Skip to content
Part 5 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Harararta Hussaini yake yi ita kuma ta ɗauke kai. Jiran dawowar likita suke yi a falon Inna. Da ga shi har itan Alhaji ya ce a yi ma allura. Shi bai ma lura da yanda ta rame idanunta suka yi wani kogo ba sai yanzu. Lomar tuwon ta ƙara dannawa a baki shi ma sai ya saka cokali ya gutsira. Inna ce ta haɗa musu abinci a kwano ɗaya, abunda suka daɗe basu yi ba. Tun lokacin amarcinsu kafin ya nuna baya so.

“Ina naman?”

Ya tambaya yana zaro idanu. Idan ba idanunsa bane suka yi masa gizo ba, kamar naman farantin ya fi biyar. Yana kallon yanda ta ɗage kafaɗu alamun bata sani ba ita ma.
“Je ki karo naman tunda kin cinye. Ni ban ci ko ɗaya ba.”

Inna ce ta fito daga ɗaki tana tsare su da idanu

“Maganar me ake ta yi ne tun ɗazu?”

“Gaba ɗaya fa naman da ke miyar ta cinye. Ban ci ko ɗaya ba.”

“To me ka tsaya yi har ta cinye? Sai dai ka jira na abincin dare kuma.”

Kicin – kicin ya yi da rai. Yana matukar son nama a rayuwarshi baya iya cin abinci idan babu nama. Haka ba dan ya so ba ya ci tuwon. Yana yi yana ranƙwala ma hannun Nabila cokali.

Lissafi ya yi ba dai – dai ba. Rashin bacci, kwanciyar hankali da abinci mai inganci ya saka shi yin kuskure a lissafi wanda ya ja musu asarar dubu ɗari uku da saba’in! Idan Hussaini ya yi kuskure a lissafi, to ba ƙaramin abu bane ya janyo haka. Wannan ne karo na uku da ya taɓa batan lissafin a shekarun da ya fara jan ragamar lissafe – lissafe a harkar kasuwancin Alhaji. Shekaru tara baya kenan.

Na farkon, lokacin da Nabila ta yi ɓarin ciki ne. A lokacin shekararsu uku da aure. Suna murna ta samu ciki amma rana ɗaya ya ɓare. Sai ya ji kamar wani ya ce ba zata ƙara samun ciki ba. Halin da Nabila ta shiga shi ya dagula masa lissafi har ta kai ga an rasa kuɗi marasa yawa, basu fi dubu hamsin ba.

Na biyun kuma, Hajja ce ta yi wani ciwo mai rikitarwa. Ciwon da sai da ya fidda rai da ita. Har kuka yake ɓuya ya yi dan baya son karyarma Nabila zuciya, yana ganin ta fi shi jarumta. Idan ya shiga mota, kuka. Da ya je gida karbo saƙo, kuka. Alwala, kuka. Sallah, kuka. Bayan da ta warke sai da ya kwanta cuta shi ma. Duk kuɗaɗen da ya yi tunanin an yi asararsu, bayan ya nutsu sai ya gano cikin lissafi suka ɓace.

Alhaji ne ya kira shi domin tuhumarsa. Amma ganinsa da ya yi sai kawai ya ƙura mishi idanu. Farat ɗaya ba zaka gane ba sai ka zuba mishi idanu zaka ga ya faɗa, ya yi kamar bashi da lafiya.

“Me yake damunka?”

Dama daga kallon da Alhajin ke mishi ya san wannan tambayar zai mishi. To me zai ce yana damunshi? Nabila tana hana shi bacci? Kafin ya furta , a cikin kanshi ma maganar ta ba shi dariya. Ba zai ma iya faɗa ba.

“Ko ma dai me ke damunka, ka ajiye shi gefe idan harkar kasuwanci ya tashi. Ka yi maganin koma meye sannan ka zauna ka sake sabon lissafi ka ga inda kuɗin ya tafi.”

Alhaji kenan. Babu abunda ya shafe shi. Yanzu da Hajiya Mama ce sai ta saka shi a gaba ta ji me ke damunshi. Shi yasa kwana biyu yake ƙoƙarin basu haɗu ba. Ya ce ayyuka sun yi masa yawa. Ita ma da yake tana wasu shirye shiryen bikin sai bata matsa ba.

