Skip to content
Part 4 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

“Ni dai dan Allah ki yi hakuri ki yafe min. Na amshi gashi ya isa haka.”

Hassan ke lallashin Safina a hanyarsu ta zuwa zai kai ta saloon. Nan ake mata gyaran jiki da na gashi. Idan ya kai ta ya ajiye, da ta kusa gamawa zata kira shi ya taho ya maida ita gida.

“Kalli fa yanda na rame na zama kwarangwal. Ulcer fa har ya kama ni. Idan so kike na mutu to.”

Cuno baki ta yi tana ƙunƙuni. Ina zata so ya mutu? Kawai dai haushin abunda yake shirin yi take ji har ƙasan ran ta. Ta kalle shi ta ga ya rame ɗin, sai ta ɗan ji tausayinsa. Amma sai ta gama gasa shi a hannu tukunna. Hira yake yi mata tana amsa shi sama sama amma bai fasa ba. Suna ina harabar wajen ya faka sannan ya mika mata katin bankinsa na ciro kuɗi ( ATM card). Ɗaya daga ciki ya bata wanda kuɗaɗen ciki ba wasu masu yawa bane amma zasu isheta duk wata hidima da zata yi a yau.

Karɓa ta yi tana ƙunƙuni ta fice, shi kuma murmushi ya yi yana binta da kallo har ta zarce wajen da injin cirar kudin yake da ke a babbar plaza shagon yake. Sai da ya ga ta shiga wajen saloon ɗin sannan ya janyo wayarsa da ta yi tsuwa alamar saƙo ya iso.

Ɗaya na banki ne, ya nuna masa an ciri kudi dubu hamsin. Ya san bata cirar kudi sama da dubu ashirin. Dan haka sai ya nemi lambarta ya tura nata sako.

Saboda ke nake neman kuɗi Safina, ki cire dukka ma idan kina buƙata kuma a ƙara miki. I love you, always.

Daya saƙon talla ne daga kamfanin wayar. Dayan kuma daga Afra ne amma ya adana lambar a karkashin suna, Shago 12, a nufinsa lambar ɗaya daga cikin yaran shagon Alhaji ne. Duk bin ƙwaƙwaffin Safina ba zata taɓa ɗago shi ba. Dama bai faye ture turen saƙo da ita ba sai dai waya da zarar ya samu sarari. Saƙon gaya masa ya yi cewar.

Ina makaranta.

Tunani ya fara yi, da niyyarsa ya je gidan Hussaini ya ci abinci dan yunwa yake ji. Amma kuma yana son zuwa ya ga Afrah dan ya ɗan kwana biyu bai je wajenta ba. Wajen Afrah ya nufa bayan ya kirata ya ce yana zuwa ta gaya masa inda zasu hadu.

Tana zaune a kan irin kujerunnan da ake yi na siminti. Murmushi suka sakar ma juna kafin ta ce,

“Ka rame Boo. Ka yi rashin lafiya ne?”

Ya shafa wuyansa.

“Ina rashin lafiya? Kin san idan za’a yi biki ango duk ramewa yake ya yi zuru zuru.”

Dariya ta yi tana girgiza kai.

“Kin gama ne?”

“Da tuni na yi submitting, kai nake jira ka zo”

“To mu je na raka ki ki yi submitting ɗin.”

Haka suka jera suna hira ya raka ta cikin department har bakin ofishin H.O.D, ta shiga. Bata wani jima ba ta fito tana ta murmushi.

“Uhm, shikenan kuma an zama graduate. Sauran jiran result.”

Ta saka tafin hannu ta rufe fuskarta tana jin daɗi na ratsa ta. Suka wuce inda ya ajiye mota.

“Na san baki ci abinci ba. Dimple ɗin ya kara shigewa, ɗan kumatun tuni ya koma.”

Hannu ta saka tana rufe kumatunta tana dariya.

“Kar ki zo kina ramewa fa, duk so na da dimples na fi son kumatu.”

Haka sukai ta hira har suka karasa wajen cin abincin. Daga nan ya ɗauketa ya maida ita gida idna ya shiga ya gaida mahaifiyarta sannan suka shiga wani babin hiran. Da ƙyar ya hakura ya yakice kansa ya wuce dan Hussaini na ta doka mishi kira.

