Skip to content
Part 23 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Girman Kai

01.

Da sunan Allah mai duniya, 

Ilahu da Ya yi samaniya, 

Ya ƙagi tudu har maliya, 

Shi ne yai mana safiya, 

Ya aiko manzon gaskiya. 

02.

Tsira da aminci bai ɗaya, 

Ga Annabi sirrin gaskiya, 

Da ya kawo saƙon gaskiya, 

Haɗa ahalinsa gaba ɗaya, 

Da Sahabbai duk ‘yan gaskiya. 

03.

Girman kai rawanin tsiya, 

Na ɗauka na ja tsiya, 

Gani ina ta fagabniya, 

Duk na bi ko na sha wuya, 

Na yi nadama don wuya.

04.

Ni ba ni da ko fa aniniya, 

Babu sarautar duniya, 

Ba ilimin ga na duniya, 

Ilimin addini ko ɗaya, 

Sai girman kai ko da fariya. 

05.

Ni ba suturar kirki ɗaya, 

Ba mota ko ma taya, 

Ba daraja ko da ɗaya, 

Ba haƙuri ba tarbiyya, 

Sai jahilci da kwaramniya. 

06.

Ban girmama kowa duniya, 

Ba Sarki koko Sarauniya, 

Ba yarima ko wata Gimbiya, 

Babu Uba ko Mahaifiya, 

Balle Malam mai tarbiyya. 

07.

Yau gani tsulum fa a rijiya, 

Rijiyar wahala da hayaniya, 

Na yi tsuru kamar mujiya, 

Na yi luguf kamar taliya, 

Ba sauƙi zaman ita duniya. 

08.

Banda aboki ko ɗaya, 

Ba mata ko da ɗaya, 

Yara babu na moriya, 

A gidana kau ko tsintsiya, 

Ba na magani don tsiya. 

09.

Dama ba fara’a kamar hasbiya,

Ba kunya kamar wata harƙiya, 

Sai feleƙe kamar wata kurciya, 

Bana taro ko ƙungiya, 

Yau gashi na ga ta duniya. 

10

Allah wadaran girman kai ɗaya, 

Wanda ya bi shi ya sha wuya, 

Ya rame ya koma sai ‘yar wuya, 

Yana rama a tsakar wuya,

Kogin wahala ko ya dulmiya. 

<< Tambaya 22Tambaya 24 >>

4 thoughts on “Tambaya 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.