Skip to content
Part 1 of 3 in the Series Tsaka Mai Wuya by Umar bin Ally

Na kasance mutum mai yawan kule-kulen yan mata a Facebook ta yadda ni kaina ban san iya adadin yan mata na ba dan kusan kullum sai na yi sabuwar budurwa sau dayawa nayi soyayya da yan mata sai daga baya na gano cewa namiji ne yake amfani da sunan mace.

Wata ranar lahadi da yamma ranar anyi ruwa gari yayi dadi ina zaune acikin abokaina acikin unguwarmu suna tsokanata kan cewa ba abinda nataba samu awannan Facebook din saidai kawai inata asarar lokacina da kudina kawai sai gani mukayi wata kyakyawar mota kirar BMW ta shigo cikin layin ta tsaya adan nesa damu kadan nan take kuwa motarnan ta tafi da imaninmu gaba daya gurin yayi shiru kamar ruwa ya cinyemu

Bude kofar motar akayi ahankali mukaga wata kyakyawar kafa tafara fitowa nan take muka dauke kallon mu daga kan motar muka maidashi izuwa wannan kafa wata kyakyawar kafa ce fara tasha adon lalle sanye acikin wani takalmi na alfarma nantake nafara sake saken wannan kodai balarabiya ko baturiya amma yanayin lallen da nagani yasa nayanke cewa gaskiya wannan saidai yar India

Ina cikin wannan tunani ne kawai mukaga tafito daga cikin motar tsarki ya tabbata ga Allah maikowa mai komai kalmarda tafito daga bakina kenan adaidai lokacinda gaba daya muka mike tsaye idanunmu akan wannan kyakyawar halittar dukda cewa ni ma,abocin kallon finafinan turawa ne da indiyawa amma bazance nataba ganin mai kyawun wannan halittar ba dan tuni na tabbatar da cewa wannan ba mutum bace inbanda nasan cewa babu mala,ika mace tabbas da zuciyata zata iya rayamin cewa wannan mala,ikiya ce

Fara ce doguwa mai matsakaicin jiki siririya amma ba sosai tanada manyan idanu blue eyes hakan ya sa nace araina tabbas wannan tahada jinsi da turawa bazan iya misalta kyawunta ba misalin da zakufi ganewa shine kamar ahada Ashwariya priyanka depika da alia bhat ne afitar da mutum daya ba cikin shigar kananan kaya farare sannan ta dora wata bakar suit akai

Nufo inda muke tayi cikin wata irinyar tafiya maijan hankali inda mukuma alokacin tuni mun suma atsaye har tazo kusa dani tana magana kawi kallon bakinta nake yana motsi amma sam banajin abinda take cewa har saida ta kyasta hannunta akusa da kunnena nai firgigit na dawo hayyacina skamar wanda ya farka daga bacci

Sai ji nayi tayi magana da wata zazzakar murya mai kamar ana busa sarewa cikin matukar mammaki naji hausa tayi ta nunani tace umar bin Ally ? cikin matukar mamaki nace eh yayinda idanuwana ko kiftasu banayi na zubasu akan fuskarta ta jefeni da wani murmushi taci gaba da cewa sunana zainab sadeeq ni ma,abociyar bibyar rubutunka ce a Facebook suna matukar burgeni kana kuma nishadantar dani hartakai ga cewa kullum sai na karanta rubutunka nakejin dadi nasaba da kalamanka sune farincikina shine nayanke shawarar nazo gareka musaba da juna tayadda zan ringa Samun kalaman nan naka duk sanda naso basai najira andora a Facebook ba

Kasa magana nayi kawai inata kallonta hartagama maganar saga bisani ta mikomin hannunta da niyyar mugaisa fuskarta cike da murmushi tana mai cewa naji dadin haduwa dakai bin Ally