A mota ya goge wayoyin da ya yi da Shago 12 da saƙon da ta turo sannan ya wuce ya koma gida.

*****
Tsaki Safina ta yi, zuciyarta na tafasa bayan ta ƙara karanta sakon da Hassan ya tura mata. Ita bata duba kalamsa ba, bata duba I love you dinsa ba, Safina da ya kirata da shi ya fi komai kona mata rai.

“Maman Iman me ya faru ne kike ta tsaki?”

Maman Fati mai gyaran jikin saloon din ta tambaya tana kwaɓa wani abu a ƴar roba wanda zata shafa ma Safina idan an gama wanke mata kai da ƙafa. Yanzu haka tana cikin drier na gashi dan steaming ake mata yayin kuma da Blessing ke gyara mata ƙafa.

“Hmn Maman Fati ki bari. Namiji bashi da alƙawari sam sam.”

Wata mata da Inniya (Mai Kitso)  ke yi ma kitso da zaren attach ta yi dariya wanda ya saka Safina cewa.

“Allah kuwa baiwar Allah. Wai kana zaman zamanka da mijinki, babu faɗa babu gaba, yana sonka kana son shi fa amma wai ya ɗauko maka aure.”

Maman Fati ta ajiye robar hannunta tana zare idanu.

“Wai mijinki? Aure zai yi? Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Kai jama’a!”

Nan dai aka fara taya ta jimami da salallami.

“Baki ga yanda yake ji da ita ba. Yana nan nan da ita.”

Cewar Aunty Fati ga wannan wacca ake ma kitson.

“Shi fa yake kawota nan, ya zo ya ɗauketa. Baya hada hidimarta da ta kowa. Oh ni Fatimatu Binta Rasulullahi.”

“Hmn, to ai kowacce mace hakan take so. Ƙila abunda aka hanga aka hango kenan ake so a raba tare.”

“A raba tare ko a raba ka da miji Hajiya Bilki?”

Inniya ta tambaya tana tsaga kan Hajiya Bilki.

“Wallahi wasu basa so a raba miji da su sai dai su kaɗai. Shi yasa nan da kika gan ni a tsaye nake ƙyam da ƙafafuna. Ni kenan ma da mijin ba na wani a zo a gani ba. Allah dai ya kyauta ya kiyaye amma… hmn.”

A dai dai lokacin Blessing ta gama wanke mata kafar. Ta koma ta cireta daga cikin drier suka nufi wajen ɗauraya. Cikin ɗan lokaci aka busar da kan suka wuce ɗan wajen da aka keɓe dan gyaran jiki.

“Ki manta zancen su Inniya. Ke dai ki maida hankali wajen gyara kan ki kamar yanda kika saba. Akwai kaya ma an kawo. Goggo na ta Chadi ta zo da kanta dan dai bata gama dukkansu ba da duk yau kin saya ma.”

Maman Fati ke gaya mata lokacin da take yi mata dilka. Bata da gashin jiki balle a yi mata halawa. Tana mata tana bata labarin magungunan matan da suke da akwai. Su tsumi ne sai gumba.

“Idan ya yi auren akwai wata kaza da za’a hado miki. Ta fi ta waccan da kika ci da kika haifi Ilham.”

“Ke dan Allah Maman Fati.”

“Wallahi Allah. Ni ma da na ci, hmn hmn hmn abun sai wanda ya ci kawai.”

“Ai kuwa ina so wallahi. Nawa ne shi?”

“Sai dai na tambayota. Kinga ni da kazata ma aka min kuma ta gida ce amma sai da na bada dubu takwas.”

“Babu matsala, ki tambayo min ɗin sai na miki magana idan lokacin ya yi.”

An ɗan dauki lokaci ana gyaran jiki kafin daga nan ne ta maida wasu kayan da ta zo da su, shi ma saida aka turara mata su. A nan ne ta zauna Inniya ta yaryada mata kitso da ya zubo gefe da baya irin yanda Hassan yake so. Aka kuma saka mata jan lalle iya ƴan yatsu. Nan kyawunta ya kara fitowa, ta ƙara yin haske, ta ɗau kyalli kamar sabuwar amarya.

Lokacin da ta kira Hassan din ne ta karɓi magunguna daga wajen Maman Fati.

