Skip to content
Part 6 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Yanda ta dage tana ta rubutu a littafi sai da ya ba Hassan dariya. Tunda ta je ta yo rajistar JAMB ta saka shi a gaba kan sai ya samar mata mai koya mata lesson. Yanda ta uzzura mishi, bai zauna ba jiya kwata- kwata sai da ya samo mata wata malamar makarantar sakandire wacca kawar ƙanwar abokinsa ce. Tunda ya gaya mata take ta zumudi. Ta so a jiyan ta fara zuwa amma ya ce sam. Kuma a jiyan babu kunya ta saka shi gaba ya bata dubunta ashirin.

“Ni ban san JAMB ya kai har dubu ashirin ba Safina.”

“Ai dai ka san bazan cuceka ba dai ko?”

Maganar ta yi ta ne tana murguɗa baki dan bata son Safinan da yake karanta.

“Bari na maka lissafi. Kuɗin dubu tara ne da dari takwas na rijista. Ɗari biyu ce ta kai ni Cafe…”

“To me akai har na dubu goma?”

“Ka tsaya mana ka ji. Na sayi past questions na dubu shida , kowanne dubu ɗaya da ɗari biyar biyar. Na biya ɗan Cafe dubu biyu. Na aika aka saya min abinci, da kyar nake hadiyarsa dan rashin dadi. Na yi kudin mota na dawo gida.”

Kallonta kawai yake a mamakance. Dan ya lura kamar sun bugi hancinta ne da yawa. A iya saninshi, littafin JAMB daya ko dubu bai kai ba. Kamar ma idanunta a rufe suke take ta miƙa musu kuɗaɗen.

“Gaskiya ke mai kuɗi ce. Ni bani da wata dubu ashirin da zan ɓarnatar.”

“Au karatun nawa ɓarnar kuɗi ne Hassan? Da na ga kana son karatun nawa amma yanzu dan zaka ƙara aure?”

“To Madam blackmail ba sai hawayen ya zubo ba ma zan baki anjima idan na fita na dawo.”

Daren kasa bacci ta yi dan zumuɗin mai lesson zata zo. Yana jin yanda ta dinga mutsu mutsu shi ma tana katse mishi bacci. Sai da ya ce mata zai kira ya ce mai lesson din kar ta zo. Sannan ta nutsu ta yi tsam, da ƙyar baccin ya yi awon gaba da ita. Da safe ma da wuri ta tashi ta zauna jiran mai lesson. Lokaci zuwa lokaci tana duba agogo. Sai da ta zo sannan ta samu nutsuwa.

Hour uku cur! Suka ɗauka ana ta faman abu ɗaya. Safinan da ya sani ko littafin Hausa bata dubawa saboda yanda ta ƙi jinin karatu. Ko dogon saƙo ta manhajar whatsapp bata iya dubawa. Idan ya ɗauko jarida yana karantawa ta dinga ƙorafi kenan tana jinjina ma ƙoƙarinsa kenan. Shi bai gane wannan son makaranta da ya shigeta farat ɗaya ba. Amma bari ya ga iya gudun ruwanta.

Ta ce sai la’asar zata tashi daga wajen dan haka ya ɗauko wayarsa ya kira Afra. Hira suke yi mai sanyaya rai sai juyi yake yi a kan kujera har yana neman faɗuwa. Tuna mishi ta yi da convocation din su da za’a yi gobe.

“Babe har na manta fa gwanda da kika tuna min”

“Ai kuwa da baka zo ba…. Hmnn”

Yana shirin bata amsa ya ji an buɗe kofa. Jiki na rawa ya kashe wayar yana kallon Safina da ta shigo. Hankalinta ma gaba ɗaya baya kan shi. Kitchen ta wuce dan ɗora girkin dare. Sauri ya yi ya aika ma Afra text ya goge sannan ya goge kiran da yai mata ya bi Safina kitchen. A nan yake gaya mata ɗaurin auren da zai je a washe gari.

Washegari ya shirya cikin ash ɗin shaddarsa yai mata mutukar kyau. Tana kalonshi yana fesa turare sai ta ji zuciyarta ta kumbura da wani irin alfahari. Hassan ya cika na mijin da kowacce mace zata yi burin samu. Take kuma zuciyarta tai duhu tunawan da ta yi tana daf da raba shi da wata can daban. Da tana da hali, da sai ta raba wannan auren da ake shirin yi.

