Girman Kai
01.
Da sunan Allah mai duniya,
Ilahu da Ya yi samaniya,
Ya ƙagi tudu har maliya,
Shi ne yai mana safiya,
Ya aiko manzon gaskiya.
02.
Tsira da aminci bai ɗaya,
Ga Annabi sirrin gaskiya,
Da ya kawo saƙon gaskiya,
Haɗa ahalinsa gaba ɗaya,
Da Sahabbai duk 'yan gaskiya.
03.
Girman kai rawanin tsiya,
Na ɗauka na ja tsiya,
Gani ina ta fagabniya,
Duk na bi ko na sha wuya,
Na yi nadama don wuya.
04. . .
🙏🙏🙏🙏🙏
Thanks alot. #haimanraees
Da kyau! Allah Ya kara hazaka!
Amin. Jazakallah Khair. #haimanraees