*****

“Gaskiya kana da matsala Hassan. Tun yaushe nake kiranka ka ƙi ka amsa kuma ka san jiranka nake yi.”

“Ya isa. Ina gaba da kai zaka saka ni a gaba kana min fada dan baƙin rai irin naks. Mu je toh.”

Haushi ya kyara ƙule Hussaini dan ya ga Hassan din ma dariyarsa yake yi bayan ya saka shi jiran sama da hour daya. Motar kawai ya shige Hassan ɗin ya ja su, yana bin wakar da ake a rediyo yana kaɗa ƴan yatsu a kan sitiyarin mota. Hassan bashi da wata matsala. Kullum cikin walwala da farin ciki.

Da farko ya ɗauka Hassan din zai fi shi shiga matsala a wannan ƙarin aure da suka ɗauko. Ganin Hajiya Mama na bayanshi sannan kuma Nabila ma ba zata bashi matsala ba. Sai gashi abun ya juye. Da ɓacin rai yake kwana yake kuma tashi. Ina aka barshi ma ya yi baccin?

Bayan ya ƙi amincewa da aikin da tace zata nema, ya ɗauka idan ya dawo zata yi rigima da shi. Amma sai ya tarar da akasin hakan. Sai washegari bayan ya fita ya dawo, kawai ya ci karo da wani tsohon keken ɗinkinta a korido tana kai tana ɗinki. Bayan sallamar da ta amsa ko kallonsa batai ba.

Kokarin bacci yake yi amma mugun ƙarar keken ya hana shi ko gyangyadawa. Mikewa ya yi ya taho bakin kofa ya leko

“Nabila, bacci nake son yi”

“Wani abun za’a kawo maka?”

“Ƙarar keken ne ya hana ni”

“Sai haƙuri ai. Bani da kuɗin kai shi service. Idan Allah ya hore min na kai sai ka ji ƙara ya ragu.”

Ya gane kawai nufinta, ko ya yi baccin da ƙaran ko kuma ya haƙura da baccin. Bazai iya zama da wannan mugun ƙaran ba gaskiya dan haka ya tashi ya fita ya bar mata gidan. Bai dawo ba sai da ya tabattar sun yi bacci. Ya zauna ya yi ƴan ayyukan da zai iya kafin baccin gajiya ya kwashe shi.

Bai san tsawon lokacin da ya ɗauka yana baccin ba amma ya san bai daɗe ba kafin wani gigitaccen ƙara ya tashe shi. Sai da ya zauna, ƙwaƙwalwarsa ta yi lissafa sannan ya gane ai keken Nabila.

“Nabila, Dan Allah ki bar taka keken nan ko na samu na yi bacci.”

“Na yi yaya da ɗinkin mutane da na karɓo? Bana son na saka saɓa alkawari cikin sana’ata na zo na dinga ganin ba dai dai ba.”

Ɗaki ya koma ya danne kan sa da pillow dan takaici. Amma fa ƙarar keken nan bai daina iske cikin kwakwalwarsa.

Innalillahi wa inna ilaihir raji’un!

Abunda kawai ya dinga ambata kenan har zuwa wani lokaci kafin ya ji shiru alamun ta gama dinkin kenan. Ya yi ma Allah godiya sannan ya saki jikinsa ya kwanta bacci.

Karar nan ne dai ya kuma tashinsa. Da gudu ya fito daga ɗaki.

“Nabila me kike ne dan Allah dan annabi? Ba zan yi bacci ba ko me?”

Ta ɗago ta kalle shi mamaki fal fuskarta

“Ka yi bacci mana Hussaini. Kai da gidanka ai ban isa na hana ka bacci ba.”

“Kin san keken nan yana da ƙara sosai. Ki yi hakuri zuwa safiya.”

Dariya ta yi wanda tun kafin ta bude baki ya san abunda yake so ba shi zai samu ba.

“Ka ga ɗinkin nan saura biyu. Kuma gobe da safe zasu zo su karba dan shi zasu saka. Da na gama haɗe wannan, zan je na yanka sauran biyun na dawo na ƙarasa shikenan sai ka yi baccinka.”

“Yaushe kike saka ran gamawa?”

“Eh to, ba zan ce ba amma dai a ƙalla awa hudu zuwa biyar.”