Sai yau. Alhajin ya ƙara kiranshi. Wai Nabila ta faɗi. Jiri ya ɗebe ta a kitchen suna girki ita da Habiba. Ta je gida ta faɗa ya aika Umma ta taho da ita. Bai tsaya tambayarta abunda ya sameta ba amma ya san da matsala. Ta lalace baki ɗayanta. Ko zama Hussaini bai yi ba Alhaji ya hau shi da faɗa. Ya saka shi gaba sai ya gaya mishi me yake ma Nabila.

“Wallahi Alhaji ba abunda na yi mata. Idan akwai abunda nake miki ki faɗa.”

Sunkuyar da kanta ta yi ta na wasa da ƴan yatsun hannunta. Bacci take ji dan ji take yana fisgarta. Abunda ya saka ta faɗuwa ma kenan. Matsalar ma da ta fara, sai ta farka ta je ta hau keke musamman idan Hussaini na gidan. Ji tayi ya fara bayanin ƙila wahalar ɗinki ne ya ramar da ita.

“Alhaji bata bacci. Raba dare take a kan keke kuma da safe ma bata baccin. Ni ma ta hana ni.”

Waje Alhaji ya ce Hussaini ya tashi ya basu. Ya tambayi Nabila me ke faruwa. Babu abunda ta ɓoye mishi dan dama ƙiris take jira wani ya tambayeta abunda yake damunta. Nan Alhaji ya goya mata baya.

“Tunda ka hanata aiki, kuma baka so ta yi sana’a, ka saka mata albashi. Nan da kwana shida wata zai ƙare, lokacin zaka fara bata. Kafin nan ka gaya min nawa ka yanke zaka dinga bata. Hakan ba yana nufin zaka daina yi mata duk wata ɗawainiya ba. Hussaini Allah ya rufa maka asiri, ban san me kake yi da kuɗinka ba amma bana gani kana kashe su yanda ya kamata. Kai baka ganin yanda matarka ke fita daban a cikin ƴan uwa? Ka je ka yi tunani. Ka je ka sameta wajen Asma’u zan aiko likita ya zo yai muku allurar bacci. Ta daina hana ku bacci.”

Bai wani ci abincin da yawa ba Saboda rashin naman. Sai da suka ɗan zauna sannan likitan ya zo. Duba su ya yi kawai ya ce su samu su yi bacci gobe sai ya ƙara zuwa ya duba su. Ɗakin Inna suka shiga suka kwanta. Ta juya mishi baya tare da jan bargo ta lulluba dan bata iya bacci sai ta rufe ko da kafarta ce. Ƙeyarta ya dinga kallo har bacci ya ɗauke shi.

Shi ya riga ta tashi. Lokacin ta juyo da fuskarta tana fuskantar inda ya ke kwance. Wani irin motsawa zuciyarsa ta yi da soyayarta. Yana son Nabila, Allah ma ya sani. Ya san baya nuna mata kamar yanda ya kamata amma yana da dalilansa. Dalilai da a ganinsa masu kwari ne. Hannunta ya kamo yana matsawa a hankali.

“Lokacin sallah ya yi. Tashi mu yi jam’i.”

Abunda ya faɗa kenan da ya ga ta bude idanunta.

“Je ka yi kawai.”

Yanayin yanda ta yi maganar ya saka shi lumshe idanu. Yana son jin muryarta idan ta tashi daga bacci. Yana sanyaya mishi rai.

“A’a tashi dai mu yi tare”

Ya gane me take nufi data ce ya yi kawai. So yake ta yi magana ya ƙara jin muryarta. Ganin ta juya mishi baya ya saka shi matsowa yana mata raɗa.

“Assalatu khairun minal naum”

“Allah ya sa Inna ta shigo ta gan ka”

“Amin yarinya. Ke dai zaki kwana a ciki tunda kin fi ni kunya”

Tashi ya yi ya shiga banɗakin da ke cikin ɗakin ya yi alwala. Ya shimfiɗa abun sallah ya yi sannan ya koma gadon ya kwanta. Baya jin baccin dan ba laifi wanda ya yi ya ishe shi. Janyota ya yi jikinshi yana jin ƙamshin turaren jikinta.

Yanayin nan sai ya tuna mata da lokacin da suke ganiyar amarcinsu. Lokacin da yake Hussainin da ta sani, wanda ta faɗa kogin soyayyarsa. Ba Hussainin da ta tsinta rana tsaka ba. Wanda ba shi da lokacinta, baya son wani kusanci da ita.