Hannu biyu namika da nufin gaisawar saikawai wata kara naji daga sama sai ji nayi kamar andake a gefen kunne firgigit nafarka kawai maga akuya asaman kaina har tana takamin fuska afusace na mike na tabbatar da cewa mafarki nake abinda yakara susatani shine bata bari mun gaisa ba ta katsemin mafarkin nawa naji kamar nati kuma nan take natashi nazare belt na kulle kofata nahau akuyarnan da duka baji ba gani karar dukan da nake mata da kukan da take dakuma yasa hankalin kowa yadawo dakina aka taru ana bugamin kofa koda na bude akaga dakin kaca kaca komai a haritse wasu abuubuwan dak sun fado sun fashe

lafiyarka kuwa tambayarda mama na tamin kenan cikin mamaki da takaicin abinda na aikata budar bakina sai cewa nayi mama bata bari mun gaisaba kawai ta tasheni ku gaisa da wa ? Ta kara ymtambayata nace da ita zainab sadeeq mana ina mafarkina maidadi kawai takama ta tasheni eh tabbas ba lafiya ba inbanda rashin hankali dabba zakaiwa wannan dukan kuma ma akan wani mafarki ban iya abinda naji kenan tuni natasfi cikin tunanin zainab sadeeq mama tana ta fada banma san me take cewa ba ina tuno fitowarta daga mota tafiyarta da dadin muryarta inata murmushi abinda yabata mamaki kenan tafara tunanin anya kuwa dan autan ta ba gamo yayi ba

Kawai sai nadauko wayata nashiga Facebook nawuce gurin searching nayi typing zainab sadeeq naga sunfito dayawa nafara dubawa cikin mamaki ina bude na farko naga hoton ta bansan lokacinda nayi wani ihu ba nace na samota hakan ya kara tabbatarwa mama cewa gaskiya ba lafiya nake ba nantake naga tafice daga dakin tana rabka salati

Nan take nikuma natura mata friend request natsaya idona akan wayar ina jiran naga ta karba ba dadewa naga ta karbeni natura mata sallama ta amsa tareda cewa bin Ally nayi farin cikin ganin ka turomin request ni din mai bibiyar rubutunka ce a Facebook kuma ina mutukar nishadantuwa dasu

Cikin kankanin lokaci muka saba da ita kullum muna tare a online da na sauka da minti 10 zanga kiranta suk lokacina yazama nata nata lokacin yazama nawa

Wata rana ina zaune kawai sai naga sakonta tace dani inaso muhadu na mayar mata da amsa nace nafiki son hakan sai takara cewa zan turoma inda zamu hadu kazo gobe karfe goma na safe nace to Allah ya kaimu tace ameen ka kulamin da kanka

Washe gari tun asuba natashi nafara shirin haduwa da ita a cikin kayana na wanda ban saka nakalli madubi ba amma sai naga basuyi ba nan take na tuna da jiya yayana ya aikeni na karbo masa sabon dinkinsa agurin dinki wanda kuma shima yau zaisa su za,ayi auren amininsa banyi wani tunani ba naje na daukesu nafice nabar gidan dakin abokina na wuce achan nayi wanka nasaka kayan nida akace karfe goma tun takwas da rabi na shirya natafi ina jiran zuwanta karfe tara da rabi naga sakon wai kaine azaune da milk din shadda har kazo natura mata da cewa na matsu naganki ne ahiyasa nazo da wuri banga amsa ba sai kawai sojoji nagani nagani mota uku da muggan makamai kamar zasuje yaki sun faka a kusa dani sun nufoni sukace kaine bin Ally a tsorace nace dasu eh meyafaru

Maimakon subani amsa saiji nayi sun rufeni da duka baji ba gani kamar Allah ya aikosu suna fadin waye babanka agarin nan da zaka ringa hurewa matar yallabai kunne nantake nakara tsorata nafara cewa yallabai wallahi bansan matar aure bace basu ko saurareni ba saida suka yimin lilis suka jefani amota suka tafi dani muna tafiya ne a motar naji babbansu yana waya yana cewa ku shirya gurin nan zamu kawo ajiyar wani mara kunya da yake soyayya da matar ministan tsaro na kasarnan wanda yallabai ya ganoshi yakuma shirya masa gadar zare kuka kamoshi yanzu haka muna hanya.

Tsaka Mai Wuya 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.