A mota ta iske su suna jiranta bayan Hassan ya daddana horn yana nuna tafiyar lokaci. Tun jiya ta gaya mishi yau za'a fara bayar da admission letter na makaranta zata je ta amso kuma ta yi registration.
"Na raka ki ne?"
Tambayar ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba. Girkin Afrah ne amma zai fita da ita. Basu taɓa samun matsala a ka ya fita da wata ranar girkin ƴar uwarta ba saboda bai taɓa fita da Afrah ranar girkin Safina ba.
"Yi haƙuri na bar ma Suwaiba sallahu ne kar mu dawo bamu. . .