Ƙwanƙwasa ƙofar ya saka shi saurin sakinta yana dira daga kan gadon. Bata san lokacin da ta fashe da dariya ba, shi kuma ya yi kicin kicin da rai tare da bada izinin shigowa. Habiba ce,  Inna ta aikota kan su tashi su yi sallah su ci abinci. Tana fita Nabila ta faɗa banɗaki. Akwai ƴar jakarta da ta koma gida ta haɗo shi ma da kyar sai da Umma ta yi ƴar dabara Alhajin ya yarda.

Ta yi tunanin zata fito ta ga baya nan. Amma sai ta tarar yana zaune yana jiranta. Cewa ya yi ta shige gaba yana biye da ita a baya. Burabusko aka yi da miyar taushe. Kaɗan Nabila ta iya ci dan bata jin wata yunwa.

Daga nan Hussaini ya wuce wajen Alhaji inda ya tarar Hassan na nan.

A daki kuwa Umma ce take ba Nabila ƴan shawarwari.

“Kar ki zama mai tayar mishi da hankali Nabila. Wallahi ya rasa kwanciyar hankali a wajenki, wajen ɗayar matar zai je. Ƙarin aure ba yana nufin mijinki ya daina son ki bane. Kin dai ga bayan ni, Alhaji ya ƙaro wasu matan biyu amma kin shaida irin son da yake min har gobe. Ina da wani matsayi a wajenshi na daban na sani, kuma kuma duk kun sani. Ki yi ƙoƙari ki danne zuciyarki. Zaki ga kuma zaki ji abunda zai ɓata miki rai. Ki kwantar da hankalinki dan Allah Nabila. Idan akwai abunda ke damunki, ki zo ki gaya min ko ki gaya ma Umma”

Wajen tara da rabi Hussaini yace ta zo su wuce gida. Sallama ta yi da Umma suka fice. Gani ta yi sun wuce zasu tafi tace,

“Zamu ɗauko Hajja”

“Ƙyaleta gobe ba school”

Haka nan ya rike hannunta ya musu jagora suka koma gida. Ruwa ta watsa mai zafi a jikinta saboda ta ji daɗin jikinta dan ta shirya kashe daren yau tana bacci. Ta ɗauko man zafi tana shirin mulkawa a jikinta wayarta ta yi ƙara. Hussaini ne. Ce mata ya yi ta zo ta same shi zasu yi magana.

Samunshi ta yi a zaune a kan gado ya barbaza takardu sannan ga laptop yana dubawa.

“Aiki zaki taya ni. Ɗauko calculator a drawer ɗin can”

Ba musu ta ɗauko calculator ta nemi waje a gadon ta zauna. Ya gaya mata takardun da zata duba da kuma lissafin da zata yi. Babu wanda yake ce ma wani komai sai da ta gama da takardar farko sannan ta fara karanta mishi yana dubawa. Haka suka dinga yi har suka ɗan yi nisa kafin ya ce su bar shi hakanan zuwa gobe.

Ita ta tattara wanda suka gama ta ajiye su daban. Wanda basu yi ba shi ma ta ajiye shi daban. Tana shirin fita ya kirata ta dawo.

“Ki kwana a nan mana.”

Kallon kallo suka tsaya yi na wasu daƙiƙu. Magana ce a bakinta amma wani abu ya tsaya mata a makoshi ya tokare mata shi. Bata taɓa tunanin zata ga wannan ranar ba. Ranar da Hussaini zai buƙaci su kwana a ɗaki ɗaya. Ita ba tafiya take yi da shi ba balle zaman hotel ya haɗa su kwana ɗaki daya. Tunda ta aure shi banda tashar jirgi babu inda ta taɓa raka shi.

Jiki babu ƙwari ta koma ta nemi waje a gadon ta raɓe ta kwanta. Tana kallonshi yana ta je ka dawo yana shirin bacci. Sai da ya saita musu sanyin na’ura mai sanyaya ɗaki (AC) sannan ya kashe musu fitilar ƙwan ɗakin. Tana jin shi ya kwanta a gadon tare da lalubo hannunta. Bata san dalili ba, amma sai ta ji hawaye na silalo mata.

