*****

Suna zaune suna ta dariyar Lawisa ita da Safina. Mummy sai girgiza kai take tana murmushi tana ce musu gulma suke yi

“Ai Mummy ba gulma bane tunda idan tana nan ma fada zan yi”.

Da an ɗan jima sai suce “Hallleer” su kwashe da dariya. Yaro ya shigo yace ana sallama da Nabila.

“Uhm uhm, ta Gentle din fa”

Harararta Nabila tayi

“Kin san dai baya aikowa a kira ni sai dai mu haɗu a hanya”.

Miƙewa ta yi ta ja mayafin Safina zata fita Mummy ta kira ta.

“Je ki shafa ko ƴar hoda ce ki zo Safina ta raka ki”

Zumɓuro baki Nabila ta yi

“Mummy ƙila fa ba ma ni Nabilar ake nema ba fa”

” Ko ba ke bace ai a gan ki tsatsaf ma wani abun ne”

Ciki ta shiga ta saka hoda ɗan kaɗan a tafin hannu ta shafe ta mutsukke a fuska. Ta dangwali vasilin kaɗan ta saka a leɓenta.

Bata gane samarin da ke tsaye jikin mota ba amma suka gaisa.

“Gentle wajenki muka zo”

Suka kalli juna ita da Safina. Har ga Allah bata san su ba. Take tsoro ya kama ta.

“Ina ƙawarki Lawisa?”

*****

Nabila ta kalle shi da kyau, sai yanzu take ganin hoton tar tar!

“Hussaini, me yasa baka faɗa min gaskiya ba a lokacin?”

Jama’a yaya muka ji wannan waiwayen? Ai tafiyar tamu ta yi walwal ko? Kun ga hoton tar tar kuma? Ko sai an muku fashin baƙi?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 13Soyayya Da Rayuwa 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.