"Ni dai dan Allah ki yi hakuri ki yafe min. Na amshi gashi ya isa haka."
Hassan ke lallashin Safina a hanyarsu ta zuwa zai kai ta saloon. Nan ake mata gyaran jiki da na gashi. Idan ya kai ta ya ajiye, da ta kusa gamawa zata kira shi ya taho ya maida ita gida.
"Kalli fa yanda na rame na zama kwarangwal. Ulcer fa har ya kama ni. Idan so kike na mutu to."
Cuno baki ta yi tana ƙunƙuni. Ina zata so ya mutu? Kawai dai haushin abunda yake shirin yi take ji har ƙasan ran ta. . .