Safina na ganin wayar Inniya ta amsa da murmushi. Kafin ta bar saloon rannan, sai da ta karɓi lambar wayar Inniya da Hajiya Bilki. Lokacin Maman Fati ta leƙa waje suka nemi su yi musayar lambar juna. A cewar Hajiya Bilki, zata taimaka mata.

Sun yi waya sau ɗaya sun gaisa in da take gaya mata zata binciko mata wacece yarinyar da Hassan ɗin zai aura dan gwanda ta san komai a kan ta kafin ta shigo. Ta hakan ne zata san yanda zata fara yaƙin.

“Maman Iman, ina kika shiga Hajiya Bilki na ta kiranki bata same ki a waya ba.”

Inniya take tambaya bayan sun gaisa. Ita ma tun ɗazu take neman wayar da ƙyar ta samu.

“Ina gida Inniya ba inda na je”

“To ki kira ta. Akwai labari”

Jiki na rawa Safina ta kira Hajiya Bilki. Suka gaisa sannan Hajiya Bilki ta fara bayani.

“Yarinyar sunanta Afrah Suleiman. Kamar yanda kika faɗa din a Court Road suke. Su hudu aka haifa a gidansu ita ce ta uku. Ba zata fi ashirin da biyu ba yarinya ce karama kin ga kina da advantage a kan ta.”

“Advantage? Shekaru kaɗan fa na bata. Ashirin da shida nake Hajiya Bilki. Haihuwata uku, sai dai na nuna mata ragwargwajewa. Kema fa tunani kike na ba talatin baya. Na fi ta tsufa.”

“Maman Ilham kenan. Ba zaki gane karatun ba sai na miki shi dalla dalla. Ina gaya miki, kwanan nan ta gama BUK, ta karanta…”

“BUK fa kika ce.”

Safina ta faɗi hankalinta na kaiwa kololuwar tashi. Ƴar jami’a Hassan zai auro mata? Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Tashin hankali da ba’a saka mishi rana. Duk laifinta ne, ita ta ja ma kanta. Ta ki yin karatu yanzu an samo wacca ta fi ta.

“Hajiya Bilki, zan kira ki anjima.”

Bata jira abunda ta ce ba ta kashe wayar ta faɗa ɗaki. Farko rasa abun yi tayi sai kuma ta lalubo lambar ƙaninta ta kira. Kwanaki ta tura mishi kuɗi ya sayi form ɗin JAMB, Allah ya sa ba’a rufe ba.

“Musbahu, an rufe saida form ɗin JAMB ko ba’a rufe ba?”

Ko gaisauwarsa bata tsaya amsawa ba saboda yanda take jinta.

“Da an rufe kuma sai aka kara tsawon lokaci. Nan da kwana tara za’a rufe.”

Ba ƙaramin farin ciki ta ji ba jin cewa tana da damar shiga jami’ar kwana kusa. Ba zata yi saki na dafe ba.

“Yauwwa Musbah, kace a Cafe ake register ko?”

Ya yi mata bayanin yanda zata samu da abubuwa da zata buƙata sannan suka yi sallama.

Sauri ta yi ta dubo takardunta na WAEC ta ɗauki Ilham ta fita ta tari adaidaita sahu. Gidansu Hassan ta mikia ta ita kuma ta tafi inda zata.

Tunda take bata taba shan wahala irin ta yau ba. Kashe wayarta ta yi saboda kiran da Hassan ke mata ya dawo gida bai isketa ba. Ce mishi ta yi ya ɗan sarara mata zata kira shi. Ganin ya ƙi ƙyaleta ya saka ta kashe wayar. Ta fi hour biyu a Cafe saboda network. Da ƙafa ta dawo gida. A nan kofar gida ta tarar da Hassan.

“Ina kika tafi Safina sannan kika kashe waya. Ga Ilham na can tana ta kuka.”

“Form ɗin JAMB na je na cike.”

“JAMB? Wani JAMB?”

“Wanda ka sani. Makaranta zan koma. Na kashe dubu ashirin zaka biya ni.”
Ya bita da kallo yana mamaki. Matar da babu yanda bai yi da ita kan komawa makaranta ba ta ki. Har ƙawarta Nabila ta yi FCE ta gama ko a jikinta. To me ya saka take son komawa makaranta?

Kada ku manta ku yi comment, like da share.
Yaya labarin namu yake tafiya?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 4Soyayya Da Rayuwa 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.