Wane Irin Da Ne Ni?
Amshi:
Wane irin ɗa ne ni?
Wane irin ɗa ne ni?
Wane irin ɗa ne ni?
Yaushe ne zan canza?
01.
Da fari farin farko, na tuno da yarintata
Sa’adda na ɗan tasa, ina cikin ƙuruciyata
Banda aikin komai, kullum sai ragaita
In ka so kira ni da gwarzo, don na zamo fagen sangarta.
02.
Da ace ana yin sarki, da na zamo fagen kangarta
Babu moriya a gare ni, balle ma na je makaranta
Kullum ina kan titi, daga ni sai shiririta
Bani shakkar kowa, ko Uba ko Ummita.
03.
Bani tsoron komai, in ka taɓo ni ban lamunta
Rigima za fa mu yi ta, da ka taɓo ko rigata
Idan ɓarna aka yi, ka jiyo ana ta biɗa ta
Rigima sabona, na riga na gawurta.
04.
Da ka ji ɗaukar magana, ka jiyo ana zance na
Da ka ji an yo sata, ka jiyo ana nema na
Da ka ji hayya-hayya, ka jiyo ana ta kira na
Da ka ji an yo zalunci, ka jiyo ana ta kira na.
05.
Ofishin doka in ka je, can ma akwai sunana
Cikin jaridu nan ma, duba ka gano hotona
Ko da fa layi na biyo, ka gano ana zunɗe na
Ni ko fa ban jin komai, ko kaɗan ma a jikina.
06.
Bani girmama kowa, bani so a yi min raini
Yanzu ka zama gawa, in dai ka yi min raini
Ko ka koma gurgu, in na ganka ka kalle ni
Mutanen gari dukka, kowa ya riga ya san ni.
07.
Ko da Uwata ma, ta san bani son raini
Hatta Uba guna, yasan bani son raini
Yanzu za fa a dare, da zarar nai gurnani
Na zamo hankaka, babu wanda zai kama ni.
08.
Bani tausayin ɗan kowa, sai ka ce banda imani
Iyayena suna kuka, na zame musu ɗan kuka
Bani ma jin komai, don na sa su yin kuka
Gashi na dame su, kuma gashi na wuce duka.
09.
Tura da ta kai bango, suka tsine mini albarka
Nan na gane kurena, na ma gaza yin kuka
Ciwon daji ya kama ni, na koma kamar nai hauka
Na je wurin Ummina, ina ta yi mata kuka.
10.
Na sha baƙar wahala, sai ka ce Ɗanwake
Hannuna ya girma, ya zamo makeke
Ina ji ina gani, dole za fa a yanke
Amma a loton nan, na ma fi so fa a yanke.
11.
Domin da an yanke, wahalar za fa ta yanke
Rayuwa ta sa, cutar zuciya ta warke
Ya Rabbi sarkina, ka yafe ni laifina
Ya ke Ummina, ki yafe ni laifina.
12.
Ya kai Abbana, ka yafe ni laifina
Ya ‘yan uwa guna, ku yafe ni laifina
Ina makwaftana, ku yafe ni laifina
Jama’ar garina, ku yafe ni laifina.
13.
A da na yo ƙwari, sai ka ce ɗan kwakwa
Yanzu ko sai ladabi, kamar ɗan kaza a gaban kwakwa
Na ɗauki alƙawari, bani ba ƙarawa
Allahu shirye ni, daga nan har mutuwa.
14.
Jamilu dai ɗin ne, ko ku ce Haimana
Ke godiya gun sarki, jalla mahaliccina
A yau ranar Lahadi, sha tara ga wata na
Ashirin da biyun, dubu biyun zamanina.
Amshi:
Wane irin ɗa ne ni?
Wane irin ɗa ne ni?
Wane irin ɗa ne ni?
Gashi yau na canza.