*****
Sai da Hassan ya biya ta wani gida ya karɓo katuwar kwando wanda aka yi shi da kaba. Da’ira ne kwandon, cike yake da kayan kwalam da makulashe sannan akwai katuna a ciki masu ɗauke da saƙon taya murna. Kwandon an nannaɗe shi da wata leda wacca ake iya ganin abunda ke ciki sannan akwai zanen zuciya ja tsilla tsilla a ciki. Abun sai wanda ya gani.

Bai zarce ko ina ba sai jami’ar Bayero da ke birnin Kano a kan titin Gwarzo Road. A nan filin taronsu ya samu waje ya adana mota. Ya so shiga filin taron amma yana jin kunyar haɗuwa da sirikansa a ciki. Ya ci kusan awanni biyu a motar kafin ya soma ganin fitowar mutane daga cikin filin. Dan haka ya ware idanu yana kallon ta inda zata ɓullo.

Sam bata lura da shi ba sai ji ta yi an ce,

“Babe”

Murmushi ta yi kafin ta juyo. Bata yi tunanin yanzu zai zo ba. Ƴan gidansu ma sun ce idan an gama ta kira sai su zo su yi hotuna. Yanzu haka ta tura musu sako cewar an gama.

“Boo”
“Congratulations. Kayan nan sun amshe ki. Kar ki mayar musu.”

Dariya ta yi tana jin daɗi har kasan ran ta. Kafin ta yi magana ƙawarta ta ƙaraso suka gaisa. Ta bata wayarta dan ta ɗauke su hoto.

“Bari na tafi Babe. Kar ƴan gida su zo su sameni a nan.”

“Kai Boo”

Ta faɗa a shagwaɓe. Tana da buƙatar suyi hotuna da dukka ƴan gidansu saboda haka bata so ya tafi yanzun. Har mai hoto aka daukar mata na musamman, tare da mutanen gida zai zo.

“Kar ka barni ni kaɗai ƴan gidanmu basu ƙaraso ba. Boo I’ll be lonely.”

Yanda ta yi narai narai da idanu kamar zata yi kuka sai ya ji idan ya tafi bai kyauta mata ba. Motarsa suka ƙarasa suka zauna suna hira kafin mutanen gida su ƙaraso.

*****
Safina na jingine jikin kujera tana daddana wayarta. Karatu ta gama, ta ji baya shiga ne sai ta ce bari ta dyan huta ƙwaƙwalwarta kaɗan. Yaran yanzu ta fi tura su wajen Hajiya Mama dan ta samu ta dinga karatu.

Facebook ta ke dubawa. Ƴan bidiyo da hotuna take dubawa. Bata kula saƙonnin whatsapp da ke shigo mata ba. Ta shagala tana kallon bidiyo na ƴaƴan turawa lokacin da aka gaya musu abunda iyayen nasu zasu haifa (gender reveal). Sakon Hajiya Bilki da ya shigo ne ya sakata katse kallon da take yi. Basu taɓa magana da ita a whatsapp ba sai dai waya da sukan yi lokaci zuwa lokaci. kuma kamar hotuna ta tura mata. Iya saninta dai Hajiya Bilki ba kasuwanci take ba balle tai mata talla. Amma bari dai ta duba.

Kasacewar akwai ƙarfin network, nan da nan hotunan huɗu suka buɗe. Gabanta ne ya yanke ya fadi da ta ga Hassan dinta da wata yarinya ta sha gown na makarantar jami’a.

“Na shiga uku ni Safina”

Hannu na rawa ta fita daga hoton ta buɗe na gaba.

“Wallahi Hassan ne”

Ta furta a tsorace. Sauran kuma shi ne a cikin jerin wasu mutane da bata ma damu da ta san su ba. Na farkon ta kara dubawa. Kana ganinshi ka ga wanda yake cikin farin ciki. Baƙin cikinta ma irin kallon da yake yi ma yarinyar da fuskarta ke nuna alamun kunya.

“Munafukai algungumai”

Wayar Hajiya Bilki ta shiga nema. Tana ganin an amsa bata jira wani gaishe gaishe ba ta ce,

“Hajiya Bilki mijina na ga kin turo min da wata yarinya.”

“Yarinyar da zai aura ce. Shekaranjiya aka yi hotunan.”

“Ya ce min ɗaurin aure zai je”

Dariya Hajiya Bilki ta yi.

“Ke mijinki ya ɗauko aure har akwai wani abu da zai faɗa ki yarda? Ai kawai ki ƙaddara idan baya tare da ke to yana tare da ita.”

Safina ta ƙura ma hoton idanu bayan sun gama waya da Hajiya Bilki. Ko dai sirantar yarinyar ne ya ja hankalin Hassan? Ta san ta yi ƙiba amma ba mummunar ƙiba ta yi ba. Ta dai murmure ne kawai. Bata da tumbi saboda Mama takura mata take sai ta daure cikin da fai fai. Yanzu tana ganin amfanin hakan.