Banɗaki ya shige kawai ya yi alwala ya tada sallah dan ya san shi zai fishe shi.

Daren jiya kuwa tana hawa kan kenan ya fito ya hau ta da masifa dan kayan da ta kwana tana dinkawa, a jikinta da Hajja ya gani babu wasu daban da suka kawo dinki.

“To wai kwana nawa ne ma ya rage maka kai ma ka huta da ƙarar keken nan? Ina ce idan ka tafi gidan amarya zaka ɗan samu ka sarara?”

Ta ɗauko wata jaka tana lalubar zaren da zai shiga da kayan da take ɗinkawa

“Yanzu da mutum yana fita aikinsa ina shi ina takura ma masu gida?”

Muryar Hassan da ke tambayarsa ya shirye shiryen bikin ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya nausa. Nan yake gaya mishi Hajiya Mama ta ce ya bar komai a hannunta. Daga lefen har hidindimun bikin. Idan lokaci ya karato zata sama mishi gidan da zasu zauna dan ya gaya mata bashi da ra’ayin hada su gida daya. Gidan da yake ciki ɗakuna uku ne ba zai yiwu duk su gwamutsa a ciki ba.

Hankalinsa ya kara komawa kan Nabila da keken ɗinkinta. Ya bata kudi har dubu biyar ta yi service ɗin keken amma tace mishi mai gyaran ya yi tafiya sai dai idan ya dawo.

Rigima take nema, so take ta nemi aiki shi kuma bashi da ra’ayi. Ya gaya mata ba sau daya ba,  ba sau biyu ba. Dinkin ma da take ɗan yi ma kanta lokacin tana amarya duk ta watsar saboda makaranta da ya sama mata nan FCE ta karanta Business Administration. Duk da cewar lokaci zuwa lokaci tana yi ma kanta da Hajja ɗinki amma baya sanin lokacin sai dai ya gansu da kayan.

Ya gaya ma Hassan bukatar da Nabila ta zo da shi.

“Ka bar bata ta yi aikin mana tunda ta nuna tana so. Yanzu fa sai an lallaba su”

Girgiza kan shi Hussaini ya yi. Baya son matarsa ta dinga yawan fita. Idan ta fara aiki kuwa fita ya zama dole. Zata dinga cuɗanya da maza tana mu’amalantarsu. Zuciyarsa ba zata ɗauki hakan ba. Ya san Nabila tana da kamun kai, amma hakan ba shi zai hana ta ko da gaisawa da mazan bane. Yana da tsananin kishi. Hajiya Mama ta faɗi hakan.

Dinkin ma ba ya so ta yi shi a matsayin sana’a. Mata zasu dinga shige da fice a gidan da sunan ɗinki shi kuma baya so. Ba za’a maida mishi gida dandalin mata ba.

“Toh Hussaini, kar ka barta ta yi aikin. Ni ina ruwa na ne ma? Matarka ce, gidanka ne. You know what’s best for you. Duk idanunka sun yi luhu luhu, baka da lafiya ne?”

“Bacci ne bana samu”

Bai gaya mishi harda ƴar yunwa ba. Nabila bata samun gama dahuwar abinci da wuri a cewarta ɗinki ya ɗauke mata hankali. Sannan ga tazarce. Ya tsani ya ci abu da rana kuma ya ci da dare. Wataran ma har safe shi take kawo mishi.

“Dole zaka fuskanci ƙalubale. Wannan auren da ka ɗauko, alherin cikinsa na da yawa. Zaka ga masu adawa da auren nan har cikin danginka. Amma ka san sai ka daure. Babu wani abu mai kyau da ke zuwa ta sauki.”

Irin kalaman Hajiya Mama kenan tana tausarsa. Baya so yai mata ƙorafi ko ya nuna mata abunda Nabila take yi. Ta san faɗa zata mishi ta ce,

“Ka bari ta raina ka.”

Murmushi ya yi. Duk salo ne dan ta saka auren ya fita a ran shi. Amma zai daure. Kwana nawa ne kafin ya yi auren kamar yanda ta faɗa. Zai jure ƙarar kekenta, zai ɗauke shi kamar busar sarewa har zuwa lokacin. Ba zata juri ɗinkin daren ba ya sani. Na ɗan lokaci ne.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 3Soyayya Da Rayuwa 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.