Tambaya Mabudin Ilimi
01.
Tambaya mabuɗin ilimi,
Tambaya sirrin ilimi,
Tambaya aikin ɗalibi,
Amsawa aikin malami,
Ɗauka kuma aikin mumini.
02.
Tambaya tushen ilimi ,
Tambaya maganin jahili ,
Tambaya ƙaton makami ,
Tambaya kofin ilimi,
Tambaya ruwa na ilimi.
03.
Tambaya tilas ga ɗalibi,
Tambaya jidali ga jahili,
Tambaya jiki ga mumini,
Tambaya ruwan shan malami,
Tambaya makamin ɗalibi.
04.
Tambaya bata wuce ɗalibi,
Tambaya ta fi ƙarfin jahili,
Tambaya na ƙara ilimi,
Tambaya na canza zamani,
Tambaya mabuɗin ilimi.
05.
Tambaya tana da. . .
Masha Allah, muna jin dadin wannan rubuce-rubucen naka
Masha Allah. Ina godiya sosai. Allah ya saka da alheri. #haimanraees
Masha Allah Allah yakara basira haiman
Amin. Jazakallah Khair. #haimanraees
Masha Allah Allah yakara basira haiman
Na gode sosai.
Masha Allah!.
Allah ya ƙara basira da ilmi mai albarka 🥰
A gaskiya na ƙaru da wannan waƙa
Masha Allah. Lallai saƙo ya isa kenan. Na gode sosai. #haimanraees