Bata ga ta inda wannan ƙwailar yarinyar ta fi ta ba. Bata ma kamota a komai ba. Ita ba kyau ba, ba diri ba sai aukin rashin ƙiba. Anya? Gaskiya Hassan ko ya makance ko baya cikin hankalinsa. Har meye abun so a wannan yarinyar. Idan ma saboda bokon ne ai akwai haɗaɗɗun mata ƴan boko. Duk sai wani takaici ya lulluɓeta. Wayar ta ajiye ta ɗauko littafinta tana dubawa.

Can dai ta ƙara kiran Hajiya Bilki.

“Wai dan Allah Hajiya Bilki kin kalli yarinyar da kyau kuwa?”

Dariya Hajiya Bilki ta yi wanda ya nuna alamun tana cikin nishadi.

“Ƙwaila da ita fa. Babu wata mamora a jikinta wallahi Allah. Babu kyawun fuska balle na jiki. Me Baban Iman ya gani a wajenta?”

Sai da Hajiya Bilki ta yi dariyarta ma’ishi sannan ta ce,

“Safina kenan. Ba wannan tambayar zaki yi ba. Tambaya zaki yi me ta gani ta maƙale mishi? Ai da ganin wannan yarinyar ke ma kin san sai dai ta ganshi tace tana so.”

Sun ɗan ɗauki lokaci Safina na kushe ƴar budurwar da bata ma san ana yi ba. Hajiya Bilki kuwa na daɗa bata ƙwarin gwiwa. A cewarta tunda ta fi ta kyau da haɗuwa, komai zai zo mata da sauƙi in dai ta ɗauki matakin da ya dace.

Bayan wayar tasu ne Safina ta rasa daɗi zata ji ko kuma ciwo abun zai mata a rai? Daɗin cewar babu wani abu da yarinyar zata nuna mata sai karatun boko wanda ita ma tana nan zata yi shi. Ko kuma haushin cewar Hassan ya faɗo da mutuncinta ƙasa warwas ta hanyar haɗata da wannan ƙwailar kuma kucaka. Wannan tunanin shi ya hana mata ƙarasa karatun. Wayar ta ɗauko tana ƙara kallon yarinyar da ake shirin haɗata zaman kishi da. Ganin zaman ba zai amfaneta ba sai ta ga gwanda ta tashi ta wuce gidansu Hassan ɗin. Bata ma jin a ranta zata iya yin wani aiki. Zata tafi a ƙasa, ko ta rage ma kanta lokaci.

Ko da ta isa gidan, kai tsaye ɓangaren Hajiya Mama ta nufa. Muryar Hajiya Mama take ji tun kafin ta shiga falon, da alama a waya take magana tunda bata jin muryar kowa. Tun bata ƙarasa shiga ba ta cire hijabin jikinta ta riƙe a hannu.

“Assalamu alai….”

Setin akwatunan da ta gani ne a baje a tsakar falon shaƙe da kaya ya saka ragowar sallamar maƙalewa. Kujera mafi kusa da ita ta samu ta zauna dan ji tayi kamar ta zama ruwa tana narkewa. Kayan take kallo tana kallon Hajiya Mama da ke waya. Ba sai an gaya mata ba. Ta san kayan lefen Hassan ne.

“Ah Safina kin ƙaraso?”

“Uhm”

Shi ne abunda ya iya fitowa daga bakin Safina. Ji ta yi gaisuwar da zata yi ma Hajiya Mama ya bi iska.

“Ga kayan lefen Hussaini ki zo ki gani kafin a kai ma Alhaji.”

“Hassan?”

“Hussaini fa na ce”

“Wai shi ma Hussainin aure zai yi?”

Ganin mamakin da ke kan fuskar Safina ya tabattar ma Hajiya Mama cewar bata san da zancen ba. Tsaki ta ja,

“Ai na san dama ƙila ƙawar taki ba zata gaya miki ba. Ai tare za’a yi auren da na Hassan.”

“Ina kayan Hassan ɗin?”

“Oho mishi. Safina raba ni da auren Hassan ɗinnan. Ni ban ƙi a fasa shi ba wallahi tallahi. Banda halin namiji me zai saka shi ƙara aure? Ba yanda bai yi da ni na hada nai musu sayayyar lefen ba nace ba da ni ba. Ƙila uwarsa ta haɗa mishi.”

Safina ta gane wa take nufi da uwar Hassan ɗin. Jin dai ba kayan Hassan bane sai ta zame daga kujerar ta zauna tana ɗaga kayan jiki a sanyaye. Wai wannan kayan kishiyar Nabila ne. Nabila ma kishiya za’a yi mata. Wannan wacca iriyar ƙaddara ce ta faɗo musu?

Tana ji Hajiya Mama na gaya mata tsadar kayan da kuma inda ta saye su. Wasu daga Dubai wasu India. Yawancinsu ƙawarta ce ta saya mata. Kana gani ka san lefen an ɓata masa lokaci kuma an kashe mishi kuɗi. Bata jinjina ma al’amarin wannan lefe ba sai da ta ga setin gwal danƙarere a cikin akwatin sarƙoƙi da ƴankunnaye gami da agoguna. Ta daɗe da ɗan kunnen gwal din a hannunta ƙwaƙwalwarta ta kasa lissafi.

Jiki dai a sanyaye ta maida sannan ta taimaka wajen shirya kayan cikin akwati. Tana yi tana ji kamar amanar Nabila take ji. Tana gamawa ta miƙe ta wuce gidan Nabila.

A tsakar gidan ta samu Nabila riƙe da ƙaramin bokiti. Da alamu wanki ta yi ta shanya kayan.

“Wata sabon gani. Gaskiya wannan ƙawancen namu sai an yi mai sabon subscription”

Nabila ta fada tana amsa sallamar da Safina ta yi mata. Dariya Safina ta yi tana binta su shiga cikin gidan.

“Nabila bana cikin nutsuwata ne. Tun suna ban samu kai na ba”

Nabila ta shiga ciki ta ajiye bokiti ita kuma Safina ta samu kujera ta zauna tana ƙare ma falon kallo. Babu wani abu da ya canza tun zuwanta na ƙarshe. Babu ma abunda ya canza tun auren nasu. Ita kuwa a ƙalla an canza komai na gidanta ya yi sau biyu.

“Wai Nabila ba zaki yi ma Hussaini magana ya canza miki ko da kayan falo bane ba? Wallahi ba dan kaya masu kyau aka mana ba da kujerun nan ba zasu ganu ba. To dai kar ki yarda sai an miki sabbin kayan ɗaki.”

Dariya Nabila ta yi tana girgiza kai.

“Tunda idanunsa basu gane masa kujerun sun fara gajiyawa ba ni meye nawa Safin?”

“Shi da za’a kawo mishi sababbi? Ai ko ɓarkewa suke yi ba zai ga gajiyarsu ba. Can miki ke da matsalarki ko?”

Rausayar da kai Nabila ta yi tana murmusawa. Idan ta saka ma ranta ma ta san ɓacin rai ne zai biyo baya. Ya fi kowa morar kujerun ai. Rannan tana kallonshi yana ta juye juye yana neman yanda zai kwanta ya ji dadi kamar yanda ya saba.

“Nabila namiji bashi da amana. Ban taɓa tunani ba Nabila. Ban taɓa tunanin zasu mana haka ba.”

Cikin rashin fahimta Nabila ke kallon Safina.

“Wai kamar ni Hassan zai yi ma kishiya. Dama Hussaininki baƙin ranshi ma ya sa ba za’a yi mamaki ba dan ya yi ga kuma goyon bayan Hajiya Mama da ya samu.”

“Shi ma Hassan ɗin aure zai yi? Ko da wasa ban ji ba wallahi Safin”

“Ai kuwa aure zai ƙara shi ma. Wata yarinya baki ganta ba sunanta Afra. Bari ki ga hoton da suka ɗauka nima ɗazu aka turo min.”

Ta ɗauko wayarta ta buɗe ta shiga ma’adanar hotuna da hotuna masu motsi ta nemo hoton Fa’iza da Hassan ta miƙa ma Nabila.

“Kalli ƙwailar dan Allah. Wai nan graduation dinta ya je. Ta gama jami’a. Ya ce min ɗaurin aure yaje ashe ashe.”

Girgiza kai kawai Nabila ta iya yi dan bata san abunda zata ce ba. Tambayoyin da suke kanta suna da yawa. Kamar ta inda har ta san wacca Hassan ɗin zai aura har ma dai ta samu hotonsu.

“Wa Hussaini zai aura?”

“Ni fa banda auren da ya ce min zai ƙara ban san komai a kai ba.”

“Baki so ko sani bane Nabila. Idan kina son sani ai tuni zaki sani.”

*****
Ko wacece amaryar Hussaini?

Wannan lefe haka?

Kada ku manta ku yi like da comment

<< Soyayya Da Rayuwa 5Soyayya Da Rayuwa 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.